𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Ma’aurata ne sun yi shekaru bakwai ba su nemi juna ba, amma ba wai suna faɗa ba ne. Komai na gudana daidai a tsakaninsu da sauran ’ya’yansu. Shin ko akwai wani laifi a cikin hakan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Asali dai idan barin saduwar zai janyo cutarwa ga ɗayansu shi ne malamai suka yi tsawa a kan hakan. Domin bai halatta wani
daga cikin ma’aurata ya cutar da ɗan’uwansa ba, musamman ta hana shi haƙƙinsa na saduwa.
Shiyasa a cikin Fiqhun Musulunci malamai suka ware
babi kamar: Baab Az-Zihaar inda suka tattauna a kan yadda Musulunci ya lalata
abin da mutanen Jahiliyya suke yi. Yadda waninsu yake siffata matar aurensa da
mahaifiyarsa, domin ya haramta wa kansa saduwa da ita irin yadda saduwa da
mahaifiyarsa ta harmta a kansa! Allaah da kansa ya kira wannan abin ‘munkarun
minal qaul’, ya ce
الَّذِينَ يُظَاهِرُونَ
مِنكُم مِّن نِّسَائِهِم مَّا هُنَّ أُمَّهَاتِهِمْ ۖ إِنْ أُمَّهَاتُهُمْ إِلَّا اللَّائِي
وَلَدْنَهُمْ ۚ وَإِنَّهُمْ لَيَقُولُونَ مُنكَرًا مِّنَ الْقَوْلِ وَزُورًا ۚ وَإِنَّ
اللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٌ وَالَّذِينَ يُظَاهِرُونَ مِن نِّسَائِهِمْ ثُمَّ يَعُودُونَ
لِمَا قَالُوا فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مِّن قَبْلِ أَن يَتَمَاسَّا ۚ ذَٰلِكُمْ تُوعَظُونَ
بِهِ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ شَهْرَيْنِ
مُتَتَابِعَيْنِ مِن قَبْلِ أَن يَتَمَاسَّا ۖ فَمَن لَّمْ يَسْتَطِعْ فَإِطْعَامُ
سِتِّينَ مِسْكِينًا ۚ ذَٰلِكَ لِتُؤْمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ ۚ وَتِلْكَ حُدُودُ
اللَّهِ ۗ وَلِلْكَافِرِينَ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Waɗanda ke yin zihãri daga cikinku game da
mãtansu, sũmãtan nan bã uwãyensu ba ne, bãbu uwayensu fãce waɗanda suka haife su. Lalle sũ, sunã faɗar abin ƙyãmã na magana da ƙarya, kuma lalle Allah
haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara. Waɗanda ke yin zihãri game da mãtansu, sa'an nan su kõma wa abin da suka
faɗa, to, akwai 'yanta wuya a gabãnin su shãfi jũna. Wannan anã yi muku
wa'azi da shi. Kuma Allah Mai ƙididdigewa ne ga abin
da kuke aikatãwa. To, wanda bai sãmu ba, sai azumin wata biyu jẽre a gabãnin su shãfi jũna, sa'an nan wanda bai sãmi ĩkon yi ba, to,
sai ciyar da miskĩnai sittin. Wannan dõmin ku yĩ ĩmãni da Allah da Manzonsa.
Kuma waɗannan hukunce-hukunce haddõdin Allah ne. Kuma kãfirai, sunã da azãba
mai raɗadi. (Surah Al-Mujaadalah: 2-4).
Haka kuma malaman suka tattauna a Babin Al-Ilaa’i
a kan wanda ya yi rantsuwa cewa ba zai kusanci matarsa ba. A inda shari’a ta ba
shi wa’adin watannin huɗu kaɗai. Idan suka cika to lallai ɗayan biyu ya auku: Ko dai ya dawo ya cigaba da saduwar, ko kuma ya sake
ta
لِّلَّذِينَ يُؤْلُونَ
مِن نِّسَائِهِمْ تَرَبُّصُ أَرْبَعَةِ أَشْهُرٍ فَإِن فَاءُوا فَإِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ
رَّحِيمٌ وَإِنْ عَزَمُوا الطَّلَاقَ فَإِنَّ
اللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Ga waɗanda suke yin rantsuwa daga matansu akwai
jinkirin watã huɗu. To, idan sun kõma, to, lalle ne Allah Mai
gãfara ne, Mai jin ƙai. Kuma idan sun yi
niyyar saki, to, lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani. (Surah Al-Baqarah:
226-227).
Kamar kuma yadda idan mijin ne yake cutuwa daga
wannan rashin saduwar sai shari’a ta yi kakkausar magana a kan matar
«إِذَا دَعَا الرَّجُلُ امْرَأَتَهُ إِلَى فِرَاشِهِ فَأَبَتْ فَبَاتَ غَضْبَانَ
عَلَيْهَا لَعَنَتْهَا المَلاَئِكَةُ حَتَّى تُصْبِحَ»
Idan namiji ya kira matarsa zuwa shimfiɗarsa sai ita kuma ta ƙi, har ya kwana yana
fushi da ita, mala’iku za su yi ta la’antar ta har zuwa wayewar gari. (Sahih Al-Bukhaariy: 3237, Sahih
Muslim: 1436).
Amma a nan dayake babu wata cutuwa daga kowane
sashe, to babu wani laifi a kan hakan, in sha’al Laah. Domin tun tuni malamai
suka sanya ƙa’idoji a cikin Qawaa’idul Fiqhiyyah kamar mai cewa: Ad-Darar Yuzaal. Wato, cutawa dole a
kawar da ita.
Wannan kuma sun samo ta daga maganar Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ne cewa
«لَا ضَرَرَ وَلَا ضِرَارَ »
Ba cuta kuma ba cutarwa. (Maalik: 2171, Ahmad:
22778, Ibn Maajah: 2341, kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi).
Allaah ya ganar da mu.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number:
08021117734
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.