Shekaru 10 da Rasuwa: Zuwa ga Marigayi Sarkin Kano Alh. Ado Bayero (1)

    Daga Sani Shehu Lere, Kaduna

    Ina fara wa da addu'ar shiga Kushewa " Assalamu alaikum Darul Kaumul Mu'amin, Wa'inna In sha Allahu La-ragibun" bayan haka.

    Ya aka ji da jimirin rayuwa 'Barzhakiyya"? Bisa Lissafawa, yau a kidayar "Girigori" 6 ga watan 6, kana da shekaru goma cif-cif da fakuwarka daga wannan duniya tamu mai cike da zub da jini zuwa rayuwar Barzakhu, Allah Yasa ana da isasshen guzuri na wannan doguwar tafiya, Mu ma Allah Ya bamu guzurin tassheku amin.

    Allah ya haskaka Kabarinka, nasan wasikata bata zame maka sabon abu ba, domin kuwa ba ita ce ta farko ba, kuma ba lallai ta zama ta karshe ba, matukar muna da ragowar numfashi, kuma matukar ana samun "Muhdasatul Umuri" musamman a Masarautarka.

    Idan Allah Yasa na baya basu bace Maka ba, wannan ita ce kwafi ta uku cikin wasikuna gare ka, inda nakan tsegunta maka halin da ka bar Masarautarka da kuma in da ta koma.

    A wasikar farko, na fada maka yadda ta kaya bayan rasuwarka, Inda aka hana Danka da Jama'ar Kano ke kauna wato Sunusi Ado ya gaji kujerarka, Inda aka musanya shi da jikan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi (Danka na zumunta kuma Surukinka) saboda kawai siyasa.

    Bayan cikar wa'adin masu gidansa kuma, shi kuma ya kasa yi wa bakinsa linzami, ita ma sabuwar gwamnati ta tsige shi tare da yiwa Masarautar kishiyoyi har guda hudu, aka mate gurbin Sunusi da Danka Alh. Aminu Ado, tare da tasa keyar tsohon Sarki zuwa wani Kauye da ke yankin Jahar Nasarawa, ko da yake daga bisani yayi amfani da alfarmar da yake da ita ya dawo Jihar Legos.

    Faruwar haka ke da wuya, Gidan Tijjaniya da ke Kasar Morocco tayi masa tukuici babba bisa tausaya wa ba bisa cancanta ba, da mukamin Khalifar Tijjaniyya na Afurka, wai don dai ya sami natsuwa, domin kasan mutumin da ya sa wa ransa zama Shugaba to baya samun natsuwa Sai da Shugabanci.

    To an dauka shikenan wannan matsala tazo karshe... Zan ci gaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.