Shekaru 10 Da Rasuwa: Zuwa Ga Sarkin Kano Alh. Ado Bayero (2) (Cigaba)

    To an dauka shikenan wannan matsala tazo karshe yanzu za a bar Masarautarka ta zauna lafiya, cin mutuncin ya tsaya Iya nan, a kuma bar iyalinka su magance matsalar zumunta ta cikin gida Ina! Ashe akwai ragowar Rina a kaba.

    Allah ya kyauta makwancinka, cikin shessheka na kuka nake fada maka cewa, bayan cikar wa'adin mulkin wannan gwamnatin, da samun nasarar gyauron waccan tsohuwar gwamnati sai kawai ta dawo cikin fushi da kudurin daukar fansa, a yanzu haka maganar nan da nake yi da kai, sun kara kiran saukakken Sarki daga Jihar Legos sun ayyana shi a matsayin sabon Sarkin Kano, tare da rushe sauran Sarakuna hudu ba tare da wata kwakkwarar dalili ba, suka kuma basu wa'adin sa'o'i 48 da su kwashe komatsensu su kama gabansu.

    Allah ya huci zuciyarka, a yanzu haka dai an sa adda mai kaifi an daddatsa gadon Sarautarka zuwa falle gida biyu, kafin Kotu ta Samar da matsaya. A yanzu haka dai an kafa tarihin da ba a taba kafa wa ba a Kasar Hausa na samuwar Sarakuna biyu a Masarauta daya Sai a Masarautarka Inda Surukinka Sunusi ke ayyana kansa a matsayin Sarki, Danka Aminu shi ma na zaman Fada a matsayin Sarki (Subhanallah).

    Allah Ya kara Maka rahama, wannan ita ce halin da Masarautarka take ciki, bamu san me zai faru gobe ba, Sai dai Rabbul Izzati.

    Danka Alh Aminu yanzu yana rayuwa ne a daya gidanka da ke Nasarawa cikin duhuvda rashin ruwan sha, domin kuwa bisa umurnin gwamnatin Jiha, an yanke masa wuta da ruwa da hana shigar duk wani tallafi daga gwamnatin Jiha, masoyanka ne kadai ke kai masa gudunmawar Jenareto da Man Dizil kafin lokacin da kotu zata zauna ta lalubi mafita a tsakaninsu.

    Babban dai abin muni da takaici shi ne, a yanzu 'yan siyasa sun yi nasarar tarwatsa gidanka da rarraba kawukan iyalanka, Wanda ko da nan gaba duk wanda yayi nasara a kotu to zai yi wuyar gaske ya samu goyon bayan sauran bangarorin, za a rinka zama ne irin zaman 'yan Marina, kowa da Inda ya fuskanta.

     Sa'annan kuma an yi nasarar jefa Masarautarka cikin harkar siyasa, Inda aka samar da rukunin 'yan santsi da 'yan tabo, anan gaba zai zama samun gadon kujerar Sarautar ta ta'allaka ne da kusancin ka da bangaren da yayi nasarar kafa gwamnati, wanda mu mun san baka gadar musu haka ba.

    Babban abin tsoron shi ne, ana ganin a nan gaba kadan, idan wata sabuwar gwamnatin da bata da alaka da kowace bangare tazo, tana Iya kawo wani wanda ma bai taba gadon Sarautar  ba ya haye karagar, domin an siyasantar da ita tamkar kujerar Kansila, Allah ya kyauta.

    Allah Ya inganta kwanciyarka, abubuwan na da yawa wai mutuwa ta je Kasuwa, na zabi wadanda zasu Iya faduwa ne na fada Maka, na bar marasa dadin jin a burgami na, yanzu dai mu bangaren al'ummar gari matakin addu'a muka dauka na Allah ya kawo mafita a wannan tirk-tirka, don haka, a nan zan dakata in yi sallama da kai, sai kuma badi idan har mai ara numfashi ya ara mana, zan dawo in labarta Maka matakin da kotu ta dauka a tsakaninsu, Wassalam, ka huta lafiya,

    Ni ne, a kodayaushe,
    Sani Shehu Lere (Lerawa 2024)
    (08062798146)

    Fadar Kano

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.