Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Idan Mutum Ya Yanka Rago Daya Shi Da Iyalansa Ya Isar Masa Layya?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum malam barka da warhaka ina da tambayoyi kamar haka

1. Shin idan mutum ya yanka rago ɗaya shi da iyalansa ya isar masa layya?

2. Shin mutum 8 za su iya yanka rago ɗaya?

3. Shin mutum 8 za su iya tarayya akan saniya ɗaya ko rakumi ɗaya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

1. SHIN RAGO ƊAYA YA WADATARWA MUTUM ƊAYA DA IYALINSA?

Rago ɗaya ta wadatar a matsayin udiya ga mutum ɗaya da iyalansa da wanda yake so a cikin musulmi. “Nana A’isha (RA) ta ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi umurni da a kawo masa rago mai baqin qafafu, baqin ciki da bakin baya, da bakin (digo digo) a idonsa, a zo masa da shi, don ya yi layya da shi. Sai ya ce wa Aisha: “Ba ni wukar,” sai ta yi haka ta miko masa. Ya karɓa, sannan ya ɗauki ragon, ya kwantar da shi a kasa, sannan ya yanka (wato ya shirya yanka), yana mai cewa: “Da sunan Allah, Ya Allah ka karɓa (wannan hadaya) a madadin Muhammadu da iyalan Muhammadu da al’ummar Muhammadu”. Sannan ya yanka dabbar.” (Muslim ne ya ruwaito).

Abu Ayyub al-Ansariy (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “A lokacin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) mutum ya kan yanka ragonsa don kansa da kuma iyalan gidansa, sun kasance suna yanka tunkiya su na cin wani su bada wani.” (Ibn Majah da Tirmizi suka ruwaito shi, wanda ya sanya shi a matsayin sahih. Albani kuma ya sanya shi a matsayin sahih a cikin Sahihul Tirmizi, 1216).

Idan mutum ya yi hadaya da tunkiya ɗaya ko akuya a madadin kansa da iyalinsa, wannan ya wadatar masa da duk wanda ya nufa cikin iyalinsa, rayayye ko matacce. Idan kuwa bai yi niyya takamammiya ba to ya haɗa da duk waɗanda suke cikin wannan kalmar ta (iyali ko gida) na al'ada ko na harshe.

A al'adance, yana nufin duk wanda yake tallafawa, wato wa'inda suke kasansa, daga mata, 'ya'ya da dangi ko ma wanda bai da alaqa da su. A fannin harshe, kuma ya haɗa da duk waɗanda suke da alaƙa da shi na ’ya’yansa da zuriyar mahaifinsa da kakansa da kakansa.

Kashi ɗaya cikin bakwai na raƙumi ko saniya yana daidai da tunkiya ɗaya ne. Idan mutum ya yanka kashi ɗaya bisa bakwai na rakumi ko saniya a madadin kansa da iyalansa, hakan ya wadatar. Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam ya ce kashi ɗaya bisa bakwai na rakumi ko saniya yana maye gurbin tunkiya a wajen hadaya da ake yi a lokacin Hajji. Don haka wannan ma ya shafi uduyya ne domin babu wani bambanci tsakanin udiyya da hady a cikin wannan mas’ala.

2. SHIN MUTANE ZA SU IYA RABA RAGO/TUNKIYA/AKUYA (TUMAKI)?

Idan mutum biyu ko fiye suka sayi tunkiya suka yanka, wannan bai wadatar musu ba, domin ba a ruwaito irin wannan abu ba a cikin Alqur'ani da Sunna ba.

3. MUTUM 8 ZA SU IYA RABA RAKUMI KO SANIYA?

Haka nan idan mutum takwas ko fiye da haka suka raba rakumi ɗaya ko saniya, hakan bai wadatar musu ba su ma (amma ya halatta mutum bakwai su raba rakumi ko saniya). Domin kuwa ayyukan ibada sun kasance kamar yadda Alqur'ani da Sunna suka shar'anta ne kuma ba ra'ayin mutum ake bi ba. Ba ya halatta a ketare iyakokin da aka gindaya dangane da nawa ne za a yi ko kuma yadda za a yi. Wannan ba ya rasa nasaba da shigar da wasu cikin ladan, domin an ruwaito cewa babu iyaka ga adadin mutanen da za a yi layya a madadinsu.

Kuma Allah ne Mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments