Fadin "Ta'ala" A Cikin Sallama Bidi'a Ne

    TAMBAYA (123)

    Assalamualaikum. Barka da rana. Ya gida. Dan Allah ena tamabaya kan rulings na fadin Assalamualaikum wa rahmatullah taala wa barakatuh. Fadin taala naji wasu malaman na magana akae

    AMSA

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhu

    ✍️AMSA A TAQAICE

    (Fadin ta'ala Bidi'ah ne saboda lafazin sallama Tauqifi ne ma'ana kai tsaye ne daga bakin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ba'a cudanya shi da lafazin wani saidai a barshi a haka. Don haka komai iya larabcin ka saidai ka tsaya a inda aka umarce ka kamar yanda su ma sahabbai da Salaf ba su yi kari ko ragi akan hakan ba)

    Bismillaahir Rahmaanir Raheem

    Kalmar ta'ala da ake sakawa a sallama bidi'ah ne. Domin kuwa ba haka Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya koyar ba

    Bara'u Ibn Azif (Radiyallahu anhu) yace: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya koyar dani addu'ar kwanciya bacci, da ya gama sai yace karanta min naji. Da yazo karantawa sai yace "Amantu birasulikallazi arsalta"

    Sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: "A'a, ce maka nayi "Amantu bi nabiyyikallazi arsalta"

    (Sahihul Bukhari)

    Duk da cewar "rasulikallazi" yafi munasaba da "arsalta" amman sai yace ni ban ce maka haka ba

    Don haka ba'a yiwa Annabi kari ko ragi a cikin abinda ya koyar

    Wasu mutanen kuma zakaga "Slm" suke turowa a matsayin sallama kamar yanda aka saba turomin

    MAI TAMBAYA: Aslm.

    USMANNOOR: "Slm" bi ma'ana aminci, kuma "Allahu huwas salam", Allah shine aminci

    A shawarce mezai hana a dinga rubuta cikakkiyar sallama domin dacewa da samun lada 30 kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya kwadaitar

    MAI TAMBAYA: Zan fara in Sha Allah na sa ba ne da yin hakan sabo da yafi sauki amma na de na Dan nasamulada 30.

    Assalamu, aliaku warahamatullahi wabarakatuhu barka da safiya ya gida

    alhamdulillah ina kara godewa, Allah da ya ba ka, ikon tunatar dani wannan garabasa ta samun lada har 30 Allah bumu, ikon durewa nagode Allah saka da,alkairi Allah ya biya maka dukkan bukatun ka na,alkairi👏

    USMANNOOR: Waalaikumussalam, warahmatullahi, wabarakatuhum. Wamaghfiratuhu

    Wani zaice a ina kuma aka samo "Wamaghfiratuhu" ?

    Allah (Subhanahu wata'ala) yace

    (وَإِذَا حُيِّيتُم بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّوا بِأَحْسَنَ مِنْهَا أَوْ رُدُّوهَا ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ حَسِيبًا )

    النساء (86) An-Nisaa

    "Kuma idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to, ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta, kõ kuwa ku mayar da ita. Kuma Allah Yã kasance a kan dukkan kõme Mai lissãfi."

    Ma'anar: "Kuyi gaisuwa da abinda yake mafi kyawu daga gare ta..." shine idan ka kara da "Wamaghfiratuh" fadin: "ko kuwa ku mayar da ita" na nufin ka amsa da cikakkiyar sallamar da dan uwanka yayi maka

    Haka kuma da akwai mutanen da zaka ga sun shigo gidanka ko shagonka ba tare da sallama ba alhalin hakan ba dabi'ar mai imani ba ce ba, kamar yanda Allah (Subhanahu wata'ala) ya umarta

    ( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَدْخُلُوا بُيُوتًا غَيْرَ بُيُوتِكُمْ حَتَّىٰ تَسْتَأْنِسُوا وَتُسَلِّمُوا عَلَىٰ أَهْلِهَا ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ )

    النور (27) An-Noor

    "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku shiga gidãje waɗanda bã gidãjenku ba sai kun sãmi izni, kuma kun yi sallama a kan ma'abũtansu. Wannan ne mafi alhri gare ku, tsammaninku, zã ku tuna"

    Sallama itace abinda mala'iku zasu yiwa musulmai maraba da ita idan an shiga Aljannah (Allah yasa da ni da ku mu shige ta)

    ( سَلَامٌ عَلَيْكُم بِمَا صَبَرْتُمْ ۚ فَنِعْمَ عُقْبَى الدَّارِ )

    الرعد (24) Ar-Ra'd

    "Aminci ya tabbata a kanku sabõda abin da kuka yi wa haƙuri. Sãbõda haka madalla da ni'imar ãƙibar gida."

    ( لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا إِلَّا سَلَامًا ۖ وَلَهُمْ رِزْقُهُمْ فِيهَا بُكْرَةً وَعَشِيًّا )

    مريم (62) Maryam

    "Bã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice"

    Sannan kuma akwai sahihin hadisi wanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: "Man bada'a bil kalami qablas salami fala tujibu" ma'ana "Duk wanda ya fara yi maka maka magana ba tare da sallama ba, kada ka saurare shi"

    Amal al-Yawm wal-Laylah na Ibn as-Sunni (214) da kuma Silsilat Ahahadith as-Sahihah na al-Albaany (816)

    Don haka yakamata mu dinga koyi da Salaf (Sahabbai, Tabi'ai da Tabi'ut tabi'in) a dukkan al'amuran mu na yau da gobe. Yanzu dai duba ka ga shawarar da Tabi'i Maymun bin Mihran (Rahimahullah) ya bawa Muhammad bin Saqah (Rahimahullah)

    Muhammad bin Saqah ya hadu da Maymun bin Mihran al-Jazary (d. 117 A.H - dan Kufah wanda yayi gwamna a zamanin Umar Bin Abdul'aziz) Sai yace masa: Hayyakallah (Allah ya aminta dakai), sai Maymun yace masa: wannan ai gaisuwar samari ce, ka fade ta hade da sallama mana (ko kuma ka fara min sallama kafin kace Hayyakallah. Kamar yanzu ne wani yace maka "Yane, ya garinne" a maimakon yayi maka sallama)

    Hilyatul Auliya na Abu Nu'aym (4/86)

    Dangane da hadisin lada 30 da ake samu silar amsa cikakkiyar sallama kuma, wannan yana cikin Musnad na Imam Ahmad, ya rawaito hadisin daga Abu Raja Al-Utardi yace Imran bin Husayn yace: "Wani mutum yazo wajen Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) sai yace: Assalamu alaikum. Sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya amsa masa, bayan mutumin ya zauna sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: "Goma". Wani mutum ma yazo yace: Assalamu alaikum, Warahmatullah. Sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya amsa masa, bayan mutumin ya zauna sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: "Ashirin". Can sai ga wani mutumin daban yazo yace: Assalamu alaikum, Warahmatullahi, Wabarakatuh. Sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya amsa masa, bayan ya zauna, sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: "Talatin"

    Abu Dawud ya rawaito wannan hadisin, hakama At-Tirmidhi, An-Nasa'i da Al-Bazzar

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.