Ina Fama Da Matsalar Yawan Tunanin Mutuwa

    TAMBAYA (130)

    Assalamu Alaikum warahamatullahiwabarakatuhu. Malam inaso abani shawara. Dan Allah

    Malam dan inada wata matsalane wajan wata biyu koda yaushe banida tunani da ya wuce sai na mutuwa kome nake koda second daya tunanin nan baya fita daga raina

    Shine nace abani shawara 😭😭 bana sakewa kwata kwata bana walwala

    ✍️AMSA A TAQAICE

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

    (An karbo daga Abu Hurairah (Radiyallahu anhu) yace: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: "Ku dinga yawan tuna mai tarwatsa farin ciki" ma'ana: mutuwa #Sunan Ibn Majah: 4258, An-Nasaa'i 1824, At-Tirmidhi 2307)

    Bismillaahir Rahmaanir Raheem

    Alhamdulillah

    To da farko dai yar uwa, ina tayaki murna domin kuwa kina da Imani

    A wannan zamanin da yawancin mutane basa son a dinga zancen mutuwa - mai Imani ne kadai yake iya tuna mutuwa a kowanne hali yake wanda kuma indai har ka tuno da mutuwa to zaka tuna makomar kalar aikin da kake a lahira, Aljannah ko Wuta

    Allah (Subhanahu wata'ala) yace

    ( كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ ۗ وَإِنَّمَا تُوَفَّوْنَ أُجُورَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۖ فَمَن زُحْزِحَ عَنِ النَّارِ وَأُدْخِلَ الْجَنَّةَ فَقَدْ فَازَ ۗ وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلَّا مَتَاعُ الْغُرُورِ )

    آل عمران (185) Aal-Imran

    Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijãrõrinku kawai ne a Rãnar qiyãma. To, wanda aka nĩsantar daga barin wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne yã tsĩra. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce jin dãɗin rũɗi.

    Da kuma ayar

    ( كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ ۗ وَنَبْلُوكُم بِالشَّرِّ وَالْخَيْرِ فِتْنَةً ۖ وَإِلَيْنَا تُرْجَعُونَ )

    الأنبياء (35) Al-Anbiyaa

    Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku.

    Da kuma

    ( كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ ۖ ثُمَّ إِلَيْنَا تُرْجَعُونَ )

    العنكبوت (57) Al-Ankaboot

    Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar da ku.

    Ba laifi bane musulmi ya dinga tuna mutuwa dalili kuwa shine shahararren hadisin da aka  karbo daga Abu Hurairah (Radiyallahu anhu) yace: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace

    "Ku dinga yawan tunawa da mai tarwatsa farin ciki" (ma'ana mutuwa)

    Sunan Ibn Majah 4258, An-Nasaa'i 1824, At-Tirmidhi 2307

    Kawai ki kwantar da hankalinki ki ci gaba da bautar Allah har mutuwa ta riske ki kamar yanda Allah (Subhanahu wata'ala) ya fadawa ManzonSa

    ( وَاعْبُدْ رَبَّكَ حَتَّىٰ يَأْتِيَكَ الْيَقِينُ )

    الحجر (99) Al-Hijr

    Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.

    Indai har tunanin mutuwa zai hanaki sakewa da walwala to bai kamata ki sakata ki wala a lokacin da kike bacci ba domin kuwa bacci kanin mutuwa ne saboda duk lokacin da mutum ya kwanta bacci to ransa baya jikinsa kamar yanda Allah (Subhanahu wata'ala) ya fada

    ( اللَّهُ يَتَوَفَّى الْأَنفُسَ حِينَ مَوْتِهَا وَالَّتِي لَمْ تَمُتْ فِي مَنَامِهَا ۖ فَيُمْسِكُ الَّتِي قَضَىٰ عَلَيْهَا الْمَوْتَ وَيُرْسِلُ الْأُخْرَىٰ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ )

    الزمر (42) Az-Zumar

    Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.

    To idan da ace mutane suna tuna mutuwa akai - akai kamar yanda kike tunawa haka ai da an dan samu raguwar wasu abubuwan. Duba ki ga yanda azzaluman shugabannin kasarmu suke sace kudaden talakawa, ko gajiya basa yi yanzu da ace suna yawan tunanin mutuwa kina ganin zasu ci gaba da satar da suke ? Tunanin mutuwa yayin aikata zunubi yana saka mutum gaba daya ya haqura da aikata wannan laifin domin duk sanda ka tuna mutuwa to zaka tuna haduwarka da Allah. Kuma mutuwar nan dai wajibi ce tun da ga Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) wanda Allah Azzawajallah yafi so fiye da kowa a cikin halittunsa amman Allah yace masa zaka mutu

    ( إِنَّكَ مَيِّتٌ وَإِنَّهُم مَّيِّتُونَ )

    الزمر (30) Az-Zumar

    Lalle kai mai mutuwa ne, kuma su mã lalle mãsu mutuwa ne.

    Ki koyi iya sarrafa tunanin mutuwar ta hanyar daina tada hankalinki, ki daina gudun mutuwar, kawai kedai ki shirya zuwanta a kowanne lokaci. Allah (Subhanahu wata'ala) yace

    ( قُلْ إِنَّ الْمَوْتَ الَّذِي تَفِرُّونَ مِنْهُ فَإِنَّهُ مُلَاقِيكُمْ ۖ ثُمَّ تُرَدُّونَ إِلَىٰ عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ )

    الجمعة (8) Al-Jumu'a

    Ka ce "Lalle mutuwar nan da kuke gudũ daga gareta, to, lalle ita mai haɗuwa da ku ce sa'an nan kuma anã mayar da kũ zuwa ga masanin fake da bayyane, dõmin Ya bãku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

    Ki tuno da dalilin da yasa fa aka halicci ita kanta mutuwar da rayuwa shine don ayi mana jarabawa

    ( الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ )

    الملك (2) Al-Mulk

    Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.

    Duk sanda kika tuna mutuwa to ki tuno da cewar a Aljannah fa ba'a mutuwa. Jin dadin wannan dawwamar ta Aljannah kadai ya isa ya tafiyar da wancan qunci da baqin cikin da kike na tunanin mutuwa. Allah (Subhanahu wata'ala) yace

    ( وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ )

    البقرة (82) Al-Baqara

    Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan, 'yan Aljanna ne, sũ a cikinta madawwama ne.

    Ki tuna firar dan Aljannah da dan Wuta, lokacin da dan Aljannah zai ce saura kadan ka halakani (batar dani) a duniya

    ( فَاطَّلَعَ فَرَآهُ فِي سَوَاءِ الْجَحِيمِ )

    الصافات (55) As-Saaffat

    Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.

    ( قَالَ تَاللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرْدِينِ )

    الصافات (56)

    Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."

    ( وَلَوْلَا نِعْمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ الْمُحْضَرِينَ )

    الصافات (57)

    "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."

    ( أَفَمَا نَحْنُ بِمَيِّتِينَ )

    الصافات (58)

    "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."

    ( إِلَّا مَوْتَتَنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ )

    الصافات (59)

    "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"

    ( إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ )

    الصافات (60)

    Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.

    ( لِمِثْلِ هَٰذَا فَلْيَعْمَلِ الْعَامِلُونَ )

    الصافات (61) As-Saaffat

    Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.

    A karshe ina jan hankalinmu daga ni harke da mu gaggauta neman gafarar Allah don rabauta da Aljannah wadda fadinta yakai sammai 7 da kassai 7 kamar yanda Allah (Subhanahu wata'ala) ya fada

    ( وَسَارِعُوا إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ )

    آل عمران (133) Aal-Imran

    Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nman gãfara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda fãɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta dõmin mãsu taƙawa.

    Ya Allah ka sa muyi kyakkyawan karshe.

    Wallahu ta'ala a'alam

     Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.