Hudubar Jariri Da Radin Suna

    TAMBAYA (133)

    Assalamu Alaikum, Allah ya gafarta Malam , Ina Da Tambaya Dan , ya Ake hudubar jariri Idan an haifi Shi Da Radin Suna ??? Nagode sea Naji Daga gare ku 🙏🙏

    ✍️AMSA A TAQAICE

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhu

    (Ibn al-Mundhir ya fada a cikin littafinsa Al-Awsat cewar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya umarci mutane su dinga saka suna a rana ta bakwai da haihuwa, wanda karshen riwayar hadisin ta kare daga Abdullahi Ibn Amr (Radiyallahu anhu)

    (Al-Ishraf ala Madhahib al-Ulama #3/421)

    Sannan kuma hudubar da akewa jarirai ba sunnar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) bace ba. Imam al-Bayhaqi yace ruwayoyin wadannan hadisan duk basu inganta ba duk da'efai ne

    (Shu'ab al-Iman #8620)

    Bismillaahir Rahmaanir Raheem

    Dangane da huduba a kunnen jariri da akwai mabanbanta riwayoyi akan hakan

    Na farko

    An karbo daga Abu Abdullah Al-hakim, daga Abu Ja'far Muhammad Ibn Duhaym, daga Muhammad Ibn Hazim Ibn Abu Gharzah, daga Ubaidullah Ibn Musa, daga Sufyan Ibn Sa'id Al-Thawri, daga Asim Ibn Ubaidullah Ibn Rafi' daga mahaifinsu (Allah ya kara yarda a garesu baki daya) ya ce: Naga Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yana kiran sallah (adhan) a kunnen Hasan Ibn Ali, a lokacin da Fatima (Radiyallahu anha) ta haife shi

    (Abu Dawud #5150 da Tirmidhi #1514 ne suka rawaito, sunce hadisi ne Sahih. Imam Ahmad yace da'ef ne a cikin Musnad dinsa 6/9, 362, 391)

    Na biyu

    Imam al-Bayhaqi ya rawaito Hadisi a cikin littafinsa 'Al-Shu'ab', an karbo daga Al-Husain Ibn Ali (Radiyallahu anhu) ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Duk wanda aka yi masa haihuwa sai ya kira sallah (adhan) a kunnensa na dama ya yi iqamah a kunnensa na hagu, za'a nesanta dan daga qarin (aljaninsa)"

    (Abu Ya'ala a cikin Musnad dinsa #6780, Ibn Adi' a cikin Kamil dinsa #7/2656, Bayhaqi a cikin Shu'ab al-Iman #8619. Saidai wannan ba tauqifi bane ma'ana ba daga bakin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) aka ji hakan ba)

    Na uku

    An karbo daga Abu Sa'id, daga Ibn Abbas (Radiyallahu anhuma) cewar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yayi kiran sallah (adhan) a kunne Hasan Ibn Ali na dama da kuma iqamah a kunnensa na hagu

    Bayhaqi yace ruwayoyin wadannan hadisan duk basu inganta ba duk da'efai ne

    (Shu'ab al-Iman #8620)

    Dalilin da yasa ake kiran sallar (Allah ne mafi sani) shine saboda ana son yaron ya fara jin sunan Allah da kuma musulunci da zarar ya shigo duniya kamar dai yanda ake son ya firta kalmar shahada da zarar mutuwa ta riske shi lokacin da zai bar wannan duniyar

    Dangane da radin suna kuma koyi da sunnah shine a radawa jariri suna a rana ta bakwai kamar yanda Muhammad Ibn Ali yaji daga Salih daga mahaifinsa har ma ya kawo hujja daga hadisin Samura

    Haka kuma saka suna haqqin mahaifi ne ba na mahaifiya ba domin kuwa da sunan mahaifi za'a kira mutum a ranar lahira. Za'a kira shi da wane-dan-wane, kamar yanda Allah (Subhanahu wata'ala) ya fada

    ( ادْعُوهُمْ لِآبَائِهِمْ هُوَ أَقْسَطُ عِندَ اللَّهِ ۚ

    الأحزاب (5) Al-Ahzaab

    "Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah"

    To kaga wannan ayar qalubale ce ga wadanda suke jingina sunansu da iyayen da ba nasu ba. Sannan kuma bayan saka suna (ism) akwai laqabi (laqab) da kuma sunan alkunya (kunyah). To ammanfa duk yanda za'ayi kada ku bari a dinga fada masa sunan banza (alqab) domin Allah (Subhanahu wata'ala) ya hana hakan

     وَلَا تَنَابَزُوا بِالْأَلْقَابِ ۖ

    الحجرات (11) Al-Hujuraat

    "...kuma kada ku jfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ..."

    Sannan kuma sunan da Allah ya fi so shine: Abdullah da Abdurrahman kamar yanda Ibn Umar (Radiyallahu anhu) ya rawaito daga Annabi (Sallallahu alaihi wasallam)

    (Sahih Muslim #3/1682)

    Abu Wahb Al-Jushami ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Ku kira kanku da sunayen Annabawa. Sunan da Allah ya fi so shine: Abdullah da Abdurrahman. Suna mafi gasgatawa shine Harith da Hammam, sunan da aka fi qyama shine Harb da Murrah"

    (Sahihul Bukhari #813 da Abu Dawud #13/350. Duba littafin: "Tuhfatu'l Maudud bi ahkam al-Maulud" na al-Hafiz Ibn al-Qayyim Aljawziyya - Rahimahullah)

    Ina fatan Allah ya albarkaci jaririn da aka samu, Allah ya tabbatar dashi akan addinin musulunci da bin Sunnar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam), Allah ya rabashi da Bidi'ah da kafirci

    Wallahu ta'ala a'alam

     Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.