Hukunce Biyan Bashin Sallar Qasru A Yayin Da Aka Dawo Gida

    TAMBAYA

    Dan Allah tambaya nake akan sallar kasaru

    Yar garin kano ce ni

    Tambayar shine yanxu idan naje garinda kasaru tah kamani kamar dustan jigawa sai laasar tah riskeni a garin amma banyi bah sai bayan nah dawo Kano

    Toh xanyi raka biu ne koh hudin xanyi

    AMSA

    BISMILLAH WASSALATU WASSALAMU ALA RASULlLLAH

    An yiwa samahatush sheikh bn baz (rimahullah) irin wannan tambayar A cikin [fataawa nurun alad darbi]

    Sai ya bada amsa da cewa shi matafiyi idan ya  riski ahlin sa (wato yayin da ya koma gidan sa) zai biya abin da yake kansa na sallar da biyiba a halin tafiya to zai yita ne cikakkiya (wato raka,a hudu) ba zaiyi qasru ba, ka dai dai zaiyi qasru ne a halin kasancewar sa a cikin tafiya, to amma idan ya jirkinta sallar la,asar ko azahar ko sallar isha,i har sanda ya koma gida to haqiqa shi zai sallace ta raka,a hudu ne, domin tafiyar ta gushe kuma saukin ma ya gushe.

    Allah shi ne mafi sani

    Amsawa (abu abdullah)

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    [8:46 pm, 24/07/2024] +234 703 538 7476: SANARWA

    Assalamu alaikum, warahmatullahi, wabarakatuhu

    Biyo bayan amsar da na fitar kwanaki 10 da suka gabata gameda bincikawa wata baiwar Allah Rajalis Salih wato Miji Nagari, an samu yan uwa da dama daga cikin wannan group mai albarka da suka turo buqatu makamanta wannan Kuma ana sa ran za'a dace domin kuwa an tsara program dinne bisa tsari mai kyau

    Alhamdulillah, sakamakon hakan, akan gaba, an samu dan uwa shugaban "DBK MARRIAGE & ORPHANS FOUNDATION", wanda aikinsu shine qulla alaqar aure don raya sunnah tsakanin maza da mata wadanda suka fahimci juna, tun tsawon sama da shekaru 3 ba su da wani aiki sama da wannan

    A tsawon shekarun nan an samu nasarar aurar da yan mata da Zaurawa sama da goma sha [Wadanda muka Sani kenan]. A hakan ma Allah ne kadai yasan wadanda suka daidaita har Kuma suka yi auren. Alhamdulillah. Wannan Nasara ce babba haka Kuma dama ce ga duk wanda yake neman abokin zaman aure.

    Allah Subhanahu wata'ala yace

    ( الْخَبِيثَاتُ لِلْخَبِيثِينَ وَالْخَبِيثُونَ لِلْخَبِيثَاتِ ۖ وَالطَّيِّبَاتُ لِلطَّيِّبِينَ وَالطَّيِّبُونَ لِلطَّيِّبَاتِ ۚ

    النور (26) An-Noor

    Miyãgun mãtã dõmin miyagun maza suke, kuma miyãgun maza dõmin miyãgun mãtã suke kuma tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin tsarkãkan mãtã suke.

    Bayan tattaro bayanai da Kuma jin tsare tsaren na ga dacewar a bude kofar SANARWA ga duk wanda yake buqatar neman abokin zama, Wanda kuma ana sa ran ya zamo nagari laakari da kusan duk Wanda ka gan shi a wannan group to dalilin gyara addinin sa ne ya shigo domin kuwa wasu basu damu da neman ilimi ba ballantana Kuma aiki dashi. Kwanakin baya wata mata tacemin Allah ya biyamu da Aljannah domin kuwa suna daga gidajensu amman suna amfanar ilimin da ko masu zuwa Makaranta sai Haka

    A karshe duk Wanda yake da raayin shiga sannan kuma ya shirya aure [ba soyayya ba] bisa wannan tsarin zai cike wadannan bayanai kamar Haka

    Send your details using this format

    1.First Name

    2.Gender

    3.Tribe

    4.Location

    5.State of Origin

    6.Age

    7.Blood Group

    8.Genotype

    9.Health status:

    10.Marital status:

    11. No. of kids

    12.Height:

    13. Body size

    14.Complexion:

    15.Educational Status

    16.Occupation:

    17.Religious ideology- Muslim

    /Aƙida

    18.Interested in

    19. Pictures

    Sannan kuma inda baa gane ba sai ayi tambaya

    Muna roqon Allah ya duba manufarmu ya shiga al'amarin. Sannan Nima a matsayina na wanda lokacin sa bai zo ba, a tayani da adduar samun mace tagari: MAR'ATUS SALIHA wadda zamu Sha ZANJABEEL daga tafkin SALSABEEL da yake a cikin ALJANNAH

    ( وَيُسْقَوْنَ فِيهَا كَأْسًا كَانَ مِزَاجُهَا زَنجَبِيلًا )

    الإنسان (17) Al-Insaan

    Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne.

    ( عَيْنًا فِيهَا تُسَمَّىٰ سَلْسَبِيلًا )

    الإنسان (18) Al-Insaan

    Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil.

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu an la ilaha illa anta astaghfiruka wa'a'tubu ilayka

    Sanarwa

    Usman Danliti Mato, (Usmannoor_As-salafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.