Ana Bi Na Bashin Kudi Ko Zan Iya Barin Garin Don Na Nemo Kudin Da Zan Biya

    TAMBAYA (140)

    Aslm malan barkanka da warhaka dan Allah malan shin. In anabin mutum bashi yayi iya bakin kokarinsa dan yaga yabiya amma inhar hakan bata samuba ga ana neman wala kantashi shin yahalarta yabar gari ya je can wani gurinda baza aganshiba domin yayi kokarin neman abunda zaibiya wannan bashi

    ✍️AMSA A TAQAICE

    (Ya halatta amman da sharadin zaka nemo halak ne ka biyashi kuma bazaka fifita wata buqatar akan ta biyan bashin ba)

    Bismillaahir Rahmaanir Raheem

    Idan har zamanka a inda kake zai iya zama silar tozarci a gareka to ya halatta ka je ka nemo kudin da zaka biya

    Domin kuwa ba kyau a tozarta kafiri ballantana kuma musulmi. Ka sani cewar sauke bashin nan shine abu na farko da zai dinga fado maka idan har ka yi bulaguro zuwa wani garin la'akari da bashi nauyi ne mai zaman kansa. Kuma Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ba ya sallatar gawa indai ana binta bashi har sai an biya ko kuma har sai wani ya yarda ya dauke wannan bashin

    (Duba littafin: "Ahkamul Jana'iz" na Shaikh Muhammad Nasiriddin Al-Albaany, Rahimahullah)

    Sannan kuma ka yawaita karanta addu'ar da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya koyar ga duk wanda ake binsa bashi, ga addu'ar kamar haka

    اللّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحُزْنِ، وَالعَجْزِ وَالْكَسَلِ وَالْبُخْلِ وَالْجُبْنِ، وَضَلْعِ الدَّيْنِ وَغَلَبَةِ الرِّجَالِ.

    Allahumma innee a'oothu bika minal-hammi walhuzn, wal'ajzi walkasal, walbukhl, waljubn, wadal'id-dayni waghalabatir-rijal.

    Ya Allah! Ina neman tsarinka daga kunci, da bakin ciki, da kasawa, da lalaci, da rowa, da tsoro, da nauyin bashi, da rinjayen mazaje.

    (Hisnul Muslim)

    Wallahu ta'ala a'alam

     Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.