Shin Sunan Rumaisa'u Yana Da Asali?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum. Mene ne asalin sunan Rumaisa'u kuma a zamanin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) akwai mai sunan, in akwai a ba ni tarihin ta?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikum assalam. Rumaisa'u suna ne na ɗaya daga cikin sahabbai mata, ita ce ta haifi Anas ɗan Malik, hadimin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam), ita ce ta kai shi wajan Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) don ya dinga masa hidima. Ta auri Abu-Ɗalha, shahararren Sahabi mutumin Madina, kuma ta sanya sadakinta Musuluntar Abu-Ɗalha. An fi saninta da sunan Ummu-sulaim, tana daga cikin mata masu hikima, akwai mahaddatan Al'Qur-ani da yawa da suka fito daga tsatsonta.

    Allah ne mafi sani.

    Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.