𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Idan Tufafin Mutum Yasamu Najasa Kuma Bai Samu Ruwanda Zai Wanke Ba, Bashi Dawani Tufar Dazayi Sallah Dashi Yaya Zaiyi?.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Sallah
bata ingantuwa da tufa mai najasa, Mutum zai iya sallah ne da tufafi masu
tsarki, saboda faɗin Allah madaukakin sarki:
ﻭَﺛِﻴَﺎﺑَﻚَ ﻓَﻄَﻬِّﺮْ
Ka
tsarkake tufafinka. (Suratul Mudasir aya 4)
Wata
mata tazo wajan Annabi Sallallahu Alaihi wasallam tace: Jinin haila yana taɓa
tufafin wata daka cikinmu yaya zatayi? Yace; Tawankeshi daruwa Tamatse shi
sannan Tayarfe ruwan, sannan saitayi sallah da tufafin. Bukhari ( 227) da
Muslim (291)
Annabi
Sallallahu Alaihi wasallam ya Umarceta data tsarkake tufar kafin tai sallah da
ita.
Idan
najasa tasamu tufafin mutuminda bashi da wani tufafin dazai sallah sai mai
najasar kawai, baya wuce halaye uku
1.
Zai iya wanke wajanda najasar datake jikin tufafin yai sallah dashi, kamar najasar
ajikin hannun riga ko gefen karshen riga take, wajibine wanketa yai sallah da
tufafin, domin yanada ikon sallah da tufafi mai tsarki babu uzuri akansa idan
yai sallah da najasa.
2.
Zai iya cire tufafin batareda Al'aurarsa ta bayyana ba, kamar idan yanasa wani
kayan daka ciki wanda yake rufe al'aurarsa ( gajeran wando, singileti, sikel
diras) wajibine yacire tufar yai sallah damai tsarki, saboda hakane Annabi
sallallahu Alaihi wasalla yacire takalminsa mai najasa ajikinsa yana cikin
sallah lokacinda jibirilu Alaihissalamu yasanar dashi akwai najasa ajikinsu.
Abu dauda (650) Albani ya ingnatashi acikin sahihu Abu dauda.
3.
Bashi da wani tufafin mai tsarki da zaiyi sallah dashi kuma bazai iya kawarda
najasar ba, magana ingantacciya cikin zantukan malamai shine zaiyi sallah
dawannan tufar mai najasar, saboda yazama mai uzuri, kuma sallarsa
ingnatacciyace bazai sake sallar ba bayan yayita da tufafin.
Shaikul
Islma ibnu taimiyyah Allah yajikansa yace: Wanda baisamu tufafi ba sai masu
najasa kaɗai? Wasu malamai sukace: yayi sallah tsirara, wasu sukace: yai sallah
da tufafin Amma yasake sallar, wasu sukace: Yai sallar dasu haka bazai sake
sallar ba, wannan shine ingantaccen zance cikin zantukan malamai domin Allah
bai umarci bawa yayi sallar farillah sau biyu ba, saidai idan baiyi wajibinda
aka ɗora masaba tunfarko, kamar yai sallah babu nutsuwa zai sake sallah kamar
yanda Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya Umarci wanda yai sallah babu nutsuwa
acikinta yace: ( Koma kayi sallah dan bakayi sallah ba, haka wanda yamanta
tsarki yai sallah babu alwala, zai sake sallah kamar yanda Annabi sallallahu
Alaihi Wasallam ya umarci mai lam'a akafarsa bai wankeba yasake alwala da
sallah, Amma wanda ya aikata abunda aka kaddara masa gwar-gwadon ikonsa Allah
maɗaukakin sarki Yace
ﻓَﺎﺗَّﻘُﻮﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻣَﺎ
ﺍﺳْﺘَﻄَﻌْﺘُﻢْ
Kuji
tsoran Allah gwar-gwadon ikonku.
Annabi
sallallahu Alaihi wasallam Yace ( Abunda na Umarceku kuzo dashi gwar-gwadon
Abunda zaku iya). Majmu'u fatawa (22/ 34-35)
Saboda
haka zaiyi sallah da tufafinda suke da najasar babu komai akansa domin anmasa
uzuri kuma bazai sake sallar ba, bayan uzurin yagushe daka kansa.
WALLAHU
A'ALAM.
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.