Manyan baƙi daga ciki da wajen Nijeriya ne suka haɗu da sauran jama'ar da Allah ya amincewa, ciki kuwa har da mai wannan rubutu a "Matan Fada" dake garin Argungu inda nan ne babbar fadar Kabawa a duk inda suke cikin duniya tun da Sarkin Kabi Yakubu Nabame ya ƙirƙire ta a cikin 1840s, domin shedar kawo ƙarshen gasar bikin kamun kifi da wasannin al'adun gargajiya na Argungu (Argungu Fishing & Cultural Festival) na shekarar 1981, a ranar 28/02/81.
Bikin ya samo asali ne a shekarar 1934, lokacin da
Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Hassan ɗan
Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu
Bello ɗan
Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio
tagammadahullah birahamatihi da ya yi Sarauta daga shekarar 1931 zuwa 1938 ya
samu amincewar Marigayi Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Muhammadu Sani (ya yi
Sarauta daga shekarar 1934 zuwa shekarar 1942) ya zo Argungu ziyarar sada
zumunci da gyaran zamantakewa tsakanin Masarautunsu( Sokoto da Argungu) saboda
lamurran da suka faru tsakaninsu a can baya.
Domin ƙawata
wannan ziyarar ne Marigayi Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Muhammadu Sani ya
shirya bikin al'adun gargajiya na Kabawa, ciki kuwa har da kamun kifi wanda
daga nan ne aka haifi wannan ƙasaitaccen
biki na ƙasa da ƙasa
da ake kira "Argungu Fishing & Cultural Festival a turance ya zuwa
yau.
A wannan rana ta 28/02/1981 ne, a gaban Marigayi Mai
girma Mataimakin Shugaban Ƙasar
Tarayyar Nijeriya na wancan lokacin, Dr. Alex Ekwueme da tsofafin Gwamnonin
Jihohin Kano da Rivers, Marigayi Alhaji Mohammed Abubakar Rimi da Marigayi Cif
Melford Okilo da mai masaukin baƙi,
tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Marigayi Alhaji Shehu Mohammed Kangiwa (Turakin
Kabi) da manyan Sarakuna da sauran muhimman mutane, Malam Maidamma Ɗan Dare daga Ƙaramar Hukumar Mulkin Birnin Kebbi ya
zamo zakara a gasar da kama kifi mafi girma.
Ya samu nasarar kama kifin da ya yi kimanin kilo 70 a
wannan rana. Aka gwangaje shi da kyautar Naira dubu ɗaya
(#1, 000.00) da Babur ƙirar
Honda Belly sabo da kujerar aikin Hajji da agogon hannu da kuma bandur na yadi
guda ɗaya.
An samu ƙarin
bayani daga Mujallar Zaruma, A Cultural Magazine of Sokoto State, February,
1982.
Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin
Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.
08149388452, 08027484815.
birninbagaji4040@gmail.com
Asabar, 27/07/2024.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.