Fitar Banaga Dan Bature Dan Danau Daga Anka Zuwa Sabon Wurin Da Ya Kafa, Watau Sabon Birnin Banaga

    Fitar Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau Daga Anka Zuwa Sabon Wurin Da Ya Kafa, Watau " Sabon Birnin Banaga 

    Akwai magana /maganganu guda biyu game da wannan fitar ta Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau daga Anka da suka fi shahara a Tarihin samar da Anka a matsayin hedikwatar ƙarshe ta Zamfarawan da suka zauni Dutci/Dutsi da Birnin Zamfara da Kiyawa da Banga da Ƙuryam Madaro da Sabongarin Damri tsakanin 1300 zuwa 1815/1824.

    Ta farko ita ce wacce/wadda Dr. Kurt Krieger ya tafi akai cewa Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo (1815-1824) ne ya yi wa Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau sammu da aka haɗa a kab'akin Tuwo aka ɗauka daga Sabongarin Damri zuwa Anka. Har Bawan Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo wanda ya ɗauki sammun zuwa Anka ya ambata a cikin aikinsa "Tarihin Zamfara" (wanda akasari daga rubutun magabata ne da suka mulki Daular Zamfara da aka rubuta a cikin Ajami da ya karɓe daga Fadar Sarkin Zamfaran Anka a cikin 1940s/50s) ya tafi dashi Ƙasar su, Jamus. A shekarar 1959 kuma ya wallafa wannan Littafi nasa mai suna "Tarihin Zamfara" wanda kusan shi ne madogara ta biyu akan Tarihin Daular Zamfara bancin Infak'ul Maisur na Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.

    A ciki ya bayyana cewa bayan wannan Bawa ya girke wannan kab'akin tuwo a Ƙofar gidan Banaga Ɗan Bature a Anka( a gidan ne Sarakunan Zamfara tun daga Sarki Ɗan Baƙo, 1815-1824 ya zuwa yau suke sarauta) da ya fito Sallar Asuba ya yi kicib'is da shi sai sammun ya shige shi.

    Da hantsi ya tara hakimansa da manyan mutanen garin ya sanar dasu cewa zasu tashi daga Anka ba tare da ɓata lokaci ba, ya yanke shawara umurni ne ya ke basu. Saboda haka a ranar suka kimtsa kayansu, su ka fice daga garin, suka tsallaka Kogin Zamfara dake Kudu da Anka ya sake kafa sabon zama da ya kira "Sabon Birnin Banaga" inda na ambata a cikin rubutun da ya gabata cewa anan ne Allah ya yi masa wafati. Na je garin a cikin farko farkon shekarar 2011.

    Magana ta biyu kuma akwai bayanin da ke nuna cewa umurnin Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne Sarakunan Zamfara na wancan lokaci da ke zaune a Sabongarin Damri su ka bi wajen fitar da shi daga Anka da zummar su zauni wurin a matsayin sabuwar hedikwatarsu duk da yake ba a bayyana ko ta wace hanya suka bi ba wajen aiwatar da wannan umurni ba, ban kuma ci karo da wannan bayani a rubuce ba. Allahu Wa'alam!!!

    Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya

    Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya
    08149388452, 08027484815.
    birninbagaji4040@gmail.com
    Asabar, 29/06/2024

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.