Shin Kun San Irin Addu'o'in Da Ya Kamata Ku Yi Ranar Arfa? Ga Samfur

    Bismillahir Rahmanir Rahim

    وعن عبد الله بن عمرو بن العاص رضي الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: خير الدعاء دعاء يوم عرفة، وخير ما قلت أنا والنبيّون من قبلي: لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك، وله الحمد، وهو على كل شيء قدير. رواه الترمذي (3585) وحسَّنه الألباني في " صحيح الترغيب " (1536) .

    Dubi da hadisin Abdullahi ɗan Amru ɗan As (Allah Ya yarda dasu), yace Manzon Allah (saw) yace: "Mafi alkhairi addu'a itace addu'ar ranar Arfa. Kuma mafi alkhairin abinda nace da ma duk annabwan da suka zo kafin ni, shine La'ilaha illallahu wahadaHu la sharika lahu laHul mulki wa laHul hamdu wa Huwa ala kulli shai'in ƙadeer. (Tirmizy ya ruwaito, kuma Albany ya Hassan shi).

    GA samfur na irin ADDU'O'IN da ya kamata mu riƙa muyi ta maimaitawa, musamman bayan La'asar zuwa Magriba. Kamar yadda Abu Nu'aim ya ruwaito daga Aɗa'u ɗan Abi Rabahin cewa, "idan mutum ya samu dama ya keɓa da maraicen ranar Arfa, toh ya aikata" saboda ana sanya ran  karɓan addu'a yafi kaifi a wannan lokacin.

    Toh shawari anan shine, kada mu dage da roƙon kuɗi zalla (you know, ƴan Najeriya, damuwar kenan 🤪). Kamata ya yi muyi ADDU'O'IN wa kawukan mu da iyayen mu (rayayyunsu da matattunsu), sauran ƴan'uwa da abokan arziƙi, al'umman musulmi baki ɗaya da ma ƙasar, jihohi mu da kuma uwa uba, shugabannin mu. Kada mu manta, ƴan'uwan mu musulmai a Falasɗin musamman a Gaza, suna buƙatar ADDU'O'IN mu na musamman.

    Muyi nazarin waɗannan adduoin;

    1. La'ilaha illallahu wahadaHu la sharika lahu laHul mulki wa laHul hamdu wa Huwa ala kulli shai'in ƙadeer. Tunda Manzon Allah(saw) yace shine mafificin abinda za'a faɗi, toh muyi ta maimaitawa.

    2. Rabbana atina fiddunya hasanatan wa fil akhirati hasanatan wa ƙina azaban Nar. Anas (RA) ya ruwaito cewar Manzon Allah(saw) yana yawan maimaita wannan addu'ar. Muyi ta maimaitawa, domin ta ƙunshi kusan duk abinda zamu roƙa a ɗaiɗai.

    3. AllaHumma inny as'alukal afwa Wal afiyata fiddunya Wal akhira. Saboda hadisin Anas da yazo a Musnad Ahmad, Sunanut-Tirmizy da Sunan Ibnu Majah, cewar wani mutum yazo ya tambayi Manzon Allah akan wani addu'a ne yafi falala, sai Manzon Allah Ya gaya masa wannan addu'ar. (Shu'aibul Arna'uɗ yace Hasan ne ligairihi, Amma isnadinsa me rauni ne).

    4. Rabbi inni zalamtu nafsy zulman katheeran, fagfirly magfiratan min indik, war hamny innaka antal gafurur-Raheem.

    5. la'ilaHa illa anTa subhanaKa inni kuntu minazzalimin addu'ar annabi Yunusa.

    6. Hasbunallahu wa ni'ima wakil, alallaHi tawakkalna. Addu'ar Annabi Ibrahim.

    7. Hakanan, idan zamu roƙa wa shugaba ni shiriya, ko mu roƙi Allah Ya ƙwata mana wani haƙƙin mu, kamar halinda ake ciki a ƙasar nan da jihohi dabam dabam na zalunci. Ga tsadan kaya, ga kora daga wajajen kasuwa da sana'a, babu gaira babu dalili aka hau ɗaga mutane a inda suke neman abinda suke rufa asirin kansu da na iyalan su. Toh zasu iya addu'ar Allah Ya ƙwato musu haƙƙin su, kuma Allah zai amsa. Amma zasu iya la'akari da wasu dalilan, kamar yadda ake cewa, shi al'amarin Public Policy ko leadership and management, Abu ne sai wanda yake kai ke iya fahimtar me yafi da cewa ayi a koda yaushe, ya yin irin wannan dokoki. Koma meye, ai ana la'akari da halin ƙunci da talakawa kan iya shiga.

    8. Ya Allah ka ba mu lafiya da zaman lafiya a gidajen mu, anguwaninmu, garuruwanmu, ynkunanmu da ma ƙasa baki ɗaya.

    9. Ya Allah Ka shiryi shugabanninmu, Kayi riƙo da hannuwa su zuwa daidai.

    10. Ya Allah Ka shiryi al'umman mu maza da mata, da matasa. Ka ɗauramu baki ɗaya a hanyar daidai, Ka rabamu da aikin ashsha.

    11. Ya Allah Ka yaye mana duk wata damuwa, masifa, bala'i, matsala da jinya.

    12. Ya Allah kayi katangan ƙarfe tsakanin mu da duk wani mugu, azzalumi, maha'inci, mayaudari.

    13. Ya Allah duk me nufin mu da sharri da hassada da ƙyashi, da cuta, da ƙulle ƙulle, da makirci, da musgunawa, da tozartawa, Ka mana maganinsa. Ka shirye shi, idan ba me shiryuwa bane, ka mana maganinsa, ka mayar masa da ƙullinsa kansa. Ameen

    Yanada muhimmanci mu sani cewar, wanda duk Allah Yaja kwnansa zuwa yau, toh Ya masa falala, kuma Ya bashi babban rabo. Don haka kar ayi ƙasa a gwiwa, a himmatu da ADDU'O'IN alkhairi. InshaAllah za'a dace.

    Mu sanya juna a ADDU'O'IN mu na yau. Ku tuna dani cikin ADDU'O'IN ku, ku roƙamin sabati da cikawa da shahada da rayuwa mai amfani.

    Allah Ya datar damu, ameen, Ya zil Arshil Majeed, Ya Hayyu Ya Qayyum, Ya sami'ud Du'a.

    Daga Zauren Ko Ka San?
    https://chat.whatsapp.com/D2jlYWCJKhpAG5xnWDKy0k

    Admin:

    Phone: +2348036806678
    Email: yusufaumar97@gmail.com

    Ko Ka Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.