𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin ya halatta ga musulmi yayi sallah aɗakin da bangonsa an lilliqe shi da hotunan mutane da dabbobi? kuma ya halatta musulmi yayi sallah darigar datake da hoto?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Baya
halatta yin sallah agurin dayake akwai hoton abubuwa masu rai sai inda lalura,
saboda Abunda bukhari yaruwaito acikin sahihin littafinsa, (3322) da muslim (2106) daka Abi dalha Allah yakara yarda dashi daka Annabi Sallallahu Alaihi
wasallam ya ce: ( Mala'iku basa shiga gidan dayake akwai kare ko hoto
acikinsa).
An
tambayi fatawa lajnatul da'imah shin yahalatta ga musulmi yayi sallah aɗakin da bangonsa an lilliqeshi da hotunan mutane
da dabbobi? shin kuma yahalatta musulmi yayi sallah darigar datake da hoton
dabbobi?
Sai
suka Amsa: Hotunan Abubuwa masu rai haramun ne, sanya hotunan abubuwa masu rai
ajikin bangwan ɗaki
haramun ne, haka yin sallah aɗakin
da bangwansa akwai hoton abubuwa masu rai, bata halatta saida lalura, haka yin
sallah da tufafinda yake da hotunan dabbobi ko hoto mai rai bai halatta, saidai
idan mutum yayi sallar ta inganta tareda haramcin yinta awajan, yatabbata daka
Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ( lokacinda yaga labulen ɗakin A'isha yana da hotuna yai fushi ya yayyagashi
ya ce: ma'abota waɗannan
hotunan za'a dunga azabtar dasu ranar alkiyama ana cewa dasu ku rayar da abunda
kuka halitta).
Fatawa
lajnatul da'imah ( 1/705).
Saboda
haka wanda yayi sallah aɗakin
da yake da hoto ajikin bango yana fuskantar bangon da hoton yake, sallarsa
tayi, Amma kuma haramcin saka hoton da haramcin yin sallah awajanda yake da
hotuna yana kansa za'a rubuta masa zunubi akan hakan, abunda yake wajibi
gareshi shine tuba da istigfari zuwaga Allah, sannan ya gaggauta cire hoton
daka ɗakinsa dan samun yardar
ubangijinsa Allah maɗaukakin
sarki, Allah yakara shiryar damu baki ɗaya.🤲
WALLAHU
A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.