𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Idan Mutum ya auri Mace akan cewa Budurwa ce, bayan ya keɓe da ita sai ya tarar da ita ba a matsayin budurwa ba, to ya zai yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Hakan yana da dalilai, ta yuwu budurcin ya tafi ba
ta dalilin aikata Zina ba, dan haka ya wajaba a kyautata mata zato matukar a
zahiri mutuniyar kirki ce, kuma a zahiri tsayayya ce a addini, dole a kyautata
mata zato saboda hakan, ko kuma ta taɓa aikata alfasha amma ta tuba kuma tayi nadama
daga baya alheri ya bayyana gareta, to hakan bazai cutar dashi Mijin nata ba,
kuma ta yuwu budurcin nata ya gushe ne saboda tsananin jinin Al'ada da take yi,
domin lallai tsananin jinin Al'ada yana gusar da budurci kamar yadda Malamai
suka ambata, Wani lokaci kuma budurci yana gushewa ta dalilin tsalle-tsalle
daga wani waje zuwa wani wajen, Ko ta sauko daga saman wani waje zuwa 'kasa da
'karfi, budurci yakan gushe ta dalilin hakan, ba lallai bane sai ta hanyar aikata
zina yake gushewa ba, a'a, idan Mace tayi ikirarin gushewar budurcinta ta wani
dalilin da ba alfasha ba to babu matsala, ko kuma ta hanyar alfasha ne amma sai
dai ta ambata cewa tilasta ta akayi ko fyaɗe aka yi mata , wannan ma bazai cutar dashi ba, idan har tayi jini ɗaya bayan faruwar lamarin (domin istibra'i), ko ta ambaci cewa ta tuba
tayi nadama, kuma ta aikata hakan ne da rashin sani bisa kuskure sannan ta tuba
tayi da na sani, hakan bazai cutar dashi ba, kuma bai kamata ya yaɗa hakan ba, kuma ya kamata ya rufa mata asiri, idan ya tabbatar da cewa
tana da gaskiya kuma tsayayya ce kan addini, to ya zauna da ita ko ya saketa
tare da rufa mata asiri Kada ya bayyana abun da zai kawo sharri da fitina"
Majmu'u fatawabni Baaz (20/286).
AMSAWA
Ash-Sheikh Abdul-Azeez Bin Baaz R.A
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.