Ticker

Baban Luba, Uban Nana: Sarkin Sudan Na Wurno, Alh. Shehu Malami

"Baban Luba, Uban Nana,

 Baban Aminu Alh. Shehun Malami,

 Ba da kai aka wargi ba,

 Ginshik'in Marahwa abag gasa da kai".

Inji Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun a cikin faifan da ya yi wa Marigayi Maigirma Sarkin Sudan Na Wurno murabus, Alhaji Shehu Malami OFR CON mai Turke "Ba da kai aka wargi ba, ginshik'in Marahwa abag gasa da kai", Allah ya kyauta makwanci, amin.

Luba wadda ake yi wa laƙabi da "Yar Kaɗan" ƙanwar Sarkin Sudan Shehu Malami ce, Mahaifinsu ɗaya watau Sarkin Sudan Bello. Amma a hannun Sarkin Sudan Shehu Malami ta tashi domin shi ya aurad da ita ga mijinta na farko Marigayi Senator Aliyu Mai Sango Abubakar III Durumbun Sakkwato har suna da ɗa namiji da ake kira Sada.

Bayan rasuwarsa ne ta auri Marigayi Alhaji Sahabi Dange yanzu haka a gidansa dake Abuja take zaune.

Al'adar Hausa /Fulani da ake cewa "Babban Wa Mahaifi" shi ne ta shigo a zaman Luba da Sarkin Sudan Shehu Malami domin haka ne ta ɗauke shi a matsayin Uba.

Nana kuma ɗiyar Ƙanensa, Abu /Abubakar ce. Abubakar da Sarkin Sudan Shehu Malami Mahaifinsu ɗaya, watau Sarkin Sudan Bello. Ga al'adar Bahaushe ta zama ɗiyar Sarkin Sudan Shehu Malami.

Aminu kuma ɗan Sarkin Sudan Shehu Malami ne na cikinsa.

Inda ya ke cewa "Zaki gwarzon Sada mai jiran daga Bajinin Ali", Uban Kiɗi na nufin Sada Bello, Ƙanen Sarkin Sudan Shehu Malami domin Mahaifinsu ɗaya, watau Sarkin Sudan Bello.

Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, ya yalwata bayanmu, amin.

Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.

Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.
08149388452, 08027484815.
birninbagaji4040@gmail.com
Lahadi, 07 /07/2024.

Post a Comment

0 Comments