Barden Tsangayun Hausa Na Farko: Ruwa Ba Ya Tsami Banza

    Hon. Dr. Balarabe Shehu Kakale Shuni
    Hon. Dr. Balarabe Shehu Kakale Shuni

    Tun yana karatun Allo a Makarantar Malam Bello Mai Wurno dake Unguwar Mad'unka a cikin Birnin Sakkwato, Hon. Dakta Usman Balarabe Shehu Kakale Shuni, Tsohon ÆŠan Majalisar Wakilai ta Tarayya da ya wakilci Mazab'ar Tureta /Dange, Shuni /Bod'inga ya ke yiwa karatun wani kallo na musamman a zuciyarsa.

    Duk da karatun zamani da ya yi har ya kai matsayin ƙwararren likita a sashen Radiology bai sa ya zubar da wannan tunani nasa akan karatun Allo ba.

    Sai gashi sannu a hankali haƙarsa ta cimma ruwa domin kuwa zamansa a Majalisar Wakilai ta Tarayya daga shekarar 2019 zuwa 2023 ya bashi damar yin tsayin gwamin Jaki sai da ya ga ƙudurinsa na ƙirƙiro Hukumar Kula da Almajirai da bai wa Yaran da basu shiga Makarantu damar samun Ilmi (National Commission for Almajiri&Out-of-School Children Education, NCAOOSCE) ya cimma gaci.

    Alhamdulillahi! Domin yabawa wannan namijin ƙoƙari da kuma ƙarawa masu tunani irin nasa ƙwarin gwiwa, Mai Martaba Sarkin Daura na 60, Alhaji Dr. Umar Farouk Umar da yan majalisarsa suka damk'a masa wannan sarauta ta Barden Tsangayun Hausa.

    Bahaushe ya na cewa "Ruwa baya tsami banza". Malam Muhammadu Agali da ya fito daga Ƙabilar Buzaye dake Jamhuriyar Nijar ta yanzu ne ya shigo yankin Kogin Rima ya na sana'arsa ta Wanzanci har ya zauna a yankin Rikina daidai lokacin da Sarkin Sullub'awa watau Arɗo Malam Manuri da jama'arsa ke kai komo wajen taimakawa masu jihadin jaddada addinin musulunci na Daular Usmaniya ƙarƙashin jagorancin Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi, kuma ya bayar da tasa gudummawa.

     Malam Muhammadu Agali ne ya haifi Malam Abubakar Akawal, Malam Abubakar Akawal ne ya haifi Malam Muhammadu Barmo wanda ya zauna a wani Ƙauye da ake kira Heterete a cikin gundumar Shuni, Ƙaramar Hukumar Mulkin Dange/Shuni, Jihar Sakkwato inda ya auri wata mata da ake kira A'isha /Indo da mahaifanta suka fito daga Talata Mafara ta Jihar Zamfara ta yau. Sune suka haifi Alhaji Usman /Shehu Kakale Shuni a shekarar 1929 a wannan Ƙauyen (Heterete).

    Alhaji Usman /Shehu Kakale Shuni ne ya haifi Hon. Dr. Usman Balarabe Shehu Kakale Shuni a Ƙofar Taramniya a Birnin Sakkwato, ranar 8/11/1974.

    Hajiya Halimatu/Inna Malama 'yar Malam Ubandawaki Umaru ce, Malam Ubandawaki Umaru ɗan Sarkin Tambuwal Malam Haruna ne, Sarkin Tambuwal Malam Haruna ɗan Sarkin Tambuwal Malam Umaru ne, Sarkin Tambuwal Malam Umaru ɗan Sarkin Tambuwal Malam Muhammadu Buhari ne, Sarkin Tambuwal Malam Muhammadu Buhari ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne, wannan baiwar Allah ita ce Mahaifiyar Hon. Dr. Usman Balarabe Shehu Kakale Shuni, Barden Tsangayun Hausa. Haƙiƙa Ruwa bai yi tsami a banza ba.

    Allah ya sakawa Mai Martaba Magajin Bawo, Sarkin Daura Alhaji Dr. Umar Farouk Umar da mafificin alherinsa akan aza wannan ƙwarya daidai gurbinta.

    Allah ya ja zamanin Mai girma Barden Tsangayun Hausa, Honorable Dr. Usman Balarabe Shehu Kakale Shuni, amin.

    Ibrahim Muhammad ÆŠanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya

    08149388452, 08027484815.
    birninbagaji4040@gmail.com
    Alhamis, 25/07/2024.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.