Wannan wata karin magana ce da ta samu a Tsohuwar Daular Zamfara a lokacin mulkin Sarkinta na 30, watau Sarki Yakuba ɗan Sarkin Zamfara na 29 Babba ɗan Sarki Muhammadu na Makake.
Sarki Yakuba ɗan
Babba wanda ya yi mulki a cikin 1720s jarumin gaske ne da ya yi yaƙe- yaƙe ya
kuma samu gagarumar nasara. A lokacinsa ne karen Daular Zamfara ya kai tsaiko.
Sarki ne mai kwarjini ga jama'arsa domin jarunta da kyautatawarsa zuwa gare su.
Wata rana wani Ba'azbine ya taso daga Ƙasarsu,
Azbin da Doki zuwa Birnin Zamfara domin ya kawo wa Sarkin Zamfara Yakuba ɗan Babba ya siya. Bisa ga ƙaddara
sai doki ya mutu kafin Ba'azbinen ya iso Birnin Zamfara.
Ba'azbine ya ciro ragamar dokin ya ci gaba da tafiya har sai
da ya iso Birnin Zamfara. Aka yi masa iso a wajen Sarki, ya faɗi ya yi gaisuwa ya kuma
sanar da Sarki labarinsa. Sarki Yakuba ɗan
Babba ya tambaye sa "ina ragamar dokin? Ba'azbine ya ce ga ta a hanunsa.
Sarki Yakuba ya umurci Sarkin Zaginsa da ya karɓi ragamar ya shiga a Bargar
Dawakinsa ya dinga gwada ta akan dawakin, duk dokin da ta yi wa daidai ya zo ya
sanar dashi.
Bayan wani lokaci Sarkin Zagi ya fito daga Barga ya gayawa
Sarki cewa an samu dokin da ragamar ta yi wa daidai. Sarki ya tambaye sa nawa
ne aka siyo wannan dokin? Sarkin Zagi ya ce bawa ashirin da biyar aka siyo shi.
Sarki ya ce akai Ba'azbine masauki har zuwa gobe.
Kashegari Sarki ya sa aka zo da Ba'azbine da ragamar dokinsa
a gabansa. Ya ce a bashi bawa ashirin da biyar ya yi niyya ya koma Ƙasarsu
ya na mai cewa "Ai hasarar doki sai Sarki". Daga wannan lamarin ne
aka samu karin magana a Daular da ake cewa "Hasarar Doki sai Sarki".
Allah ya jiƙan
magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, ya yalwata
bayanmu, amin.
Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara,
Nijeriya.
08149388452, 08027484815
birninbagaji4040@gmail.com
Alhamis, 11/07/2024
Ƙarfe 11:52 na dare.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.