Idan Maniyyi Ya Zuba A Tufa Najasa Ne?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Malam ya karatu ya dalibai, Malam tambaya ce idan Maniyyi ko maziyyi ya zuba atufa ko jiki najasa ne ko ba najasa bane? Allah Kara ilimi.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    Farko dai akwai saɓanin malamai game da hukuncin shin maniyyi najasa ne, ko ba najasa bane?

    Kuma saɓanin ya samo asali ne daga fahimtar da malamai suka yiwa wasu hadisai guda biyu waɗanda aka riwaitosu duk daga Nana A'ishah (rta).

    Tace : "Na kasance ina wanke janabah (wato maniyyi) daga tufafin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam sai ya fita zuwa sallah alhali gurbin ruwan yana jikin tufafinsa".

    Da kuma hadisin da tace "Na kasance ina kankareshi (da farcena) daga tufafin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam kuma yayi sallah acikinsa".

    Duk wadannan hadisan akwaisu cikin Bukhariy da Muslim da wasu litattafan.

    Maluman Mazhabin Shafi'iyyah da Hanbaliyyah da kuma Sufyanuth Thauriy da Abu Thaur sunce maniyyi ba najasa bane. Hujjarsu ita ce Nana A'ishah tace tana kankareshi daga tufafin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Kuma da ace maniyyi ba tsatsarka bane, da kankarewa Kaɗai bazata isar ba. Kuma wannan ita ce fatawar manyan Sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam irin su Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib, da Abdullahi bn Abbas, da Abdullahi bn Umar, da Sa'adu bn Abi Waqqas da ita kanta Nana A'ishah (Allah ya yarda dasu baki ɗaya).

    Imam Malik da Imam Abu Hanifah (Allah ya jikansu) sun ce maniyyi najasa ne. Hujjarsu ita ce hadisin da Nana A'ishah (ra) tace tana wankeshi daga tufafin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Kuma sun ce saboda yana fita ne daga mafitar fitsari. Kuma tunda fitsari najasa ne, don haka shima najasa ne.

    Amma gaskiya waccen fatawar ta farko (fatawar Shafi'iyyah da Hanbaliyyah) tafi Qarfin hujjah mai karfi tare da cewa ta samu tushe daga sahabbai (Allah ya yarda dasu).

    Amma babu saɓani cikin wajibcin yin wanka saboda fitarsa ta hanyar mafarki ko a farke ta dalilin jima'i ko motsuwar sha'awa ko shafa, ko kallo.

    Shi kuwa maziyyi, dukkan maluman fiqhu sunyi ittifaki akan cewa najasa ne shi. Kuma idan ya taɓa tufafi wajibi ne sai an wankeshi.

    Don karin bayani aduba littafin Ta'aseesul Ahkam na Shaikh Ahmad bn Yahya Annajmiy (juzu'i na daya shafi na 86 zuwa na 87)da kuma shafi na 62 - 63.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    HUKUNCIN SUTURAN DA MANIYYI YA TAƁA

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    malan da fatan kana lafiya tambayace dani tambayata itace ya masayin suturan da manniyi yataba wanne irin wanke akeyi mata ruwa ba sabulu ko ba omo?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    To ɗan uwa shi kansa maniyyin Malamai sun samu saɓani dangane da hukuncinsa ma'ana Shin maniyyin Najasane ko ba najasa bane?

    Wasu malaman sun tafi akan cewa naniyyi najasa ne, inda kuma Wani ɓangare na malamai sukace maniyyi ba najasa bane, amma dai fahimtar da muke kai ita ce fahimtar malaman da suka tafi akan cewa Maniyyi ba najasa bane.

    sabida haka idan miniyyi ya taɓa tufafi ya halatta ayi sallah da tufafin mustahabbi ne a wankeshi Amma dai ba najasa bane, Saidai kuma fitarsa ta hanyar Jima'i, Mafarkin suduwa ko wasa yana wajabta wanka. Sabida haka idan mutum ya wanke maniyyin to shine yafi, sai ba dole ne sai an sanya sabulu ko omo yayin wankewar ba idan an wanke da ruwa ya wadatar

    Domin neman karin bayani dangane da hukuncin maniyyin Sai a duba Al'mugni na Ibn qudama (1/736)

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.