Tarayya A Kan Layya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin ya halatta mai layya da wanda yakeson yin walima su haɗu su sayi saniya ko raqumi suyi layya?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Ya Hallata tarayya akan saniya ko raqumi, koda Wasu daka cikin Waɗanda akayi taraiyyar dasu, su ba layya suka niyyataba, kawai suna San Samun namane don suyi Walima dashi, ko don suci, ko dan Sayarwa da sauransu.

    Nawawi Allah yajiqansa da rahama acikin Al-maj-mu'u (8/372) ya ce: Ya halatta Mutum bakwai su haɗu akan raqumi ko Saniya don yin layya, mutanen gida ɗayane gaba ɗayansu, ko gidansu daban, Ko Nama sukeso kawai, Wanda ya niyyaci layya cikinsu ta Isar masa, layyar Bakance ce kota Nafila, Wannan shine mazhabar mu, Imamu Ahmad ya faɗa da jamhur ɗin Malamai.

    Ibnu Qudama acikin Al-Mugni (13/363) yace: Raqumi Ya Isarwa mutum bakwai, haka Saniya, wannan Shine Zancen mafi yawan Malamai, Wanda Suka haɗu akansu mutanen gida ɗayane, ko ba mutane gida ɗaya bane, Layyar wajibi kota Nafila, Nama Wasunsu suke so, ko wanne ɗaya daka cikinsu kasonsa ya isar masa, niyyar wani bata cutar dashi.

    Babu laifi kayi taryya da Abokanka ku bakwai kuyanka saniya, dakai Da wanda yanaso ya Samu nama ne dan yayi walima, ko ya Sayar ko yaci.

    Shekarun da ake buqata wajan layya da Saniya Shine shekara biyu, wacce bata kai hakaba bai halatta layya da itaba, koda tana da yawan Nama.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.