Lakabin Sarautar Banaga Daga Tsohuwar Daular Zamfara Ne Asalinta

    Laƙabin Sarautar Banaga Daga Tsohuwar Daular Zamfara Ne Asalinta

    Banaga sunan wani Mayaƙi ne da ya fito daga jinsin Zamfarawan da suka samar da Masarautar Mafara /Talata Mafara ta yau. Waɗan da ke da zumunci da Zamfarawan Masarautar Bukkuyum da Gummi dukan su dai suna a Jihar Zamfara ta yau ne.

    Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau muzakkarin gaske ne da ya fito daga tushensa tun suna zaune a Tunfafiya(Tunfafiya tana akan Titin Gusau zuwa Sakkwato, yan kilomitoci kaɗan kafin zuwa garin Talata Mafara, hedikwatar Masarautar Zamfarawan Mafara ta yanzu a Jihar Zamfara) a ƙarshe ƙarshen ƙarni na 18.

    Ya tasarwa Kudu maso gabashin Tunfafiya /Mafara sai da ya ƙirƙiri gari da ya kira da Birninsa, watau " Birnin Banaga" . Anan ya zauna har zuwa bayyanar Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da mataimakansa da suka shigo yankin daga wajensu na asali, kenan su Malam Muhammadu Daɗe/Daɗi /Da'e wasu Fulani Adarawa da suka fito daga wani yanki na Jamhuriyar Nijar ta yau.

    Daga Birnin Banaga ne (a halin yanzu wannan Birni ne ake kira "Tsohon Birnin Banaga dake cikin Masarautar Maru a Jihar Zamfara) ya dinga kai samame ya zuwa iyakar Daular Katsina ta yamma(gabas da shi kenan) ya kuma matsawa Masarautar Maska lamba da hare-hare, uwa uba ya hana sakewa ga masu jihadin jaddada addinin musulunci na Daular Usmaniya.

    Da al'amarinsa ya yi tsanani ne Malam Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya umurci Malam Muhammadu Daɗi /Daɗe /Da'e da zuriyarsa da a lokacin suke zaune a yankin Jabaka (Jabaka hedikwatar gunduma ce a Masarautar Maru ta yau) da Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa dake zaune a yankin Yandoto da Malam Muhammadu Bachiri dake Bunguɗu da Malam Karaf dake Kannu(Kannu gunduma ce a halin yanzu a cikin Masarautar Birnin Magaji) da su fitar da shi daga wannan yanki.

    Da wannan ne sai suka yi masa taron dangin da ya sanya ya fice daga wannan Birni nasa, watau "Birnin Banaga". Ya je yamma ya ƙirƙiri sabon mazauni da ya kira "Murai" /"Morai" ya ci gaba da mulkinsa da laƙabin "Banagan Murai" ( Murai/Morai hedikwatar gunduma ce a Masarautar Talata Mafara a Jihar Zamfara).

    Ya sake fita daga Murai ya je yamma ya ƙirƙiri garin Anka ya ci gaba da rayuwa tare da jama'arsa har zuwa shiyoyin 1815 zuwa 1824 lokacin da Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo daga zuriyar Sarkin Zamfara Abarshi ( Zamfarawan da suka zauni Dutci/Dutsi ta Ƙasar Zurmi, Jihar Zamfara tun a shekarar 1300 da Birnin Zamfara a Ƙasar Isa, Jihar Sakkwato har zuwa 1764 da Kiyawa a Masarautar Birnin Magaji da Banga da Ƙuryam Madaro dake Masarautar Ƙaura Namoda da Sabongarin Damri a Masarautar Bakura duka a Jihar Zamfara) suka sake fitar dashi da jama'arsa duk da yake ba ta hanyar yaƙi ba.

    Daga Anka ne ya fita ya sake girka wani gari da ya kira "Sabon Birnin Banaga" da ke Kudu maso gabashin Anka( wannan gari hedikwatar gundumar Sabon Birnin Banaga ne a Masarautar Anka, Jihar Zamfara) inda a nan ne Allah SWT ya yi masa wafati.

    Kenan daga Tunfafiya zuwa Birnin Banaga zuwa Murai zuwa Anka zuwa Sabon Birnin Banaga ne Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau ya yi rayuwarsa.

    Daga baya ne masu jihadi suka mayar da garin Maru a matsayin sabuwar hedikwatar wannan yanki da Birnin Banaga yake, suka naɗa Malam Ummaru ɗan Malam Muhammadu Daɗi /Daɗe /Da'e a matsayin jagora da laƙabin "Banaga" a matsayin Sarautarsa domin taskace Tarihin wannan muzakkari watau Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau.

    Daga wannan ne wasu Masarautun Arewancin Nijeriya suka ari laƙabin wannan Sarauta ta "Banaga" suka ci gaba da amfani da ita/shi.

    Allah SWT ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, ya yalwata bayanmu, amin.

    Ana iya duba "Tarihin Zamfara" na Dr. Kurt Krieger wani Baturen Jamus da aka buga a shekarar 1959 da "The Rise and Collapse of Zamfara Kingdom" PhD Thesis na Dr. Garba Nadama (ABU Zaria, 1976) da "The History of Zamfara from 1764 to 2013" PhD Thesis na Dr. Sanusi Shehu Gusau (UDUS, 2017) da Littafin Infak'ul Maisur wallafar Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da kuma Littafin Shaihin Malami Sa'idu Muhammad Gusau na Jami'ar Bayero, Kano da ya wallafa akan rawar da masu jihadi suka taka a Katsinar Laka domin samun ƙarin bayani.

    Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.

    Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.
    08149388452, 08027484815.
    birninbagaji4040@gmail.com
    Jumu'a, 28/06/2024

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.