Hukunce-Hukuncen Jaririn Da A Kahaifa Da Ga Alqur’ani Da Sunnah Da Kuma Magabata Na Kwarai

    TAMBAYA

    Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuhu

    Barka da safiya Malam Allah ya qara rufa asiri ya biya mana buqatunmu na Alkhairi ya Saka maku da alkhairi bakidaya🙏🏻

    Tambayata itace Dan Allah yaakeyiwa yaron da aka Haifa huduba da Saka suna da duk wata sunnah da ta kamata ayi lokacin da aka samu qaruwa ta haihuwa?

    AMSA

    Wa'alaikumus salamu waramatullah wabarakatuh

    Salati da aminci maras adadi sukara tabbata sugaban abin abin kaunar mu annabin rahma (S. A. W).

    KEBANTATTUN SUNNONIN DA SHARI,AR MUSULINCI TA TANADA DA AKEYIWA JARIRI A YAYIN DA AKA HAIFE SHI.

    kamar yadda suka zu daga manzun allah (S.A.W)

    1- naima masa tsarin allah

    2- yin godiya ga allah bayan an haife shi(ba tare da la,akari da namiji ne ko mace ce ba)

    3-yi masa tahniik(fara ciyar da shi dabino) da kuma naima masa albarka

    4- sanya masa suna

    5- Yanka masa haqiqah

    6- Aske masa gashin kansa

    7- Yi masa kaciya

    Bayanan su daki-daki:-

    1- naimawa jariri tsarin allah daga shaidan kamar yarda mahaifiyar nana maryam (A.S) (wato matar imrana)ta ce-: a yayin da ta haife ta

    عليهما السلام -: ﴿ رَبِّ إِنِّي وَضَعْتُهَا أُنْثَى وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا وَضَعَتْ وَلَيْسَ الذَّكَرُ كَالْأُنْثَى وَإِنِّي سَمَّيْتُهَا مَرْيَمَ وَإِنِّي أُعِيذُهَا بِكَ وَذُرِّيَّتَهَا مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ ﴾ [آل عمران: 36].

    To a yayin da ta haife ta sai ta ce:, ya ubangijina lalle ni na haife ta ya' mace, kuma allah shine mafi sanin abin da ta haifa, kuma da na miji ba daidai ya ke da ya' mace ba, kuma haqiqa ni na rada mata suna maryam, kuma haqiqa ni ina nema mata tsarinka da zurriyar ta daga shaidan korarre(suratu al,imran 36)

    Ya kamata da zaran anhaifi jariri to yana da kyau mahaifiyar sa ta nema masa tsarin allah daga babban maqiyin sa wato iblis domin addu,ar uwa ga ya'yan ta karbabbiya ce in sha allah.

    2- yin godiya ga allah yayin da aka haife shi lafiya(ba tare da la,akari da namiji ne ko mace ce ba)

    Daga kasiir dan ubaida (R.D) ya ce : "nana a,isha (allah ya kara yarda agare ta) ta kasance idan akayi haihuwa acikin su- wato a ahalin ta - bata tambayar namiji ne ko mace ce, tana cewa ne an haife shi lafiya? Idan akace ee an haife shi lfy, sai ta ce:dukkan godiya ta tabbata ga allah ubangijin halittu" [imam albani - allah yai masa rahama- ya hassana shi acikin sahihi adabul muprad a shafi na 534 ].

    3- yi masa tahniik da kuma yima sa addu,ar samun albarka

    Daga nan aisha (R. d) tace: "annabin (S. A.w) ya kasan ce ana zuwam masa da yaran da aka Haifa, yana musu addu,a ta samun albarka daga wajan allah da kuma yi musu tahniik" [muslim ne ya rawaitu shi].

     Menene tahniik?

    Attahniil shi ne sakawa jariri wani abu na dabino a bakin sa bayan an tattauna dabinun sai ya kasan ce taunannan da binun shine farkon abin da zai fara shiga hanjin sa bayan an haife shi.

    1- wanene zai yiwa jariri tahniik?

    An tambayi samahatush shaikh dan baz - allah yai masa rahma:- game da daukar jarirai a kai su wajan malamai domin su yi musu tahniik; sai ya hana hakan, kuma ya ce: " mahaifin sa ko mahaifiyar sa suyi masa tahniikin, sannan ya ce: da za,a bude kofar tahniik, ti da mutane sun zurfafa a cikin sa." (ma, ana sunhuce gona da iri) [risalatu masaa,ili abii umarus sadhaani lil,imaami binu baz shafi na 43].

    (domin a dauki jariri a kai shi wajan wani domin yayi masa tahnik ya kebanci annabi (s.a.w.) Ne Shi ka dai bisa mafi ingancin maganar malamai)

    An rawaitu daga al,imam ahmad: "haqiqa shi an haifa masa yaro, sai ya cewa mahaifiyar yaron ki yimasa tahniik"; [tuhfatul mauduud bi ahkamil mauluud safi na 66]

    **Lokacin tahniik shi ne lokacin da aka haife shi

    Shaikh dan uthaimin - allah yaima sa rahma- ya ce:- " attahniik yana kasancewa lokacin da akayi haihuwa har ya kasance shi ne farkon abun da za a fara ciyar da jaririn da shi....."; [fatawaa nurun alaad darbi shafi na 14\2]

    **Tahniik yana kasancewa da dabinu

    Daga nana a,isha, (allah yakara yarda da ita)ta ce: "anzu da abdullahi dan zubair wajan manzan allah (s.a.w)- domin yayi masa tahniik, sai muka naimi dabinu, sai naiman sa yaimana huya"; [Muslim ne ya rawaitu shi.]

    **To Idan kuma ba a sami dabinu ba

    Ahmad dan anbal( rahimahullah) yace-: wani lokaci ya na lasawa yaron zuma" [almugnii 2\497]

    ** Idan ba a samu zuma ba, sai aimasa tahnik da dukkan wani abu mai zaqi

    ** Tambaya: shin ya halatta ayiwa jajiri tahniik da zuma ko suga?

    Amsa: "ya halatta, sai dai asali shine ayi tahnik da dabinu, to amma idan ba a sami dabinun ba sai aimasa tahnik da abin da ba shi ba daga abin da yake da zaqi";[ashshaikh abdul muhsin al,abbaad, ya fadi hakan acikin sharyin sunanu abii daahuud 1/158].

    **Daga cikin Fa,idar tahnik

    Daga cikin dabinu da annabiba (s.a.w)ya kasance yana yiwa jirirai: tahnik da shi, lalli acikin dabinu akwai alkhairi da albarka, kuma yana da amfani ga ma,ajiyar abinci (wato babban hanji) da ke ciki, to idan ya kasance shine farkon abin da ya fara shiga zuwa ma,ajiyar abinci, Hakan sai ya zama alkhairi ga ma, jiyar abincin"; [shaikh dan uthaimin acikin sharhin riyadus saliyiin, a babin hakuri 1\269].

    4- sanya masa suna

    **A- sanya masa suna haqqi ne na mahaifin sa

    Imam dan qayyum ( rimahullah) yace-: wannn na daga cikin abin da babu jayayya acikin sa a tsakanin mutane, kuma haqiqa idan iyaye suka yi jayayya wajan sanyawa yaro suna, to haqqin samasa suna na mahaifi ne, kuma hadisan da suka gabata dukkan su suna nuni akan haka"; [tuhfatul mauduud bi ahkaamil maluud shafi na 233].

    **B- sanya suna ga wanda ba mahaifi ba kuma ba mahaifiya ba ya halatta

    Daga baban musa yace: "yace an haifamin yaro,sai na kaiwa annabi (s. A.w) shi sai ya sanya masa suna ibrahim yaimasa tahnik da dabinu, kuma yaimasa addu,ar albarka, kuma ya miko min shi"; [bukhari ne ya rawaito shi].

    **C- yaushene ake sanya masa suna

    1- a ranar da aka haife shi

    Daga baban musa yace: "yace an haifamin yaro,sai na kaiwa annabi (s. A.w) shi sai ya sanya masa suna ibrahim yaimasa tahnik da dabinu"; [bukhari ne ya rawaito shi 5467].

    **2- a rana ta uku

    Khallaal ya ce acikin jami,i nasa-rahimahullah - :(a babin ambatun sanyawa yaro suna).

    Abdul malik dan abdul hamid ya bani labari ya ce: mun tattauna gami da a kwana nawa ne ake sawa yaro suna? Sai abu abdullahi- ahmad dan hambal ya ce mana-: amma abin da ya tabbata, an rawaito daga anas (allah ya qara yadda da shi) haqiqa shi yana sanyawa yaro suna a rana ta uku, amma shi kuma samura - allah ya qara yarda da shi - yana sawa yaro suna a rana ta bakwaic";[tuhfatul maudud fi ahkamil maulud shafi na 167].

    **3- a rana ta bakwai

    Daga samura (r. d) ya ce: annabi( s. A. W.) yace: ((yaro ana tare shi daga alkhairi idan ba a yimasa haqiqa ba, za,a yanka masa haqiqa a rana ta bakwai da haihuwar sa, kuma asa masa suna

    a rana ta bakwai, kuma a aske masa kansa)) [ imam ahmad ne ya rawaitu shi, kuma albani ya inganta shi acikin mushkaatil masaabiih].

    **D- sunaye mafiya daraja da ake so a sanya su kuma suka halatta

    An so asanya wadannan sunayan

    Daga anas (R. D) yace: annabi (s. A. W) ya ce- (( mafiya soyiwar sunaye awajan allah sune: abdullahi da abdurrahman da kuma haris)) [ albani ya inganta shi acikin sahihil jaami,i shafi na 162].

    Fadakarwa

    ** anso a sanya sunaye da suka fara da (abdu) da aka rabasu da kowane sunan daga cikin sunayen allah.

    **Kuma anso asanya sunayen annabawa da manzanni (amincin allah ya kara tabbata a gare su).

    ** kuma anso a sanya sunayan sahabbai (allah ya kara yarda da su) da kuma sunayan salihan bayi daga cikin musulmai.

    5= yankawa dan jariri haqiqa(abin yanka irin su rago ko akuya ko tunkiya)

    Ma,anar haqiqah: "ita ce mutum ya yankawa jaririn sa abin yanka:

    yanka abin yanka a rana ta bakwai, (alhaqiqah): ita ce abin yankan da ake yankawa ga jariri arana ta bakwai a yayin da ake aske gashin kansa" ; [alwajiz shafi 428].

    **HUKUNCEN TA: Shaiku dan uthaimin (rahimahullah) ya ce-: ita haqiqah sunnace mai qarfi ya dace ga wanda yake da ikon yinta to ya tsayar da ita (ya aikata haqiqar), kuma ita an shar,antata ga mahaifi ne kadai, ana yankata a rana ta bakwai daga haihuwar jaririn"; [majmu,ul fatawa wa rasa,ilul uthaimin 25\203].

    LOKACIN DA AKE YIN HAQIQAH: Sunnah shine a yanka abin yankan a rana ta bakwai daga haihuwa, idan ba asamu damar yankawa ba a rana ta bakwai sai a yanka a rana ta goma sha hudu idan ba a samu damaba sai a yanka a ra rana ta ashirin da daya;

    Daga buraida (r.d) daga annabi (S. A. W) ya ce: ((haqiqah ana yankata a rana ta bakwai da haihuwa ko kuma rana ta sha hudu, ko rana ta ashirin da daya)) [baihaqi ne ya rawaitu shi, kuma albani ya inganta shi acikin sahihul jami,i 4132].

    ** GWARGWADON ABIN DA ZA, A YANKA: ana yanka akoyoyi biyu ga yaro, yarinya kuma ana yanka mata akoya daya; sabo da abin da ya tabbata daga hadisin ummuna a,isha (r.d) ta ce: annabi (s.a.w) ya umarce mu muyankawa yaro akuya biyu, ita kuma yarinya akuya daya" [dan maja ne ya rawaitu shi, kuma albani ya inganta shi acikin sahihu bn majah 2561]

    ** HALACCIN YANKA NAMIJI KO MACAN DABBA A CIKIN HAQIQA

    saboda hadisin ummu kurzun (r.d) ta ba shi labari haqiqa ita taji mazan allah. - s.a.w- yana cewa -: ((ga yaro ayanka masa akuya biyu ga yarinya kuma a yanka mata akuya daya, ba zai cutar da ku ba idan abin yankan ya kasance namiji ne ko mace ce)) [ abu dahud ne ya rawaitu shi kuma albani ya inganta shi acikin sahihil jami,us sagir 4106]

    ** IDAN ZA, A YANKAWA YARO AKUYA BIYU TO SU KASANCE SA,ANNI (TSARAN JUNA)

    daga ummu kurzin. (R. D) ta ce: na ji mazan allah. (s.a.w) yana cewa: ga yaron da aka haifa ayanka masa akuyuyi biyu tsarannin juna, ita kuma mace a yanka mata akuya daya; [ baihaqi ne ya rawaitu shi, kuma imam alvani ya inganta shi a cikin al, irwaa,a 1166.]

    ** Shin ya halatta a yanka akuya daya ga da namiji?

    Shaikh bn uthaimin (allah yaimasa rahama) ya ce : idan mutum bai sami akuya biyu ba sai daya to ta, isar masa, kuma an samu da ake nufi da ita, sai dai idan allah ya kasance ya azurta shi, to biyun sune sukafi falala" [ ashsharhul mumta,a 7/492]

    ** cin bashi domin yin haqiqa

    Kuma an tambayi abu abdullah: akan mutumin da aka haifa masa da (yaro), kuma bashi da abin da zai yanka masa, shin yafi soyiwa agare ka ya ci bashi ya yi masa haqiqa, ko ya jinkir ta har sai allah ya hori masa? Sai ya ce: mafi tsananin abin da na ji gami da haqiqa abin da alhasanu, ya rawaitu daga samurah (r.d) daga annabi(s.a.w)-: ((ko wani ya a natare shi da ga alkhairi idan ba a yanka masa haqiqa ba)) kuma haqiqa ni ina fatan idan yaci bashin allah zai gaggauta bashi abin da zai biya bashin, domin ya raya wata sunnah da ga cikin sunnar annabi (s.a.w) kuma ya bi abin da ya zo daga gare shi; [ masa,ilu imam ahmad riwayatu ibnahu masaa,ilun fiil aqiqah juzu,i 2 shapi 208]

    ** abin da ake cewa ayayin yakan aqiqah

    عن عائشة - رضي الله عنها - أنها قالت: "عق رسول الله - صلى الله عليه وسلم - عن الحسن والحسين، وقال: ((قولوا: بسم الله، والله أكبر، اللهم لك وإليك، هذه عقيقة فلان))؛ [رواه البيهقي، وقال النووي: إسناد حسن، في المجموع (8/428)].

    Daga ummuna a,isha (r.d) haqiqa ta ce: annabi (s.a.w) ya yankawa hasan da Hussain aqiqah kuma ya ce: (Ku ce: da sunan allah kuma allah ne mafi girma ya allah daga gare ka kuma zuwa gare ka, wannan ita ce aqiqar wani)

    6- aske gashin kan yaro arana ta bakwai da kuma yin sadaka da azurfar da ta kai kwatan kwacin nauyin gashin kan sa (ko kuma sadaka da kudin da suka kai qimar nauyin azurpar)

    Daga samura (r. d) ya ce: annabi( s. A. W.) yace: ((yaro ana tare shi daga alkhairi idan ba a yimasa aqiqah ba, za,a yanka masa aqiqah a rana ta bakwai da haihuwar sa, kuma asa masa suna

    a rana ta bakwai, kuma a aske masa kansa)) [ imam ahmad ne ya rawaitu shi, kuma albani ya inganta shi acikin mushkaatil masaabiih].

    Daga baban rafi,i haqiqa annabi (s.a.w)ya ce wa fadima yayin da ta haifi alhussain: (( ki aske masa gashin kansa, kuma ki yi sadaka da azurfa da ta kai nauyin gashin kan sa ga miskinai [imam ahmad ne ya rawaitu shi, kuma albani ya hassana shi a cikin al,irwa,i 1175]

    ** na daga cikin sunnar da aka kaurace mata shafe kan yaron bayan an aske kansa da za,afaran

    Daga buraidah (r.d)ya ce: mun kasance a jahiliyya idan aka haifarwa dayan mu yaro, za, ayanka akuya kuma sai a shafe kan yaron da jinin ta, amma yayin da musulunci ya zo mun kasance muna yanka akuya a rana ta bakwai kuma mu aske kansa kuma mu shafe kan nasa da za,afaran"; [abu dahud ne ya rawaitu shi, kuma albani ya inganta shi a cikin sahihi abi dahud 2843]

    7-Yiwa jariri kaciya a rana ta bakwai

    Daga jaabir (r.d) ya ce annabi (s.a.w) ya yankawa hasan da husain aqiqah, kuma yayi musu kaciya arana ta bakwai. [baihaqi ne ya rawaitu shi]

    Daga dan abbas ya ce: " abubuwa bakwai suna da ga sunnar yaron da aka haifa arana ta bakwai: sanya masa suna, da yi masa kaciya, da kauda masa qazanta, da huda masa kunnan sa, da yanka masa aqiqah, da shafe kan yaron da jinin dabbar da aka yanka masa, da kuma yin sadaka da azurfa ko zinari da suka kai nauyin gashin kan sa da aka aske" [ baihaqi ne ya futar da shi acikin al,ausad"(1\133\2)]

    Sheikhul albani (rahimahullah) ya ce: daya daga cikin wadannan hadisai biyu yana karfafa daya duk da dai hanyar da suka futu ta bambanta, kuma babu tuhuma a cikin su, kuma haqiqa shafi,iiyah sunyi roko da shi, sai suka so ayi kaciya arana ta bakwai da haihuwa ; kamar yadda ya ke a cikin majmu,i1\307"; [tamamul minnah fiit ta,aliiqi alaa fiqihus sunnah juzu,i na 1 shafi na 68].

    ** kaciyar mace

    An tambayi sheikh bn baz- menene hukunxin kaciyar mace, shi ko akwai wata hujja baiyananna da take nuni akan haka?

    Sai shaikh bn baz rahimahullah]) ya amsa da cewa: da sunan allah kuma dukkan godiya ta tabbata ga allah

    Kaciyar mace sunnah, idan aka sami likitan da zai kautata hakan ko likitar da zata kyautata hakan; saboda fadin sa (s.a.w)-:((dabi,o,i biyar suna daga cikin dabi,o, in musulunci: yin kaciya, da da aske gashin mara, da rage gashin baki, da yankan kunba (farce), da tsige gashin hammata (wato askewa) [bukhari da muslim ne suka rawaitu shi] shi wannan hadisin ya game maza da mata bai banbanta suba acikin hukuncin sai dai ban da aske gashin baki domin shi ya ke banci maza ne kawai banda mata domin shi sufface ta maza" [majmu,ul fatawa10/47].

    Allah shine mapi sani

    Amsawa: abu abdullah

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.