Dalilan Da Ke Sa A Karbi Addu’a Da Abubuwan Da Ke Hana Karbar Addu’ar Bawa

    Da sunan Allah mai Rahama mai Rahama

    Dukkan godiya da yabo da jinjina sun tabbata ga Allah maɗaukaki, buwayin Sarki gagara-misali. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi ɗan Amina Shayabo, babba farin jakada. Tareda alayensa da sahabbansa baki ɗaya.

    Bayan haka,

    Ƴan'uwa musulmi masu albarka, barkan mu da wannan rana ta Arfa mai ɗimbin falala da daraja da matsayi a wajen Allah. Ranar da Allah Yake alfahari da bayinSa da suke tsaye yanzu haka a filin Arfa a matsayin mahajjata, Yake kuma gafarta musu zunubansu. A wannan ranar ɗin kuma, Allah Yake amsa addu'ar sauran bayinSa da suke gidajensu a garuruwansu mabanbanta.

    Haƙiƙa nasan kowa ya shirya tsaf don ribatar abinda malamai sukayi ta tunatarwa akai, wato kwaɗaitarwa akan yawan addu'o'i domin Allah yana karɓar duk addu'ar da akayi a wannan yini ta Arfa. Allahu Akbar! Allah Ka karɓa mana, ameen.

    Toh wani abu mai muhimmanci da ya kamata ace duk musulmi ya sani kuma ya kiyaye, shine, akwai wasu laifukan da idan mutum yana cikin su, Allah bashi karɓan addu'arsa. Wato, ba kowa bane Allah Yake karɓan addu'arsa! Gasu kamar haka;

    1. Azzalumi/Zalunci: ya kamata musan cewar, Allah Ya hana zalunci (a hadisin Ƙudsy kamar yadda Abuzar ya ruwaito daga Annabi shi kuma daga Allah Azza wa Jalla. Kamar yadda Muslim ya ruwaito: 2577). Kuma Yace baya son azzalumai (Ali'Imran 3:140).  Hakanan, Manzon Allah (SAW) ya yi tsawa akan kiyaye addu'an wanda aka zalunta (Hadisin Ɗan Abbas riwayar Bukhari da Muslim akan aika Mu'az zuwa Yemen). kenan ƙarara munga cewar duk wanda ya zalunci wani, toh ya shiga cikin fushin Allah. Wanda yake cikin fushin Allah kuwa ko ya yi addu'a ba lallai bane a karɓa. Kuma idan akayi addu'a akan sa, za'a karɓa.

    2. Mai cin haramun: A hadisin Abu Huraira (RA) riwayar Muslim, yace Manzon Allah (saw) yace; "Allah mai tsarki ne baya karɓa sai mai tsarki,..... Sai ya ambata (labarin) wani mutum da ya yi tafiya mai tsawo, ga gajiya gashi ya yi fururu, ya ɗaga hannu yana addu'a, Ya Rabb Yaa Rabb, Amma abincin haramun ne..... Yaya za'a amsa masa?". wannan ya nuna mana ba'a karɓan addu'ar mai cin haramun.

    3. Gafalalle/gafalalliyar zuciya: duk wanda yake addu'a alhakin zuciyarsa bata inda yake addu'ar ko kuma mutum ne da ya rafkana daga bauta da ambaton Allah, toh ko ya yi addu'a ba za'a karɓa ba. Saboda hadisin Abu Huraira riwayar Tirmizy, yace manzo Allah (saw) yace; "ku roƙi Allah kuna masu yaƙinin za'a amsa muku, ku sani Allah baya karɓan addu'a daga zuciyar gafalalle rafkananne" (Albany ya hassana shi a Sahiha). Don haka, ya yin addu'a wajibi ne mutum ya halarto da zuciyar sa.

    4. Gaggawa ya yin addu'a : an hana yin gaggawa wajen neman biyan BUƘATA a gaban Allah. Malamai suka e hatta Annabi Musa sai da ya shekara 40 yana jiran a halaka Fir'auna bayan ya yi addu'a. Idan anyi keeping Annabi Musa waiting for 40 years, how about you? Ita addu'a Allah Yana amsawa lokacin da ya gadama, ba'a masa tilas, kuma ba'a ƙosawa ko gajiyawa. Lokaci nayi, ake amsawa. Kuma yana iya chanjawa mutum abinda ya roƙa da wani abun wanda yafi wannan. Yana iya aje masa amsa addu'ar sai a lahira.

    5. Rashin ɗa'a ya yin addua: ana so a girmama Allah a yabe Shi ya yin addu'a, kada a masa lafuzza munana ko izgili ko duk wani nau'in rashin ɗa'a. Anaso a roƙi Allah cikin ƙanƙantar da kai da girmamawa. Kuma ba'a roƙonSa abinda ya saɓawa hankali.

    Wannan a taƙaice kenan. Duk mai yin addu'a sai ya sani, kar ya zama akwai haƙƙin wani aka sa, ko ya cika cikin sa da haramun ko gafalalle ne shi ko yana gaggawa wa Allah ko ya munana masa zato ko ya wuce iyaka ya yin addu'ar.

    Yaa Allah Ka karɓa ibadun mu da addu'o'in mu, Allah Kaso mu, Kaso ayyukan mu, Ka mana abinda Kakeyi wa waɗanda Kakeso, Ka ba mu mai kyau a duniya da lahira, Ka mana afuwa da gafara, Ka ba mu duk wani alkhairi da Annabi ya taɓa roƙonKa, Ka tsare mu daga duk wata sharri da Annabi ya taɓa neman tsarinKa daga gareta. Ameen

    Ranar Arfa, Asabar,
    9th ZhulHijjah, 1445.
    15th June, 2024.
    Bauchi.

    Daga Zauren Ko Ka San?
    https://chat.whatsapp.com/D2jlYWCJKhpAG5xnWDKy0k

    Admin:

    Phone: +2348036806678
    Email: yusufaumar97@gmail.com

    Ko Ka Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.