Budurcin 'Ya Mace

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum warahmatullah Malam barka da safiya. Dan Allah Ina da tambaya malam yarinyace akayi mata fyaɗe tun tana shekarun kuruciya  kamar shekara 8 malam to wannan hymen ɗin da ake magana ita lokacin tana dashine tun farkon halittarta kokuma sai bayan yarinya ta girma ake halittarsa a jikinta ko Kuma dama tun haihuwa. To malam ita wannan yarinyar za'ace bata da budurci ne idan anyi aurenta kokuma tana dashi? Malam sai kaban shawarar yaya zanyi Dan Allah. Wassalamu alaikum.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Walaikumussalamu Hymen ɗin ko ince tantanin budurcin bawai sai ta girma yake samuwa ba a'a tun asali daman tana dashi, Sannan dangane da Budurcin kansa Shi budurcin mace fahimtarsa ta kasu kashi kashi yadda wasu suka fahimci budurci ba haka wasu suka fahimta ba misali Wasu na da fahimtar duk matar da Al'aurar namiji bata taɓa shiga al'aurata ba to tana nan a matsayinta na budurwa, wasu kuma su a wajensu koda ɗan yatsa ne ya shigeta to ta tashi daga budurwa, Wasu kuma su dazarar mace ta wuce wasu shekaru koda bata taɓa aure ba to su a wajensu ta tashi daga budurwa Akwai kuma masu ganin cewa duk cikakkiyar budurwa sai ta zubar da jini a ranar da aka fara jima'i da ita kuma wannan fahimtar tafi shahara a cikin mutana domin bama 'kabilar hausa ba Hatta Larabawa dausauran 'kabilu daban-daban duk suna da wannan fahimtar, Sabida wannan dalilin zanyi ɗan 'karin haske Akan wasu hanyoyi da akan iya rasa budurci bawai sai ta hanyar jima'i ko fyaɗe kaɗai ba, Sannan Ba duk mata ke da wannan hymen ɗin ba, Hakanan kuma ita fatar haymen ɗin tasha banban daga wata matar zuwa wata misali kamar kaurin fata wata tana da kaurin fata wata kuma bata da kaurin fata To itama hymen haka take idan mace hymen ɗinta mai kauri ce to abune mai wuya ta iya buɗewa da wuri Amma idan mara kauri ce to wasu ďabi'u na iya sawa ta buɗe ta yadda budurcin zai iya tafiya ba tare da an mata fyaɗe ko tayi zina ba, kamar yadda manazarta har da maluman musulunci suka faɗa, daga cikin HANYOYIN RASA BUDURCI akwai

1. SANANIN FITAR AL'ADA: ma'ana fitar jinin al'ada me nauyi me yawa yana iya tafiyar da budurcin mace, Amma ba duk me zubar jini mai yawan gaske ke iya rasa budurcinba Abin nufi dai ana lissafa hakan a cikin hanyoyin rasa budurcin.

2. TSALLE TSALLE: mace tana iya rasa budurcinta idan tana da 'dabi'a ta tsalle tsalle musamman lokacin 'kuruciyarta ko a lokacin da take budurwa to budurcin yana iya tafiya a dalilin tsalle tsallen ko guje guje.

3. TU'KIN KEKE: budurci yana iya tafiya ta hanyar tu'kin keke ga 'ya mace.

 

4. ƊAUKAN KAYA ME NAUYI: budurci yana iya tafiya ta hanyar ɗaukan kaya ko wani abu mai nauyi ga 'ya mace.

  

5. HAWA DOKI: budurci yana iya tafiya ta hanyar hawa doki ga 'ya mace.

 

6. ISTIMNA'I (BIYAWA KAI BU'KUTA BATA HANYAR AURE BA): budurci yana iya tafiya ta hanyar istimna'i ga 'ya mace.

 

7. CIWON SANYI INFECTION: budurci yana iya tafiya ta hanyar ciwon sanyi na infection  ga 'ya mace. dadai sauran wasu hanyoyin.

Wasu matan ma gaba ɗaya Allah maɗaukakin sarki baya halittarsu da budurcin.

Da wannan nake bata shawara kawai taji tsoron Allah ta tsarkake niyyarta kuma ta nemi taimakon Allah akan Allah ya rufa mata asiri sannan ta dage da addu'ar Allah ya bata miji nagari domin idan ta fifita lahirarta akan duniyarta Sai Allah ya zaɓa mata maji wanda zai fifita tarbiyyarta da kamun kanta sama da rashin ganin budurcinta bayan sunyi auren, Amma idan  baki da kamun kai da tarbiyya kuma baki da addini to idan akayi rashin sa'a kika rasa budurcinki ba ta hanyar banza ba to sai mijin ya zargeki da rasa budurcinki ta hanyar da bata dace ba a sakamakon munanan 'dabi'un da kike dasu.

Akarshe iyaye kuma musamman mata waɗanda 'kaddara tasa akayiwa 'ya'yansu fyaɗe suyi 'kokari su bawa yaransu tarbiyya ta islama sai Allah ya rufawa yaran naku asiri koda mijin ya fahimci cewa sun rasa budurcinsu tun kafin aure to bazai munana musu zato ba ma'ana bazai kawo cewa ta rasa budurcin ta hanyar neman maza ba, Amma idan yaranku basu da kamun kai baku basu tarbiyya ta islama ba sunita kawai suka sanya a gababa to tabbas zasu iya haɗuwa da 'kalu bale koda kuwa basu kasance masu bin mazan banza ba tun kafin ayi musu aure.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments