Hukuncin Gwajin Test Din "Genotype" Da Ake Yi Kafin Aure

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum warah matullah wabarakatuhu. Malam ina yini ya aikin lada Allah ya taimaka Ameen. Malam Dan tambayace dani akan test ɗin nan da ake kafin aure Wanda ake kira da GENOTYPE test to malam naga yanzu majority sai ansa biki yazo dab dazaran anje gwaji sai ace As +As ne sai kaji ance anfasa auren. Dan Allah malam a mahankar addini islama ya abun yake inason amin bayani. Saboda anacewa gudun wahala ne kar a haifo 'ya'ya marassa lafiya wato skill cell anaemia nagide. Allah ya kara basira kuma ya azurtaka da mata ta gari Ameen ya Hayyu Ya Qayyum.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikis Salaam Wa Ramatullahi Wa Barakatuhu:-

    Zuwan Zamani da kuma Yawaitar Abubuwa na Wannan zamanin Sabida cigaba ta hanyar Technology, Da ana Iya gano cututtukan da Ake Ɗauka ta hanyar Auratayya da zamantakewa. Kamar Jinyar HIV da GENOTYPE, wanda wannan wani gwaji ne da Ake ganowa Akan ɗan da waɗannan Ma'auratan Za su Haifa.

     Zai Iya Zuwa da Jinyar SIKILA da Sauran gwaje-gwaje da Ilimi ya Tabbatar da Su Sabida haka kenan, Ni a Nawa Tunanin Inaga Kamata Yayi ga wanda yake da Niyyar Yin Aure, Waɗannan Gwaje-gwajen Su zama Shi ne Mataki Na Ukku

    1. Mataki na Farko Shine, Yin Magana da ita wannan yarinyar, Domin Neman Amincewar ta da Karbar Soyayyar ka.

    2. Mataki na Biyu Shi ne, Neman Izini a Wajen iyayen ta na zuwa wajen wannan yarinyar. Idan har Sun Amince maka da zuwa wajen ta, Zaka sanar da su kuma Su Baka Izini Akan mataki na Ukku.

    3. Mataki Na Ukku Shine, Zaku je Ayi Muku Waɗannan Gwaje-gwajen guda ɗaya. Shine na GENOTYPE.

    Idan Magana ta yi Karfi Kuma, sai Aje ayi gwaji na HIV da Kuma Na PREGNANCY. Ma'ana gwajin da zai tabbatar da Cewar, babu ciki a Tattare da Ita.

    Tabbas a Shawara irin wadda Likitoci da kuma Musulunci yake Bayarwa ga Waɗanda Suka Samu Cewar Jinin su zai Haifar da Wanda yake da SIKILA. Sai a Hakura da wannan Soyayyar kawai. Kafin Ma Aje ga Maganar Auren. Sabida Za su Wahalar da Ɗan Da Zasu Haifa Lokaci bayan Lokaci Yana Cikin Wahala da Jin Ciwon Wannan Rashin Lafiyar. Haka Zalika Iyayen sa Suna Cikin Kashe Kuɗi da Wahalhalu da Kuma Rashin Samun Nutsuwa.

    Ga waɗanda Suka Amince da Cewar zasu yi Aure Akan Hakan, sai Suyi Hakuri da wannan Soyayyar da kuma wannan Auren. Idan Kuma Suna Ganin Kamar Ba zasu Iya Rabuwa ba Sabida Son Junan su. Sun Amince da Cewar zasu yi Aure Akan Hakan. Toh A Shawara sai su Hakura da Haihuwa. Duba da halin da zasu Jefa ɗan da zasu Haifa. Kuma ya Kamata Ma Su Sani Cewar, Idan Sun Amince da Cewar Zasuyi Aure da Sharadin Ba Zasu Haihu ba. Toh fa ya Kamata su sani Cewar. Daɗin Aure Da Ribar Sa Shi ne Haihuwa, Ko da Shi Namijin ba ya son Haihuwa. Sabida ana Samun Maza masu irin wannan Akidar na Rashin Son Haihuwa. Toh amma Ita Matar fa.?

    Babu Matar da zata so tayi Aure kuma  wayi Gari Wai ba zata Haihu ba. Bana Jin Akwai Macen da zata Amince da hakan. Sabida haka dai ta kowacce Fuska. Hakuri da wannan Auren a Nemi Wata, Itama ta Nemi Wani Yafi Alkairi. Idan Kuma Aka gano a ɗaya Gwajin, Aka tabbatar da Cewar wannan da zai Aura ko wannan da zata Aura yana ɗauke da Jinyar HIV. A Hakura da wannan Auren Shi ne yafi zama Alkairi.

     Kar ki ce Wai ke ba zaki Iya Rabuwa da wannan Saurayin Naki ba, toh Kika Rabu da Iyayen ki ma balle Saurayi. Ko kace ba zaka Iya Rabuwa da wannan Matar ba, Kuma ka Rabu da iyayen ka?

    1. AA+SS = Yayi dai-dai.

    2. AA+AA= Yayi dai-dai.

    3. AA+AS= Ba damuwa.

    4. AS+AS= Bai yi ba.

    5. AS+SS = Da Matsala.

    6. SS+SS= bai yi ba kwata-kwata.

    ABINDA YA SHAFI AURATAYYA TSAKANIN MIJI DA MACE

    Shawara shine idan ana so a kauce ma samun yara masu fama da matsalar shi ne a kauce ma dukwata hanyar da za ta kai ga samun yara tsakanin waɗannan genotypes din, SS, SC, CC, abu ne mai wuya wasu lokuttan a iya banbance wahalar da masu SS da CC suke sha.

     ALURA: AA genotypes normal ne. AS genotype ba wata alama ta sickler amma carrier ne, SS sickler ne. AC shi ma carrier ne amma ba wata alama a bayyane, CC wannan yana kusa ko kamada SS, SC yana fama da yawan matsalar karancin jini, da matsalar kashi da ya shafi Ɓargo.

    SHAWARA: Idan AS da AC suka auri juna suna da chance na samun sickler cikin yaran su da kashi 25% idan kuma suka auri SS ko SC suna da chances na haihuwar masu sickler kashi 50%, idan kuma SS ko SC suka auri junansu to za su rika haihuwar duka yaran masu sickler saboda SS da SC duk ɗayane banbancin kawai mai SS yafi mai SC shan wahala.

    Duk namiji ko mace idan ana so a kauce ma haihuwar yara masu matsalar to mai AC ko AS, SS ko SC ko CC su kaurace ma auren juna in ana so a kauce ma samun matsalar ga yara.

     Haka zalika. Idan Anyi gwaji na Wannan pregnancy ɗin aka tabbatar Da Ingantaccen Gwaji cewar wannan yarinyar tana ɗauke da Juna Biyu. Indai ba Kai ne kayi Mata Ba. Ka Hakura da ita zai fi zama Alkairi. Idan kuma ba haka ba. Ka Nace Akan Kai a Haka ma Zaka Iya Aurenta. Domin Akwai Masu irin Wannan kundunbalar. Toh fa ka tabbatar da Cewar, ba'a Aure da Cikin Wani. Idan kuma Kaine kayi Mata Cikin Babu lefi, zaka Iya Auren ta. Sai ta Haifa Maka Kayan ka a Gidan ka. sa'annan gwajin kamata yayi a je Asibiti Daban-daban kamar guda 4 Nan ne za'a tabbatar da gaskiyar gwaji.

    Allah Shine Masani.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.