Hukuncin Matar Aure Ta Yi Facebook

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, shin ko ya halatta ga matar Aure ta yi facebook, har ma da chatting?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikum assalam, Wannan tambaya ce mai wahala. Saidai abin da zance duk abin da zai amfaneta zata iya yi a facebook, saboda asali a shari’ar musulunci, duk abin da mutane suke aikatawa a mu’amalarsu ta yau da kullum halal ne, mutukar ba’a samu wani nassi wanda ya haramta ba, ko kuma ya kasance cuta tsantsa, haka ma idan mafi rinjayansa ɓarna ne, ka ga facebook kuwa babu wani nassi da ya haramta shi, sannan ba cuta ba ne tsantsa, tun da ana iya samun ilimin addini ta wannan kafa.

    Ya kamata ta daina yin chatting da waɗanda ba muharramanta ba in ba malamin da ta yadda da iliminsa da tsantseninsa ba, zata yi masa fatawa, saboda akwai maza da yawa da suke bi ta hanyar chatting don lalata matan auren da basu da kamewa. Wannan ya sa barin chatting da mazan da ba muharramai ba, ko kuma waɗanda suke neman auran matar, zai iya zama wajibi, saboda hakan yana kaiwa zuwa ɓarna, duk abin da yake kaiwa zuwa ɓarna, zai iya zama haramun ko makaruhi, kamar yadda malaman musulunci suka tabbatar.

    Allah ne mafi sani.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.