Hanyoyin Da Za Su Kubutar Da Kai Daga Kallon Fina-Finan Batsa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamualaikum Malam ina neman taimakone na shawara dakuma hanyoyin da zan kubutar dakaina daga kallon videos na batsa wanda hakan yajawomin nake wasa da al'aurana har sai na gamsar da kaina. Wallahi Malam nayi bakin kokarina wajen naga nabari har nakan tashi cikin dare naroki Allah ya yafemin kuna nisancin kaina da hakan amma daga baya kuma sai nakoma ruwa kuma gashi banida halin yin aure a yanzu domin makaranta nakeyi kuma ba kuɗin auren. Nagode Allah yasaka da Alkhairi.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

    Kallon finafinan batsa bashi da kyau a rayuwar mu ko kaɗan sannan ma addinin musulunci yayi mana gargaɗi game da kallon tsiraicin wani. Saboda haka, yana da kyau mu daina wannan mummunar ɗabi'ar. Amma matsalar itace duk wanda ya saba kallon irin waɗannan finafinan zai sami matuƙar wahalar dainawa. Saboda haka idan kana son daina wannan halayyar akwai hanyoyi da yawa da zaka bi.

    1. Ka sa a ranka cewa babu kyau, ka goge duk finafinan batsa dake cikin wayarka ko cumputer, wannan yanayin zai taimaka sosai wajen daina wasa da gaba, da kuma kallon finafinan.

    2. Ka ƙona duk CD/tarkardun batsa, Matuƙar kana ajiye da irin waɗannan takardun ko CD na batsa, to daina kallonsu zai yi maka wahala sosai. Saboda haka, ka ƙona su sannan kuma a goge wanda yake cikin cumputer ko waya da duk wani abu daya danganci batsa.

    3. Ka saka application da zai katange shafukan batsa. Ko kana amafani da waya ko cumputer duk akwai applictation da ake kira da ANTI-PORN Shi wannan application ɗin zai hanaka shiga duk wani shafi a yanar gizo da yake da abubuwan batsa. Amma fa idan zaka saka masa lambar tsaro wato password, yana da kyau ka kira wani ya saka lambobin da baka sani ba, domin kuwa idan kaji kano son kallo babu yadda zaka buɗe ba tare da wanna lambar tsaron ba (password). Wasu daga cikin waɗannan application ɗin sun haɗa da: Qustodio, Microsoft family Safety, Norton Family Online, Covenant Eyes da sauransu.

    4. Yanke service na yanar gizo-gizo. Idan kaji kana son kallon waɗannan finafinan a yanar gizo to abu mafi sauƙi shine ka kashe data ɗin wayarka ma gaba ɗaya ko na cumputer. Idan ma da hali ka kashe wayar ka ajiye ta.

    5. Kashe lokaci da wasu abubuwan. idan ka saba zama haka kawai babu wani abinda kake yi, to lallai shaiɗan zai dinga raya maka ka kalli wannan finafinan musamman idan kai kaɗai ne a cikin ɗaki. Saboda haka, ka sami abinda zai dinga kashe maka lokaci. Misali

    👉ka fara motsa jiki: saboda motsa jiki yana bada wasu sinadarai a jikin mutum da suke sawa yaji daɗi.

    👉ka ɗan yi balaguro. Idan kana da halin barin unguwar da kake zaka iya tafiya wata unguwar na wani ɗan lokaci. Chanza waje zai taimaka sosai Chanza ɗabi’u.

    6. Ka gane abubuwan da suke jawo maka kallon. Zaka iya samun littafin da zaka dinga rubuta abubuwan da suke jawo maka kallon film ɗin batsa duk lokacin daka kalla. Zama ka iya rubuta abinda ya faru a lokacin. Misali abokanai dake zancen batsa, rashin bacci, shiga whatsApp ko facebook, da sauransu.

    7. Ka nemi aikin yi. Bincike ya nuna cewa idan mutum bashi da aikin yi suna iya fadawa cikin nema abubuwan kala-kala a cikin yanar gizo. Ɗaya daga ciki shine fara kallon hotuna/finafinan batsa. Saboda haka ka nemi aikin yi da zai kashe maka lokaci. Zaku yarda dani idan nace mutumin dayake son aikinsa zai dinga yin aikin ne har a lokacin dana hutu ne, kenan bazai ma dinga tinanin kallace-kallacen batsa ba.

    8. Ka nemi hanyar katange abubuwan dake jawo maka. Idan da hali ka katange abubuwan dake jawo maka kallon duk gaba ɗaya, amma idan bazai yiwu ba, sai ka fara kaɗan-kaɗan. Misali, idan kallon talla ne a TV yake taso maka da sha'awar kallon, sai ka guji kallon TV a lokacin dakasan za'a saka irin waɗannan tallukan. Idan kuma babu yadda za'ayi ka guje wa abubuwan dake taso maka da sha'awar, to sai ka guje su a kwakwalwarka. Misali sai ka dinga hango kanka cewa gasu sunzo maka kuma gashi ka guje musu ta hanyar tinanin wani abun kamar abinci, tattaki da sauransu.

    9. Ka shiga cikin mutane. Kowa ya sani kallon film ɗin batsa ba abinyi bane a cikin mutane, amma idan baka yarda ba zaka iya gwada kalla wanda nasan mutum bazai iya ba. Saboda haka, ka kasance cikin jama'a.

    10. Ka nemi taimakon masana. Idan daina kallon film ɗin batsa ya zama wahala a rayuwarka, ko kuma yana jawo maka wasu matsalolin, yana da kyau ka nemi malaman addini ko kuma malaman zamantakewa domin su taimaka maka.

    11.Ka nemi waya mara abubuwa da yawa. Yawancin mutane da suke kallon waɗannan fina-finan suna yinsu ne a cikin wayarsu babba. Saboda haka, idan kana son ka daina sai ka ɗauki matakin rabuwa da wayar hannunka domin ka nemo karama ko kuma wadda bazakaji daɗin kallon ba a ciki.

    12. Kayi aure. Idan rashin aure ne yake jawo maka kallon finafinan batsa, to abu mafi sauƙi shine kayi aure nan take. Idan kuma halin auren ne baka dashi to yana da kyau ka nemi malaman addini domin suyi maka bayani akan haramcin kallon finafinan batsa da kuma hanyoyin da ake bi domin a rage sha'awa da tayi ƙarfi sosai.

    WALLAHU A'ALAMU

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.