Cizon Cinnaka Magani Ne Ba Cuta Ba

    TAMBAYA (143)

    Wai naji ance ba kyau mutum ya kashe cinnaka, kenan ko cizo nawa zai dalla min saidai na kalle shi yayi tafiyarsa ?

    ✍️ AMSA A TAQAICE

    Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya hana a kashe dabbobi kala 4: qwari, zuma, hudhud (tsuntsu) da Suradi (shaho)"

    (Musnad Imam Ahmad: 3066, Abu Dawud 5267 Shaikh Shu'aib al-Arna'ut malamin hadisi ya sahihantashi)

    A likitance kuma an gano cewar yana maganin cutar obesity wato cutar matsananciyar qiba da dai sauransu

    Alhamdulillah

    A yanda cizon macen cinnaka yake sa wasu kuka su kuma wasu kidimewa suke suyi ta sosa wajen. To ammanfa abin al'ajabin shine: wannan cizon da take magani yake sakawa mutum bawai cuta ba, kamar dai yanda likita zai tsikara maka allura mai dauke da Chloroquine don magance cutar Malaria to haka shima sinadarin da macen cinnaka take zuba maka wanda ake kiransa da "ionic saliva" yake aiki a matsayin sedative a cikin jikin Dan Adam

    Yayin da sahabbai (Radiyallahu anhum) suka zamo sami'ina wa'ada'ana ma'ana sun ji hanin kuma sunyi biyayya bazasu kashe wadannan halittu ba - bari mu ji abinda Annabin Rahama (Sallallahu alaihi wasallam) ya hango wanda sai kwanannan likitoci suka gano

    1) Cizon macen cinnaka yana maganin qiba wadda ake samu silar taruwar fats wato kitse. Yayin da ta cije ka tana saka maka sinadarin ionic saliva ne shi kuma wannan sinadarin yana kashe halittun da suke a cikin fats ne wadanda suke zama silar da mutum yake yin qiba

    Misali: idan ta cije ka a hannu to nan take sinadarin zai qona halittun da suke a cikin fats na wannan hannun 99%, hakama idan a kafa ne ko a wani sashe na jiki. Kuma ko kasan cewar ba hakanan take cizon mutum ba - saboda nasha dora cinnaka a hannuna bazaka ji cizon ba har sai ka yi yunqurin kashe sa, shi kuma domin neman tsira sai ya maida martani wato cizo. Allahu Akbar

    2) Cizon cinnaka yana qarawa mutum adadin yawan red blood cells wato jajayen qananan halittun da suke a cikin jini wanda hakan ke qarawa mutum energy wato kuzari - misali: idan aka ce tashi ka rakani kanti zaka iya cewa gaskiya na gaji amman yayin da cinnaka ya manna maka bazaka san lokacin da zaka miqe zumbur ba. Meyasa ? Saboda ka samu energy silar halittar red blood cells da al-Khaliqu Allah Azzawajallah yayi a lokacin. Subhanallah

    3) Cizon cinnaka yana maganin cutar fata da ake da "cirrhosis of the skin"

    4) Haka Kuma yana kunna sinadaran neurons da suke a qwaqwala daga sensory signals inda cizon ya afku zuwa sensory cells dake qasan qwaqwala. Subhanallah

    Dogaro da wadannan hujjojin da na zayyano a addinance da kuma a kimiyyance kuskure ne kashe cinnaka. Amman dangane da qwari irinsu kunama wannan ba laifi bane don an kashe ta saboda dafinta yana iya kisa. Haka kuma baa son a kashe tururuwa saboda ita musamman ma aka saukar da Sura mai sunanta: Suratu Nahl inda Allah Azzawajallah yace

    ( حَتَّىٰ إِذَا أَتَوْا عَلَىٰ وَادِ النَّمْلِ قَالَتْ نَمْلَةٌ يَا أَيُّهَا النَّمْلُ ادْخُلُوا مَسَاكِنَكُمْ لَا يَحْطِمَنَّكُمْ سُلَيْمَانُ وَجُنُودُهُ وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ )

    النمل (18) An-Naml

    Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, "Yã kũ jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba."

    Haka kuma tsuntsun huda - huda da yazo a hadisin, shima Allah ya ambace a Qur'ani

    ( وَتَفَقَّدَ الطَّيْرَ فَقَالَ مَا لِيَ لَا أَرَى الْهُدْهُدَ أَمْ كَانَ مِنَ الْغَائِبِينَ )

    النمل (20) An-Naml

    Kuma ya binciki tsuntsãye, sai ya ce: "Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne?"

    Da kuma zuma wadda itama Surah ce guda da aka anbace ta da: Suratu Nahl;

    ( وَأَوْحَىٰ رَبُّكَ إِلَى النَّحْلِ أَنِ اتَّخِذِي مِنَ الْجِبَالِ بُيُوتًا وَمِنَ الشَّجَرِ وَمِمَّا يَعْرِشُونَ )

    النحل (68) An-Nahl

    Ubangijinka Yã yi wahayi zuwa ga ƙudan zuma cwa: "Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa."

    Do haka sai mu kiyaye yunqurin kashe wadannan halittun indai ba da wani dalili qwaqqwara na shari'a ba

    Kuma idan mutum yayi haquri da cizon cinnakan to zai samu riba biyu

    Na farko zaka samu waraka daga cutar obesity wato qiba idan kana da ita

    Na biyu kuma idan kayi haquri to zaka samu lada da kankarar zunubi kamar yanda hadisi ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari cewar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: ina mamakin al'amarin mumini, idan sharri ya same shi sai ya gode Allah haka idan alkhairi ya riske shi

    Wallahu taala aalam

     Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.