Hadisin Da Aka Fara Rawaitowa

TAMBAYA (146)

Wanne Hadisi ne farkon rawaito wa ?

AMSA

An rawaito hadisi na farko ne a lokacinda Annabi SAW yayi HIJIRA daga MAKKA zuwa MADINA, bayan taguwarsa ta saukeshi a gidan ABU AYUBAL ANSARI RTA, ya sauka a BANI UNAIF, kudu maso yamma daga inda QUBA take, anan yafara kwana

KULSUMU ibn HIDMI RTA shine wanda ya bashi dakin dazai kwana, sai SAADU ibn HAISAMA RTA shikuma sai yace ya RASULULLAH naga baki sunata zuwa wajenka amman babu gurinda zaka karbesu amman ga filina inda muke shanya dabino zamuzo musakamaka ZANA saika dinga karbar bakinka a wajen, a lokacinne akazo ana maraba da saukarsa

Ananne wasu daga cikin mutanen garin sukace bari suje tsegumi da ganin kwakwaf, irinsu Abdullahi Ibn Salami, yana kallon fuskar ANNABI SAW yace kai wannan ba sauran qarin bayani ba maqaryaci baneba, bayan anyi tsit sai Manzon Allah SAW yace, AYYUHANNASU, AKSHUS SALAMA, WA'A INA DA'AMA, WASULUL ARHAMA, WASALLU BILLAYYA WANNASU MIYAMU TADKULU JANNATA BISALAMI

Ma'ana; Yaku mutane ku yada aminci (sallama), duk inda zakuje, ba tsugudidi, ba munafurci, ba algungumanci, ba annamimanci, hadin fada, ba yi da mutane, duk abinda zaisa qauna shi zakuyi

Sannan ku ciyarda mutane, kuyita abinci, ku sada zumunci, sannan kuyi sallah cikin dare zaku samu ALJANNAH ba wahala

Sunan al-Tirmidhī 2485

To amman yanzun anzo wani zamani wanda ba'a damu da yada sallamaba, ga munafunci yayi qatutu a zuciyoyinmu, sannan masu hali basa ciyarwa kowa sai rowa, gashi ba'a zumunci saikanada abin hannu, sannan sallarma anfi fifita neman duniya akanta, to ahakan zamu shiga ALJANNAH ?

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu an la ilaha illa anta astaghfiruka wa'a'tubu ilayka

Amsawa

Usman Danliti Mato, (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments