Na Yi Kwana 40 Amman Jinin Haihuwan Bai Dauke Ba

    TAMBAYA (128)

    Assalamu Allaikum. Barka da safiya mllm, ya aiki. Mllm tambaya gareni Dan Allah

    Mllm macece ta haihu har tayi kwana 40 jini Bai dauke mata ba ,zatayi wanka ne taci gaba da sallah ko zata jirane har ya dauke ? Nagode mllm

    AMSA

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

    Alhamdulillah

    Idan har jinin ya ci gaba da zuba sannan kuma ya hade mata da jinin al'ada to zata dauke shi a matsayin jinin haila saboda abune mai yiwuwa jinin al'ada ya biyo bayan jinin haihuwa (an-nifas)

    Idan kuma jinin haihuwar ya ci gaba da zuba ne har bayan kwanaki 40 din sannan kuma bai hade da jinin al'ada ba to ba jinin haihuwa bane (an-nifas) kuma ba jinin al'ada bane (haidah), wannan shi ake kira da jinin al-Istihaadah (cuta) sai ta tuntubi likita

    Wallahu ta'ala a'alam

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.