TAMBAYA (126)❓
Aslm Allah yakarawa mlm lapiya. Mlm tambayata shine wanine yazo da kudi sai nace yaban sai baze banba sai dai in yabani nabashi Alahira sai nace yabani sai yaban naci shin mlm ina da lefi A wajen Allah, Mlm atemaka a amsamin
AMSA❗
Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh
Alhamdulillah
Indai ya tabbata ka ci wannan kudin kuma ba bashi kake bin
sa ba to sai ka jira idan an tashi alqiyama ka yiwa Allah bayani dalla dalla
akan dalilin da yasa ka ci kudin tunda ai ya kafa maka sharadi cewar saidai ka
biyashi a lahira
Abinda yake nufi ka biyashi a lahira shine sallar da kake yi
da azumi da sadaka za'a dauke su ne a biyashi kudin da ka ci masa tunda a
lahira ba riga ba wando za'a tashi ballantana kayi tunanin saka kudi a
aljihunka
Ya Allah ka rabamu da cin haqqin al'umma ko da N5 ce
Wallahu ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta
astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.