Idan Bera Da Sata, Daddawa Ma Da Wari

    IDAN ƁERA DA SATA, DADDAWA MA DA WARI

    ✍️✍️Daga:

    Imrana Hamza Tsugugi

    Za ka sami Malami a anguwa, shi ne Liman a duk salloli biyar. Wata rana idan ya yi jinkiri har magana ake gaya masa. Idan aka sami matsala tsakanin mata da miji ko iyaye da 'ya'ya, ko maƙwabta, shi za a kira ya yi sulhu. Idan aka yi rasuwa shi za a kira ya yi wankan gawa, ya yanka likkafani, ya yi sallah, kuma ya je a binne gawar da shi. Idan aka gama wannan, shi za a sa gaba wajen lissafi da tattara dukiyar mamaci da kuma rabon gado. Idan shekarar Zakka ta yi, masu kuɗin anguwa shi za su nema ya yi musu lissafi, kuma ya kasafta. Manoma za su kira shi idan sun yi girbi, domin ya lissafa musu yadda zakkar za ta kasance. Idan wani yana neman aure shi za a tura. Da wani zai yi kasassaɓar sakin matarsa, za a nemi wannan malamin kan yadda za a gyara. Ya karantar da matan anguwar, ya karantar da 'ya'yansu, har iyaye mazan ma ya buɗe musu aji. Duk waɗannan hidindimun, babu wani tanadi da aka yi masa domin kyautata rayuwarsa da ta iyalinsa.

    Yana da mata da 'ya'ya, suna bukatar abinci da sutura, suna zuwa makaranta, suna so su ji daɗi kamar yadda sauran 'ya'ya suke jin daɗi. TA WACE HANYA KUKE SO YA RIƘA GUDANAR DA RAYUWAR YAU DA KULLUM.

    idan Allah ya yi masa wani fatahi ya buɗe makarantar Islamiyya, matanku da 'ya'yanku za su zo su cika ta. Ya nemo mataimakan da za su taya shi gudanar da makarantar, amma 200 a ƙarshen wata kuna jin ƙyashin biya, wani sai ya kwashe shekara guda bai biya ko na wata ɗaya ba. Idan kuma aka kori yaran ku ce ba shi da mutunci. Duk da haka, da za a sami matsala a doki wani yaro ya sami rauni, ku ɗin ne dai za ku nemi kai shi wajen hukuma, ko kuma wata figaggiyar mata ta zaro wani munafukin silifas ta zo har makarantar ta shirga rashin mutunci.

    A karshe malaman su gudu makarantar ta sami matsala.

    Da wannan malamin zai sauya tufafi wani sai ya ce " Malam har da ku?"

    Tsakanin ku da wanda ya halicce ku, me zai hana wannan bawan Allah karɓar wani abu idan ɗan siyasa ko mai kuɗi ya ba shi.

    KUN HANA SU NAKU, KUMA BA KU SO SU KARƁI NA WANDA YA BA SU?

    YADDA KUKE SO KU JI DAƊI, SU MA FA SUNA SO

    WANE IRIN RASHIN ADALCI NE WANNAN???

    Allah ya shirya mu.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.