Ina Ji Kamar Na Kashe Aurena

    TAMBAYA (145)

    Assalamu Alaikum. Dan Allah malam inada tmby

    Malam inajin kamar nakashe aurena saboda mijina bayabani duk wata kulawa dazata gusarmin da sha'awata daga kan duk wani da namiji shekararmu takwas da aure Yaya uku da cikin na hudu Kuma nice ta uku agurinshi Kuma Yana ciyar damu kamar yanda Allah yace Yana Kuma biyan kudin maganin duk wata lalura datasamu Yana mana dinki duk sallah Kuma Yana mu'amalantar Yan iyaye da yan uwanmu cikin martabawa, Babbar damuwar shine Dan kasuwa ne Yana fita kullum da kamar misalin karfe 7 ko 8 nasafe Sannan bazai dawoba sai karfe 12 ko 1 nadare

    Kuma idan yadawoma bazai iyayin fira damuba komunyimasa yakan nuna bayaso saidae ayishiru yakunna kallo awayarsa yaci abinci yayi bacci ko kwalliya nayi Dan na Burgesa zai nunakamar banyi komaiba tun inakorafi har nagaji nadaina babu wani shauki ko burgewa da mace takeyiwa mijinta kwanciyar aurenma sai idan shi yake da bukatarki idan bahaka ko kinaso shi bayada ra'ayi haka dasafe dayatashi yayi sallah zaiyi wanka Yana gama shiryawa shikenan zaidamu Azo adebi abinci shi sauriyakeyi kana gaidashi wallahi wani lokacin kamar Wanda yayi gudu haka yake amsawa da haki

    Sannan tarbiyar yarana yasakarmana saidai mu mata wallahi malam agidan ko fashin sallah zakai badalili babu maicewa danme haka yakemana duka matan nasa damuwar tana damunmu saidae muzanta atsakaninmu duk wasu Abubuwa nasamun ladan aure munrasashi. saidai nazaman gidan aure da girki idan yazo kanka kayi ko away bashi da lokacin iyalinsa wani lokacin idan fitar gaggawa tasami mutum yakirashi awaya wallahi kinkira yakeyi har takai wasu acikin matan sukan fita unguwa say adadi da yawa batare da saninsaba saboda rashin lokacinsa Allah yakarawa malam lafiya kaji dalilin kayi hakuri da yawan rubutu

    AMSA

    Waalaikumus salam, Warahmatullahi, Wabarakatuhu

    Alhamdulillah

    Da farko dai Ina tayaki alhini saboda halin jarabawar rayuwa da kika shiga, Allah yana jarraba ki ne Ya ga shin za ki koma gareShi ne don neman taimakon Sa bisa wannan jarrabawar, Kamar yanda ya fada

    ( الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ )

    الملك (2) Al-Mulk

    Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.

    Kuma in Sha Allahu da akwai mafita domin kuwa dukkan tsanani yana tare da sauqi kamar yanda Allah [Subhanahu wata'ala] ya fada

    ( فَإِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا )

    الشرح (5) Ash-Sharh

    To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.

    ( إِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا )

    الشرح (6) Ash-Sharh

    Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.

    Yawancin mazaje musamman na yanzu sam sam basa yiwa matansu adalci

    Indai yanda kika fada haka zancen yake to haqiqa wannan Mijin naku baya muku adalci Kuma abinda yake kawo irin wannan matsalar shine: rashin koyi da kyawawan halayen Annabi Sallallahu alaihi wasallam da kuma jahiltar bin Sunnar sa

    Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya kasance abin koyi ga dukkan al'umma kuma koyi da shi ne kadai mafita a garemu

    Irin wannan matsalar ce ta sa ake son a binciki halayen mutum da kuma kyakkyawar mu'amalarsa da mutane kafin a yi zamantakewar auratayya da shi

    Idan kika duba cikin littafin "Shama'ilil Muhammadiyya" na Abu Isah at-Tirmidhi zaki ga yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam yake gudanar da mu'amalarsa da iyalansa

    A cikin littafin sa mai suna "Adabul Mufrad", Imamul Bukhari ya kawo ladubbai dayawa akan yanda mutum zai aiwatar da al'amarin rayuwar sa na yau da gobe kamar yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar damu

    Haka ma a cikin littafin "Seerah" zaki ga yanda Ma'aiki tsira da amincin Allah su qara tabbata a gareshi yake nuna tsantsar love da kulawa ga matayensa. Nana Aisha Radiyallahu anha tace duk sanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam zai shigo gidansa Yana sumbata [kissing] dinsu, wanda tuni turawa suka kwace wannan koyin. Alhalin mu musulmai ne yakamata mu dinga dabbaqa wannan Sunnar a gidajenmu. Idan kuka karanta littafin "Guidelines To Intimacy In Islam" wato "Shiriya akan tafiyar da rayuwar aure a musulunce" zaku amfana matuqa da ilimin da littafin ya qunsa

    Duk rashin karanta irin wadannan littattafan da Kuma maida hankali a iya Kasuwanci zalla ne yasa idan namiji yayi aure zai wahala ka ga yana bawa iyalansa cikakken lokacin tattaunawa akan wata matsala ballantana Kuma ya ware lokacin fira

    Allah Subhanahu wata'ala ya bawa mace wata irin baiwa ta musamman wadda zaka ga ta iya sarrafa akalar mijin ta kamar yanda makiyayi zai iya sarrafa dabbar sa

    Da kisisina, iyayi, iya magana mai dadi, kallo mai sace zuciya da kuma shagwaba kadai mace zata iya sarrafa mijinta, sai yanda kika so kiyi dashi

    Rashin sanin dabarun iya sarrafa miji ne yake saka wasu Matan suna fadawa tarkon shaidan su fara bin tsinannun bokaye da yan tsibbu wanda a karshe kuma mace ta je ta siyarda imaninta. Wal'iyazubillah

    Duk mijin da zai bar gida tun karfe 8 na safe har zuwa karfe 12 na dare wannan kam ya zama bawan kudi. Bazai iya ware awa guda cur ya saurari maganar matarsa ba. Kusan dukkan tunanin sa yana kasuwa. Kwanciyar shimfida zai yi ta ne domin gusar da sha'awar kansa amman ba ta matarsa ba

    Ta gamsu ba ta gamsu ba, ba ruwansa indai shi ya gamsu. Wannan yana daga cikin dalilan da suke sa indai mace ba mai tsoron Allah ba ce ba sai kaji an ce an kamata tana lalata da wani a waje. Sai wadda Allah ya tseratar

    Shawarar da Zan baki anan itace

    Ki dinga tashi cikin tsakar dare kamar irin 2 ko 3 ki yi ta nafilfili kina fadawa Allah buqatunki. Ki nunawa Allah da gaske kike, ki fada maSa buqatunki musamman idan kikai sujjada. Ki roqi Allah da wadannan addu'o'in

    Kiyi salatil Ibrahimiyya

    Sannan sai kice: "La'ilaha illa antas subhanaka inni kuntu minazzalimeen" kamar yanda Annabi Yunus [Alaihis Salam] ya fada a cikin kifi

    Ki tuno da addu'ar da Annabi Ibrahim [Alaihis Salam] yayi a lokacin da aka jefa shi cikin wuta: "Hasbunallahu wani'imal wakeel"

    Ki fadawa Allah buqatunki

    Sannan sai ki sake yin salati ga Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasallam

    Kada ki gaji da yin hakan ko da sau 1 ne a kowanne sati, In Sha Allahu zaki ga sauyi a zaman ku

    Haka zalika, duk sanda mijinki ya dawo komin daren da zaiyi ki dinga tarbarsa cikin girmamawa. Idan kin fahimci yana cikin walwala sai ki bijiro masa da tambaya: "Nikam my Love me yasa kwana biyu ka sauya, ba ma fira akan yanda muke a da, ko wanine yake bata mata rai a Kasuwa". Da irin wadannan tambayoyi zaki iya jin dalilan da suka sa baya baku yalwataccen lokacin

    Sannan Kuma zata iya yiwuwa kin Bata masa rai ne alhalin ke ba ma ki sani ba, ta hanyar janyo shi a jiki da yi masa shagwaba ne kadai zaki iya gano inda gizo ke saqar

    Sannan Kuma idan bakya zuwa Islamiyyah to yakamata ki fara zuwa ki zama ustaziyar dole ta yanda idan wata matsala ta taso shi kansa Mijin zai dinga tambayar ki me addini yace gameda abu kaza da kaza domin kuwa babban abinda mata basu sani ba shine majority maza ba sa son ace mace ta fi su ilimin addini

    Shima Kuma kamata yayi ace yana karanta littattafan addini, ya dinga ware lokaci yana karatu don neman dacewa a duniyarsa da lahirarsa

    Kinga kenan duk sanda kema kika fara neman ilimi tuquru dole Mijin ki zai duba darajar wannan ilimi naki ya dinga baki kulawa wadda a da can baya baki

    Idan Kuma duk da haka kika ga bai daina abinda yake ba Kuma hakan zai iya sa ki sabawa Allah musamman ta bangaren rashin samun gamsuwa to sai ki sanar da waliyyanki, a tara ku ga ki ga shi a tambaye shi dalilan da suka sa ba ya iya biya Miki buqata

    Idan ba shi da lafiya ne to sai a bashi damar neman magani idan Kuma ya nuna shi bazai sauya ba to idan zaki iya haquri da ci gaba da zama dashi hakan zaifi Miki akasin haka Kuma zaki iya rabuwa dashi [Kul'i] indai za'a shiga haqqinki

    Wallahu ta'ala a'alam

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu an la ilaha illa anta astaghfiruka wa'a'tubu ilayka

    Amsawa

    Usman Danliti Mato, (Usmannoor_As-salafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.