Bashi A Kan Mamaci

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum. Wanda ya rasu ana bin sa bashi kuma wani daga cikin ’ya’yansa ya ce ya ɗauke masa, to wai duk da haka baya cikin kwanciyar hankali a ƙabarinsa, ko da kuwa shi ɗin shahidi ne?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    Al-Imaam Abu-Daawud At-Tayaalisiy ya riwaito hadisi a cikin Musnad ɗinsa daga Sahabi Jaabir (Radiyal Laahu Anhu) ya ce

    تُوُفِّيَ رَجُلٌ فَغَسَّلْنَاهُ وَحَنَّطْنَاهُ وَكَفَّنَّاهُ، ثُمَّ أَتَيْنَا رَسُولَ اللهِ - صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - لِيُصَلِّيَ عَلَيْهِ، فَخَطَّ خَطًّا، ثُمَّ قَالَ: هَلْ عَلَيْهِ دَيْنٌ؟ قُلْنَا: نَعَمْ، دِينَارَانِ، قَالَ: صَلُّوا عَلَى صَاحِبِكُمْ، فَقَالَ أَبُو قَتَادَةَ: يَا رَسُولَ اللهِ، دَيْنُهُ عَلَيَّ، فَقَالَ رَسُولُ الله - صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -: هُمَا عَلَيْكَ حَقَّ الْغَرِيمِ، وَبَرِئَ الْمَيِّتُ، قَالَ: نَعَمْ، فَصَلَّى عَلَيْهِ، ثُمَّ لَقِيَهُ مِنَ الْغَدِ، وَقَالَ: مَا فَعَلَ الدِّينَارَانِ؟ قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّمَا مَاتَ أَمْسِ. ثُمَّ لَقِيَهُ مِنَ الْغَدِ، فَقَالَ: مَا فَعَلَ الدِّينَارَانِ؟ فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، قَدْ قَضَيْتُهُمَا، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ - صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -: الآنَ، بَرَّدْتَ عَلَيْهِ جِلْدَهُ.

    Wani mutum ya rasu sai muka yi masa wanka, muka sanya masa turare, muka sanya shi a cikin likkafani, sannan muka je wurin Manzon Allaah domin ya yi masa sallah. Sai ya taho ya taka ’yan taki kaɗan, sannan ya ce: Ko akwai bashi a kansa? Muka ce: E, dinare biyu. Ya ce: Ku yi wa mutuminku sallah! Sai Abu-Ƙataadah ya ce: Manzon Allaah! Bashin nasa sun dawo kaina. Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Sun dawo kanka a matsayin haƙƙin wanda ake bi bashi, kuma mamacin ya kuɓuta? Ya ce: E. Sai kuwa ya yi masa sallah. Washegari ya haɗu da shi ya ce: Yaya batun dinare biyun nan? Ya ce: Manzon Allaah! Jiya-jiyan nan ne fa ya rasu! Sannan da ya sake haɗuwa da shi washegari, ya ce: Yaya batun dinare biyun nan? Ya ce: Manzon Allaah! Ai na gama biyan su. Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Yanzun ne ka sanyaya masa jikinsa! (Musnadut Tayaalisiy: 1778, kuma Al-Albaaniy ya hassana shi a cikin Ahkaamul Janaa’iz, shafi: 16).

    Wannan ya nuna: Mamacin da ake bin sa bashi yana cikin azaba a cikin ƙabarinsa, matuƙar dai ba a biya masa ba. Domin ma’anar cewa: ‘Yanzun ne ka sanyaya masa jikinsa’ shi ne: Saboda dalilin ɗauke azabar da ake yi masa a bayan biyan bashin nasa. Haka Al-Albaaniy ya fassara a ta’aleeƘinsa a cikin Ahkaamul Janaa’iz, shafi: 16.

    Amma a kan ko wannan matsalar ta shafi mai mutuwar shahada, sai mu dubi hadisin da Al-Imaam Muslim ya fitar a cikin littafinsa, daga Abu-Ƙataadah cewa: Watarana Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya tsaya a cikinsu ya gaya musu cewa: Jihadi fi sabilil laahi da imani da shi su ne mafi fifikon ayyuka. Sai kuwa wani mutum ya miƙe ya ce: Manzon Allaah! Yanzu idan aka kashe ni fi sabilil laahi ya ka gani, shin wannan zai kankare mini laifuka na? Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: E, idan dai aka kashe ka fi sabilil laahi a halin kana mai haƙuri kuma mai yi don Allaah, kuma kana mai fuskantar maƙiya ba mai juya musu baya ba. Sai kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Yaya ma ka ce? Mutumin ya ce: Me ka gani idan aka kashe ni fi sabilil laahi, shin wannan zai kankare mini laifuka na? Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

    «نَعَمْ، وَأَنْتَ صَابِرٌ مُحْتَسِبٌ، مُقْبِلٌ غَيْرُ مُدْبِرٍ، إِلَّا الدَّيْنَ، فَإِنَّ جِبْرِيلَ عَلَيْهِ السَّلَامُ قَالَ لِي ذَلِكَ»

    E! Idan dai a halin kana mai haƙuri, mai yi don Allaah ne, kuma mai fuskantar maƙiya, ba mai juya musu baya ba. Sai dai bashi. Mala’ika Jibril (Alaihis Salaam) ne ya gaya mini hakan. (Sahih Muslim: 1885).

    Wannan ya nuna, kamar yadda malamai suka faɗa: Mutuwar shahad…

    [5:55 pm, 09/07/2024] Malam Khamis Yusuf Tambayoyi 2: SUJJADA ƘABLI DA BA'ADI

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum warahmatullah. Malam barka da yamma, so nake don Allah malam aƘara mana bayani kan Ƙabli da ba'adi, da kuma dalilan da ke sa a yi su. Allah ya saka wa malam da alkhairi.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salamu.

    SUJJADA ƘABLIYYA: ita ce sujjada guda biyu da ake yi kafin a yi sallama ta dalilin rage wani aiki daga cikin ayyukan sallah da mantuwa.

    Sujjada Ƙabliyya sunnah ce ba farilla ba. Ana yin sujjada Ƙabliyya ce bayan mai sallah ya kammala karatun tahiya, kafin ya yi sallama sai yayi kabbara ya yi sujjadu guda biyu, daga nan sai ya sake yin tahiya ya yi sallama. Wasu malaman kuma suka ce ko bai sake yin tahiya ba, zai iya yana gama sujjadan ya yi sallama.

    Idan kuma mai sallar da sujjada Ƙabliyya ta same shi ya mance bai yi ta ba har sai bayan ya yi sallama, to babu laifi, sai ya yi sujja ba'adiyya (sujjada bayan sallama) a madadinta.

    Amma ba duk ayyukan sallah ne idan aka mance aka rage su ba ne sujjada Ƙabliyya take isar masu ba, sujjada Ƙabliyya tana isarwa ne kawai a lokacin da mai sallah ya mance da sunnah ɗaya ko biyu ko fiye daga cikin sunnonin sallah, misali mutum yana sallah sai ya mance da kabbarori biyu, ko ya mance da faɗin 'Sami'allahu liman hamidahu' sau biyu, ko ya mance da zaman tahiya ta farko a sallah mai raka'a uku ko mai raka'a huɗu, to a irin nan ne sujjada kafin sallama (Sujjada Ƙabliyya) take isarwa.

    Wato kenan sujjada Ƙabliyya ba ta isarwa ga mai sallar da ya mance da wani farali daga cikin farillan sallah. Wannan na nufin idan mai sallah ya mance da wani farali daga cikin farillan sallah dole ne sai ya koma ya yi wannan farali da ya mance da shi, misali mutumin da ke sallah, a maimakon ya yi sujjada guda biyu kamar yadda aka saba kawai sai ya yi sujja ɗaya, ya mance ya miƘe zuwa raka'a ta biyu, to a nan hukuncinsa dole ne ya dawo ya yi wannan cikon sujjada ɗaya da ya mance da ita, sannan ya miƘe ya ci gaba da yin raka'a ta gaba, bayan kuma ya idar da sallarsa sai ya yi sujjada ba'adiyya.

    Wannan misali kenan a sujjada, haka hukuncin yake a sauran farillan sallah, kamar karatun Fatiha, da ruku'u, da ɗagowa daga ruku'u, da sauransu. Duka waɗannan idan mutum ya mance da su a cikin sallah, to dole ne sai mutum ya koma ya kawo su, sannan kuma bayan ya kawo su, idan ya idar da sallarsa ya sallame zai yi sujja bayan sallama wato (sujjada ba'adiyya)

    Wato kenan dai a taƘaice, sujjada kafin sallama ba ta isarwa ga gyara sallar da aka mance da farilla daga cikin farillan sallah har sai an koma an yi wannan farillan da aka mance da ita kamar yadda malaman FiƘhu suka ayyana.

    SUJJADA BA'ADIYYA: ita ma sunnah ce. ita ce sujjads guda biyu da ake yin su bayan an sallame sallah ta dalilin wani Ƙari da aka yi a cikin sallah da mantuwa. Misali mai sallah ya mance ya Ƙara raka'a ɗaya ko biyu ko uku a sallar Azahur ko La'asar ko Isha'i, ko ya mance ya Ƙara raka'a biyu a sallar Magriba, ko ya mance ya Ƙara raka'a ɗaya a sallar Asubahi, to duk wanda ya sami kansa a ɗaya daga cikin irin wannan hali, zai yi sujjada biyu ne bayan ya yi sallama, wato sujjada ba'adiyya kenan.

    Amma malaman FiƘhu sun ce: Duk wanda ya Ƙara yawan adadin raka'o'in sallah, to sallarsa ta ɓaci. Misali mai sallar Asubahi ya mance ya Ƙara raka'a biyu suka zama raka'o'i huɗu, ko kuma mai sallar Azuhur ko La'asar ko Isha'i ya mance ya yi raka'a takwas, ko mai sallar Magriba ya mance ya yi raka'a shida, to duka waɗannan sallarsu ta ɓaci kamar yadda Malam Abdurrahman mai littafin Ahdhari ya ambata.

    Har-ila-yau, wanda ya mance ya Ƙara sujjada ta uku a wata raka'a daga cikin raka'o'in sallarsa, ko ya mance ya yi ruku'u sau biyu a cikin wata raka'a daga cikin raka'o'in sallarsa, ko ya mance ya yi zaman tahiya a raka'a ta farko a cikin sallarsa, ko ya mance ya Ƙara yin zaman tahiya a raka'a ta uku a sallah mai raka'a huɗu, to duka hukuncin wannan shi ne yin sujjada bayan sallama, wato sujjada ba'adiyya. Wannan dai a taƘaice kenan.

    WATA FA'IDA: Malaman FiƘhu sun ce: Duk wanda ya yi ragi ya kuma yi Ƙari a cikin sallarsa zai yi sujjada kafin sallama ne, wato sujjada Ƙabliyya, saboda ana rinjayar da ɓangaren ragi ne a kan ɓangaren Ƙari. Misali mutum yana sallah, sai ya mance ya Ƙara sujjada ɗaya a ɗaya daga cikin raka'o'in sallarsa a maimakon biyu sai suka zama uku, sannan da ya matsa gaba sai ya mance da faɗin 'sami'allahu liman hamidahu' da kuma wata kabbara guda ɗaya, to a nan hukuncinsa zai yi sujjada ne kafin sallama, domin ɓangaren ragi yana rinjayar ɓangaren Ƙari ne.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.