Ticker

Mala'iku Ba Sa Shiga Gidan Da Akwai Hoto Ko Kare A Ciki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam na ji an ce wai Mala'iku basu shiga gidan da akwai hoto ko kare aciki. Menene gaskiya magana?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

To ɗan uwa mala'ikun da suke ricodin ɗin aiyukan bayi suna shiga gidan da akwai hoto. Idan akace duka basa shiga kaga kenan sai mutum yayi ɓarnarsa ba tare da an rubuta masa zunubi ba, sai abin ya zama wasa kenan, to malaman da suka ce ba duka ba wannan tana daga cikin hujjarsu, amma dai biyo ni don mu duba sauran bayanai.

Da farko wane mala'iku ake nufi waɗanda ba sa shiga gidan da akwai hoto a ciki?

Al Imamul Bukhaari (3226) da imam Muslim (2106) sun ruwaito hadisi daga Abu Talhah (Allah ya ƙara masa yarda) cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce; “Mala'iku basa shiga gidan da da akwai hoto acikinsa.”

Al Imamul Nawawi (Allah yaji kansa da rahama) ya ce: Malamai sun ce: Dalilin da ya sa basa shiga gidan da akwai hoto acikinsa saboda akwai zunubi mai raɗaɗi, kuma gasa ne da halittar Allah, kuma wasu hotonan hotona ne da ake bautarsu maimakon Allah. Gameda mala'ikun da basa shiga gidan da akwai kare a cikinsa ko hoto, to sune mala'ikun da suke zuwa da rahama, albarka kuma suke rokarwa bayi gafara. Ga me da Mala'ikun da suke recodin ɗin aiyukan bayi, suna shiga ko wane gida kuma basa taɓa rabuwa da ɗan adam a ko wane hali, saboda aikinsu shi ne rubuta aiyukan bayi kawai.

Sharhin hadisin Muslim, 14/84 ya ce Tuhfat al-Ahwadhi (8/72): Kalmar “Mala'iku basa shiga” yana nufin: mala'ikun rahama, ba mala'ikun recodin ba ko mala'ikun mutuwa.

Ibn al-Atheer (Allah ya yi masa rahama) ya ce: Abin da ake nufi shi ne mala'ikun da suke yawo ba mala'ikun ricodin ba ko waɗanda suke nan a lokacin mutuwa ba.

A cikin Al-Nihaayah, 4/789. Imamu Suwiti (Allah ya yi masa rahama) ya ce

Al-Khattaabi ya ce: abinda ake nufi shi ne mala'ikun da suke kawo rahama da albarka, ba masu rubata aiyuka ba.

Sharhin littafin al-Nasa’i, 1/141 Shaykh Muhammad ibn Ibrahim (Allah ya yi masa rahama) an tambaye shi: shin maganar sa akan “Mala'iku basa shiga gidan da da akwai hoto ko kare” Ma'anarsu daya a ma'ana kuma shin sun haɗa da mala'iku masu ricodi ko kuwa a'a? Sai ya amsa da cewa: da alama cewa ba su haɗa da wannan ba.

A cikin Fatawa wa Rasa’il Muhammad ibn Ibrahim, 1/169

Hotonan da suke hana mala'iku shiga gidaje hotona ne da suke da rai (wato zanen abin da yana da rai ko motsi), baya ga hotona da ake sawa na rashin ɗa'a.

Al-Khattaabi (Allah ya yi masa rahma) ya ce: Mala'iku basa shiga gidan da da akwai kare ko hoto da aka haramta ajiye shi...

Ga me da wanene ba'a haramta ajiyewa ba, shi ne kamar kare don farauta, noma ko gadin dabbobi, ko hotona waɗanda babu rai a jikinsu, kamar carpets, pillow wanda zaka ga akwai zanen flower ajikinsu, mala'iku basa hana su shiga.

Tuhfat al-Ahwadhi, 8/72 Shaykh Ibn ‘Uthaymeen ya ce: Idan hotonan an bi da su da daraja, kamar hotona akan carpet ko pillow, to mafi yawan malamai suna ganin cewa ya halarta.

To ɗan uwa bisa waɗannan hujjoji da maganganun maluma, mala'iku ba'a hana su shiga wani huri, saboda idan an haramta musu shiga to da wancen damar ba'a halarta ta ba.

LiƘa’ al-Baab al-Maftooh, 85/6 ga me da Sallah a wurin da akwai hoto, baya halarta, har sai dai idan musulmin dole aka yi masa kuma aka hana shi cire hoton.

Malaman committee din fatwa su ka ce: Sallah a wuraren da akwai hoto be halarta ba sai dai idan akwai wani dalili. Haka mai yin Sallah da hoto a jikin rigarsa hotonan dabbobi, shi ma baya halarta ya yi Sallah da wannan tufafin, amma idan ya yi to sallarsa ta yi amma ya aikata haramun, saboda haka dole ne ya yi istigfari akan hakan. Fatawa al-Lajnah al-Daa’imah, 1/705

ALLAH NE MAFI SANI.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments