Matsayata Dangane Da Zanga-Zanga A Nijeriya

    إِنَّ الأُمورَ إِذا الأَحداثُ دبّرها

    دونَ الشُيوخ تَرى في بَعضِها خَللا

    إِنَّ الشَباب لَهُم في الأَمرِ معجلَةٌ

    وَلِلشُيوخ أَناة تدفع الزللا

    -الصفدي

    Y. A. UMAR

    Da sunan Allah Mai Rahama Mai Rahama, tsira da aminci su ƙara tabbata akan FIYAYYEN HALITTA da iyalansa da sahabbansa baki ɗaya. Haƙiƙa tattaunawa yana ta gudana a duk matattaran al'umma, a sama da ƙasa, ma'ana; online and offline, gameda shirin zanga-zanga wanda aka shirya shi da manufar nunawa gwamnatin tarayya, irin wahalan da talakawa suke ciki a wannan ƙasa tamu mai ɗimbin abin mamaki, wato Najeriya. Wannan shiri na zanga-zanga, ance matasa ne suka shirya shi, amma koda yake ana ganin akwai masu take musu baya wajen ganin sunyi wannan aiki, wanda wasu masana da dama sukace, yana cike da haɗarurruka ga ƙasar kanta da su kansu masu shirin zanga-zangar, da sauran ƴan ƙasa waɗanda basuji ba, basu gani ba. Ga masu bibiyan labarai, jaridar Guardian ta ruwaito cewar, gwamnatocin Amurka, Ingila da Canada sun gargaɗi ƴan ƙasashensu akan zuwa ko yawo a ƙasar, musamman mazauna Najeriya a dalilin shirin zanga-zanga.

    Tun lokacin da aka sanar da aka sanar da shirin zanga-zangar, abubuwa suke ta faruwa kullum. Daga nusarwar da malamai sukayi akan haramcin zanga-zanga a musulunci, zuwa martanin matasan ta hanyar cin zarafin malaman a kafafen sada zumunta na zamani, zuwa magantuwar gwamnatin tarayya ta hanyar jami'an ta da yawa, zuwa yunƙurin Majalisar Wakilai, zuwa magantuwar gwamnonin jam'iyyar APC, zuwa sanar da buɗe shafin neman rance ƙarƙashin Ma'aikatan Matasa da Wasanni, zuwa sanar da shirin ɗaukan aiki a kamfanin man Ƙasar, wato NNPCL, zuwa maganan jagoran Kwankwasiyya, zuwa matsayin hukumar ƴansanda da sojan Najeriya akan zanga-zangar, zuwa matsayin da Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta ɗauka, zuwa ziyaran malaman addinin Islama ga shugaba Tinubu, zuwa matsayin Peter Obi akan zanga-zangar, zuwa yau Litinin da ake saura kwanaki kaɗan don gudanar da zanga zangar. Duk waɗannan abubuwa da suka faru kuma suke faruwa zuwa yanzu, sunci tura wajen isar da saƙon su zuwa inda suke so ya isa, ma'ana, wajen sauya akalar waɗanda suke so su isarwa da saƙon.

    Idan mun lura, an rabu gida biyu ne akan wannan zanga-zangar, masu neman dakata da masu yin zanga-zangar, sai kuma masu goyon baya. Don haka, duk wanda yayi magana yanayi ne don chanja ra'ayin waɗanda yake isar da saƙon sa garesu. Masu hanawa suna buri ne wajen ganin masu shirin zanga-zangar sun janye. Masu shirin zanga-zangar kuma, suna buri ne gwamnati ta magance matsalar da suke ciki, wanda a cewar su, itace silar shirya wannan zanga-zangar. A fahimta ta, duk ɓangarorin biyu ko kuma ɓangaren masu yunƙurin hanawa, sun gaza wajen samun abinda suke so. Toh shin, masu shirya zanga-zangar zasu samu tasu biyan buƙatar bayan fara zanga-zangar?

    Wannan tambayar itace masana da yawa suke ta ƙoƙarin amsawa ta hanyar kawo dalilai da dama, ciki har da tarihin irin yadda waɗannan zanga-zangar ta kasance a wasu ƙasashe da ma ƙasar nan, da wasu zamunnan baya, da zamanin ma da muke ciki. Akan hakan ne, nima naga dacewar na furta tawa MATSAYAR. Ko ba don komai ba, saboda nima ɗan Najeriya ne, kuma matashi, kuma wanda yake fama da tsadan rayuwa, saboda zaluncin shugabannin ƙasata, Najeriya. Da kuma tsare-tsaren rashin tausayi da jinƙai wanda gwamnatin Najeriya ta ringa sanarwa da aiwatarwa, ba tareda tunanin mezai faru ba, ko yaya talakawa zamuyi ba. Alhalin ita gwamnatin bata samar da wani tsari ba, akan yadda zata inganta rayuwar al'umma ta hanyar bunƙasa tattalin arziƙin ƴan ƙasa. Mubar wannan a gefe, domin ba shine manufar rubutun tawa ba.

    Manufata itace, kawo ƙarin dalilai da suka sanya matasa da sauran ƴan ƙasa shirya wannan zanga-zangar bayan zallan tsadan kayayyakin masarufi da ƙarancin abin hannu da tsukewar hanyoyin samun kuɗaɗen shiga. Amma fa kowa ya sani, ni mai wannan rubutu, na zaɓi wannan jam'iyya, da kyakykyawar fatan zata iya kai ƙasar ga tudun mu tsira kamar yadda aka tallata su a yayin yaƙin neman zaɓe, musamman, irin yadda aka nuna ƙaƙarin ɗan takaran, wato shugaba Tinubu wajen mayar da Legas yadda take a yanzu, hakanan shima mataimakin sa, Kashi Shettima da abinda yayi a Borno.

    Idan zamu iya tunawa, gwamnatin Buhari itace ta samar da shirin na N-Power domin samar da ayyukan yi da madogaran rayuwa ga matasan da suka gama makaranta da waɗanda basuyi karatun ba ma, kuma basuda aikin yi. Aka shirya shi a ɓangarorin buƙatun al'umma dabam dabam, kamar Ilimi da kiwon lafiya sai kuma sana'o'i. An gudanar da wannan shiri na tsawon shekaru kuma matasa da dama sun samu shiga cikin shirin inda suka samu daman buɗe wajajen sana'o'i da kasuwancin su a dalilin shirin. Amma a wanda ya zama na ƙarshe a gwamnatin Buhari, an ɗauki matasa da suka gama makaranta a tsarin shirin na N-Teach domin su koyar a makarantun gwamnatin da alƙawarin za'a biya su dubu talatin a kowace wata na tsawon shekara guda, aka tura su makarantu sukayi aiki, tun daga watan Satumba na 2022, zuwa watan Yulin 2023. Amma, kwata-kwata na watanni uku aka biya su! Shikansa biyan, anyi shine a watannin Fabrairu da Maris na shekara 2023, lokacin zaɓen shugaban ƙasa. Sauran haƙƙin na watanni tara, har yanzu, kuma ko labari babu akan yaushe za'a biya. Sai alƙawuran ƙarya da yaudara da gwamnati take tayi wa matasan. Ance an ƙwato kuɗin daga hannun wasu wai "consultants" kuma za'a biya, daga nan sai ji mukayi an cire minista da shugaban hukumar da take kula da shirin bisa zargin almundahana. Daga nan kuma babu wani labari. Na biyu, gwamnatin ta ƙaddamar da wani shiri na baiwa ƴan ƙasa kyautar Naira dubu hamsin, ga mutane dubu ɗaya a kowace jiga, da kuma rancen kuɗin farfaɗo da kasuwa ga masu kasuwanci, wanda jama'a suka cika, amma ƴan ƙalilan ne suka samu wannan kuɗi na dubu hamsin, rance kam babu wani labari akai. Har ila yau, gwamnatin ta bayar da tallafi akan a raba wa talakawa don yaye raɗaɗin talauci da yunwa da suke fama dashi, amma wannan tallafi tunda ya shiga hannun gwamnoni, labari akansa ya ƙare. Kuma gwamnatin tarayya batayi wani yunƙuri na sauya labarin ba, sai kawai ta sake basu wasu tirelolin na hatsi, wanda shima yanzu an fara ganin sa ana shirin kai shi kasuwa! Duk wani shirin da gwamnatin tayi alƙawarin yin sa don talakawa, babu wanda talakawa suke mora a halin yanzu. Har waɗanda ta gada daga gwamnatin baya, kamar NG-CARES!

    Duba da waɗannan abubuwa da wasunsu, kamar kashe kuɗin ƴanƙasa wajen gyaran gidajen shugaban ƙasa da mataimakin sa da kuma chanja jiragen fadan shugaban ƙasa da ƙarin alawus ga ƴan majalisu, da sauran abubuwan da ƴan Najeriya suke ganin rashin tausayi ne da damuwa da halin da suke ciki, don haka dole su fito su nunawa gwamnati cewar, ba zasu yarda a kashe su a tsaye, kamar yadda duk me fahimta haka zai fahimta.

    Toh amma hakan itace hanyar samun gyaran ko kuma hanyar da wasu masana cikin malaman addini da na zamani suke ta ƙira akai? Amsar wannan tambayar, itace manufar rubutuna na biyu. Wato zanyi ƙoƙarin kawo wasu hanyoyi da nake ganin zasu taimaka a shawo kan masu zanga-zangar, da ma kawo sauƙi wa al'umma. Da yawan waɗannan shawari, wasu sun bayar a wajaje dabam dabam.

    Kamar yadda na ambata a baya, daga cikin manufar da ta sanya ni yin wannan rubutu, akwai ƙoƙari da fatan ganin an samu mafita a halinda ake ciki. Kuma nayi imani cewa, waɗanda abin ya shafa kai tsaye wato matasan da kuma talakawa masu fama da rayuwa ƴan Najeriya, ya kamata su faɗi abinda suke ganin zai taimaka a samu gyara. Duk waɗannan abubuwa na samu kaina a ciki, ni dai matashi ne kuma ɗan Najeriya. Na samu shiga cikin shirin N-Power a zango na uku kaso na biyu, wato Batch C Stream II. An tura ni koyarwa a wata Makarantar Ƙaramar Sakandare a cikin garin Bauchi, inda nakai takardar turo ni daga N-Power da sauran takardu wa shugaban makaranta. Bayan tattaunawa da tantancewa, sun tambaye ni me zan iya koyarwa, inda nace musu komai zan iya koyarwa har Arabic da Islamic Studies, ba'a maganan Math da Comouter, domin takarduna sun nuna musu zan iya. Sai suka bani Basic Technology wa yaran aji ɗaya. Haka kuma na koyar tsawon shekarar karatun 2022/2023, kuma na tsawon zanguna ukun. Ajujuwa guda huɗu ne saboda yawan yaran, kuma ko wani aji akwai ɗalibai sama da 70! Kenan, na koyar da yara kusan ɗari uku (300), duk ƴan aji ɗayan sakandare ko kuma 'Basic Seven'! Haka nayi wannan aiki cikin wahala da sadaukarwa, da zimman taimakawa wajen yaye jahilci a makarantun da ƴan'uwanmu ƴaƴan talakawa suke zuwa. Duk wanda yasan makarantun gwamnati a jihar Bauchi dai, yasan babu kayan koyarwa balle na koyo, haka malaman suke fama, kuma nima haka naje nayi wannan fama. Abun sai wanda ya gani, 'very bad' ma yayi kaɗan ya siffanta lalacewar. Daga cikin abubuwan wahala a wannan aikin shine makin na jarabawa, Amma shima haka nayi su, koda yake nakan nemi taimakon wasu abokan aiki na a wani wajen aikin dabam. Amma a wani karon ma, ko takardar da yake ɗauke da sunayen yaran na ko wani aji wanda za'a shigar da jarabawar wato 'score sheet' babu, sai dai na rubuta sunan yaran a fallen takardar 'fullscap' da abinda kowa ya samu na kai musu makaranta! Banda wahalan da nasha wajen zuwa makarantar, musamman saboda banida abin hawa, Achaɓa nake zuwa nake dawowa, kai wataran ma da ƙafa nake takawa naje na dawo. Gashi wni lokacin ana tsananin rana, domin makarantar rana ce, suna fara darasi ne shabiyu da rabi na rana, 12:30pm zuwa huɗu da rabi na rana, 4:30pm. Amma a hakan, saida shugaban makarantar ya sanya mun "baka miss", wato dai bana fashin zuwa, a ranakun da mukayi ƙa'idar zanje, kuma a lokutan. Kai har samar da rubutaccen darussan da zamuyi a kowani zangon karatu nayi, wato 'lesson note'. Ina nufin wanda kwamfuta ta rubuta, kuma ni nayi rubutun a kwamfuta da kaina, kuma na buga shi ina amfani dashi wajen shiga aji don koyarwa. Haka nayi tsawon zangunan karatu uku, amma abin takaici, abin kaico, abin Allah wadai, abin baƙin ciki, Gwamnatin Tarayyar Najeriya bata biya ni haƙƙin da na chanchanta ba, na Naira Dubu Talatin N30,000 duk wata. Ko kuma ta bayar wasu jami'anta suka handame, kuma aka bar su! Irin wannan abu da me yayi kama? Ace ƙasar ka ce ta cuceka a lokacin da kake buƙatar taimako, ta zalunceka, ta kashe duk wani zimma da kake dashi na ganin ka taimaka wajen gyaruwan ƙasar ka.

    A irin wannan halin, duk wani kira da za'ayi wa matasa irina da su fito su nuna wa gwamnati ɓacin ransu da rashin amincewarsu da irin tsarin da ake gudanar da ƙasar su akai, da irin yadda hakan yake barazana wa goben su, toh sai tsananin dace ne zaisa bazan shiga ba. Amma duk cika-cikai da sharuɗɗan na shiga cikin irin wannan abu sun cika. Ba kawai zanga-zanga ba, ko wasu laifuka ne irin na ta'addanci aka kira mutum zai iya shiga, saboda neman mafita, kuma wasu irin waɗannan matasan sunada fikira da baiwa mai tarin yawa, wanda ƙasar su ko al'ummar bata damu dashi ba. Ba ni kaɗai bane, akwai ire ire na da yawa, waɗanda gwamnatin ƙasar nan da ta jihohin su, suka musu zalunci da rashin adalci iri dabam dabam, kuma suna ƙulle da abin a ransu, kuma suna jin haushi da takaicin abun, kawai sun rasa yadda zasuyi su bayyana wa gwamnati ne, kwatsam sai ga dama ta samu, WAYE ZAI IYA HANASU? Suma bazasu iya hana kansu ba! Domin, sunce "hungry man is an angry man", wato "duk mayunwaci, mafaɗaci ne" ko kuma fusatacce ne, ai kusa yake da yin faɗa saboda fusata. Kuma da yawan waɗanda zasu fita wannan zanga-zangar, a halinda suke ciki kenan. Gwamnatin taƙi ko ta gagara yin abinda ya kamata. Ai kuwa kunga dole talakawan ƙasa su fito zanga-zanga. Koda yake, NI bazan fita ba.

    Toh meyasa ni bazan shiga wannan zanga-zangar ba? Kamar dai yadda nayi take ga rubutun nan, wato MATSAYATA, dalili na uku na yin rubutun shine bayyana matsayata don tayiwu, na samu wasu su yarda dani akan ƙin fita ita wannan zanga-zangar. Hakanan, ina fatan kiran da zanyi, zai iya kaiwa kunnuwan waɗanda zasuyi gyara akai. Kamar yadda zantuka suka gabata daga masana dabam dabam akan halaccin zanga-zanga a tsarin mulki irin na Dimokraɗiya, domin hatta shi kansa shugaba Tinubu, wanda a halin da ake ciki shi yafi kowa cin moriyar Dimokraɗiya, yace ya taɓa shiga zanga-zanga a baya. Wato shima tsohon ɗan zanga-zanga ne. Sai dai fa, mu bamu bautan Dimokraɗiya. Munada Ubangiji wanda ya turo mana da manzanni don su koya damu yadda zamu bauta maSa ta hanyar addini. Akan haka na tattara bayanai da dalilaina na ƙin shiga zanga-zangar kamar haka;

    1. Ni dai musulmi ne, kuma malaman musulunci sunce baya halatta ayi fito-na-fito da shugaba, ta hanyar zanga-zanga. Kuma na yarda da wannan koyarwa. Kuma ina ƙiran duk matasan masu wannan shiri daga cikin musulmai, da suma subi wannan kira. Hakanan, suma kiristoci su bi wannan kira na barin fita wannan zanga-zangar, musamman saboda CAN tace bata goyi baya ba, kamar yadda jarida Daily Trust ta rana Lahadi ta ruwaito, cewar reshen CAN na jihar Neja, tayi kira wa matasa da kar su fita. Don haka, mu saurari maganan manyan mu kuma jagororin mu a addini, mu ƙaurace wa fita wannan zanga-zangar.

    2. Duk zanga-zangar da muka san an taɓayi a baya, ko anan ƙasar ko a wata ƙasar, yawanci bata haifar da ɗa me ido ba! Musamman idan ta haɗu da gwamnati irin na shugaba Tinubu, saboda zasu iya yin komai don tabbata a mulki, kamar yadda sukayi don su hau mulkin. Yaushe muke tunani zasu bari a musu adawa me tsanani irin zanga-zangar ƴan ƙasa wanda wahalan rayuwa ta sanya su fito. Kuma duk munji irin gargaɗin da akeyi akan cewar, ɓata gari suna iya shiga cikin zanga-zangar don tayar da husuma, ɓarnata dukiyar al'umma, ko sace-sacen kayan jama'a. A yanzun, akwai hasashen da jami'an tsaro sukayi a Yobe cewar, ƴan Boko Haram suna shirin shiga cikin ƴan zanga-zangar don kai hari wa jami'an tsaro. Sun bayyana haka ne bayan harin da aka kai wani chaji ofis anan jihar Yobe. Toh kunga babu wani buƙata ko alfano, mu bada ɓata gari mafaka domin suyi aika-aika.

    3. Da yawan matasan da zasu shiga wannan zanga-zangar, babu umurnin iyayensu akai, bal, wasu ma iyayen nasu sun hanasu, amma sunyi kunnen uwar shegu, sun rantse sai sun shiga. Toh duk abinda zamuyi, mu kula da haƙƙin iyayenmu, domin saɓa musu yana cire albarkan dake cikin aiki. Yana kuma janyo tasgaro ga aikin. Saboda girman haƙƙin su. Don haka, yaku ƴan'uwana matasa, na rantse muku da Allah, duk wanda ya haɗa hanya da wanda yake cikin fushin iyayen sa, toh shima sai matsala ta sameshi. Na tuna wani abu da ya faru dani da wani abokina, shekaru kusan goma yanzu. Wata rana, wannan abokin nawa yace don Allah na raka shi gidansa da yake ginawa acan wani unguwa mai nisa, saboda inada mashin sa'ilin nan, sai nace masa toh badamuwa. Chan da yamma lis, sai na ɗaukeshi muka tafi. Munyi dab da isa wajen, sai mashin tayi faci, cikin ikon Allah kuwa, muka samu masu faci a kusa da wajen. Lokacin da muka iso wajen masu faci, tuni magariba yayi. Sai muka bayar da facin mukaje yin Sallah, bayan dawowar mu, sai me faci yace ai ƙusa muka taka kuma ya lalata tif ɗin, gaskiya a shawarin sa, sai dai mu chanja tif, mukace babu damuwa, a ina za'a samu tif a daren nan, yace babu, amma yanada tsoho mekyau, wato second, muka yi ciniki aka sanya tif. Koda nazo biyan kuɗi, sai na rasa lalitar ajiyan kuɗina, wato wallet. Shi kuma daman bashida kuɗi a sa'ilin. Mukayi jungum-jungum a gaban mutumi, sai kawai na tuna cewar, ta yiwu na mantashi a gida ne. Sai nace bari naje na ɗauko. A lokacin babu yawan transfer, koda yake ni inayi, amma da yawan mutane har masu shaguna, basuyi. Sunfi gane a basu kuɗi a hannu. Ga waje da nisa, bama kusa da inda bankuna suke bane, toh ko kusa ne, ina katin cire kuɗin, shima yana cikin lalitar. Haka dai nahau achaɓa don ɗauko lalitar tawa a gida. Koda na iso gida nabar me mashin yana jira na a ƙofar gida, ina zuwa ƙofar ɗakin, sai makullin yace ɗauke ni, ashe nabarshi a jikin mashin domin suna tare ne da makullin mashin ɗin. Ai sai kawai na tsaya turus, na rasa madafan kamawa. Sai na yanke shawarin na ranta na koma kawai, haka kuwa akayi, na ranta na koma. Na biya mai achaɓa da mai faci muka kamo hanyar dawowa gida batareda munje gidan ba, saboda dare yayi domin har anyi sallar Isha'i. Muna tafiya a hanya, kawai sai abokin nawa yake gayamun yadda sukayi da Dikko, wato mahaifiyar sa, kamar yadda suke kiranta. Kawai nan take sai naga ashe ba a banza irin wannan ibtila'in ta same mu ba, shi ya janyo mana. Kuma na sanar dashi hakan, domin shi baiyi tunanin haka ba, aganinsa ma, abinda ya faru tsakaninsa da mahaifiyar sa ba komai bane. Namai faɗa kuma nace dole mu shiga ya bata haƙuri, haka kuma akayi, ko ba don komai ba, domin abin ya tsaya a haka. Ya ƴan'uwana matasa, kunji kaɗan daga abinda ke iya zuwa ya dawo dalilin saɓawa iyaye. Ahir ɗinku ku fita zanga-zanga, alhali iyayen ku sun hanaku.

    4. Zanga-zangar ba zatayi nasara ba saboda masu shirya ta da masu goyon bayan ta, sunci naman bayin Allah. Zagin malamai babban laifine, domin Allah da manzonsa ne sukayi umurni da a musu biyayya, a girmama su kuma a mutun ta su, toh duk wanda yaƙi bin wannan umurnin, kuma ya wuce gona da iri, har yaci namansu, ya zagesu, ya shiga hurumin su, toh wallahi ya shiga uku. Domin malamai sunce ita namar malami gubace, duk wanda yaci toh zaiga sakamakon aikin sa tun anan ba sai anje chan ba. Inada yaƙin in cewa, wallahi duk wanda ya zagi malamai kuma ya fita wannan zanga-zangar, toh bazaiga da kyau ba. Amma duk matashin da yake musun haka, toh ya jira ya gani. Wata rana a masallacin unguwar mu inda nake sallah, bayan anyi sallar Magriba, sai limami ya fara nasiha, daman baƙo ne, yana zuwa ne yin karatu a masallacin duk sati. A bayanan sa sai yayi gargaɗi akan kar wani matashi yace zai fita, domin babu amfani a cikin fitar, kuma akwai yiwuwar a samu aukuwar fitina a dalilin zanga-zangar. Kawai sai wasu marasa kunyan yara da sukayi sallah a wani zaure a bayan masallacin saboda cikan waje kuma ga ruwa, sukace "AI SAI KAZO KA HANA MU" irin wannan jara'a na waɗannan yara yayi muni, saboda kawai sunajin cewa su marasa kunya ne. Da na kalli yaran, nayi nazarin al'amarin daga baya, sai naga yara ne da basu jin maganan iyayensu ma balle na wani. Amma kuma nasan cewar, tabbas zasu gamu da gamonsu, muddin suka fita wannan zanga-zangar. Domin wallahi sai Allah Ya jarrabe su akan wannan rashin kunyar da sukayi. Toh ba su kaɗai ba, hakane zai faru ga duk wanda yayi makamancin wannan. Don haka, ina kiran sauran masu hankali a cikin wannan zanga-zangar da su kiyaye haɗa hanya da waɗanda suke cikin fushin Allah, domin duk abinda zai sami masu laifin, suma zai shafesu. Allah Ya sauwaƙe.

    5. Shin ko mun tuna abinda ya faru a ƙasashen Larabawa bayan zanga-zangar da sukayi wa shugabannin su? Mu ɗauki misalin Libya, sunyi zanga-zanga kyautatuwar rayuwarsu, amma yanzu haka baya sukaci, abinda suke samu da suka raina yasa suka fita zanga-zangar, sunbar samu. Kuma daman waɗanda suka shirya zanga-zangar daban, da manufar su, amma wasu suka shiga cikinsu da nufin hamɓarar da gwamnati, sunyi nasara, amma cigaba ce irin na mai tonon rijiya. Toh ya faru da yawa irin haka, don haka mu kula.

    6. Saboda duk al'amarin da yara suka farar dashi ana samun matsala da tasgaro a cikinsa, saboda su yara suna da gaugawa a al'amura. Saɓanin manya, dattawa waɗanda suke da haƙuri da bi a sannu, toh sukam, ba'a samun tasgaro a al'amuransu. Haka Assafady ya faɗa, kuma duk munsan hakane. Wannan zanga-zangar ma yara ne suka shirya ta, kuma gaugawa ce ta ɗebe su, don haka nasarar zanga-zangar take ƙasa take dabo.

    Toh idan ba za'ayi zanga-zanga ba, me za'ayi, yaya za'a samu biyan buƙatar? Toh sai muce tazo gidan sauƙi, domin akwai hanyoyi da yawa za'a bi a samu mafita akan wannan hali na ƙunci da ake ciki. Ga kaɗan daga abinda nake ganin za'ayi a samu sauyi;

    1. Mubi koyarwa da shiriyar malamai akan wannan abu, domin su haska mana abinda Allah Yakeso kuma ya yarda dashi, su koyar damu yadda ya kamata muyi yayin hali irin na ƙunci, rashin tabbas, jarrabawa kamar irin wannan. Kuma sunyi bayanai masu yawa akan haka, sunyi ta koyarwa, don haka a koma a saurara.

    2. Shin mun tuna cewar wata guda ko biyu da suka wuce mun shiga matsatsi a ƙasar nan, saboda rashin wutan lantarki? Wutan yayi tsada kuma yayi ƙaranci matuƙa da gaske. Ta yanda mukam a unguwar mu, wutan da muke samu a lokacin bai wuce awanni biyu ba a wuni! Har saida muka ce, hala bamuda wani tsari ne, wato 'band' kamar yadda suka rarraba masu shan wutan zuwa bands, Band A, Band B, Band C, da sauran su. Toh mukam saida mukace bamuda wani band, saboda kason da ake bamu yayi ƙaranci matuƙa. Ba irin wahalan da bamusha ba a lokacin, saboda hatta chajin kwamfuta sai nakai wajen chajin kuɗi, gashi a lokacin ina cikin tsananin buƙatar chajin saboda karatuka na a yanan gizo. Shin don Allah matasan, zanga-zanga muka yi matsalar ta gyaru? Amma yanzu Yaya labarin wutan lantarkin? A dai yankin da nake a Bauchi, mukan samu hasken wutan lantarki na tsawon awanni ashirin mafi ƙaranci a kullum. Saɓanin yadda muke samu kafin ma a samu wancan matsalar. Kafin wannan rashin wutan, awanni bai kai goma ba muke samu a kwana guda, amma yanzu ninkin wannan muke samu batareda wani zanga-zanga ba, muka samu wannan cigaban.

    3. Kafin matsalar hasken wutan lantarki, ai mun shiga matsalar kuɗi a hannu, wato 'cash'. Haka kawai aka sanya mutane a damuwa, mutum da kuɗinsa bai isa ya cire ba balle ya kashe, aka takura mutane matuƙar takurawa. Amma yau ina wannan wahalar take? Itama zanga-zanga muka yi ta kawu? Ya kamata mu rinƙa tuna irin haka. Akwai su da yawa. Shin mun tuna lokacin tashe-tashen hankulan Boko Haram, da irin tsoro da firgici da muka shiga, zaman ɗar-ɗar da jimami? Yaya akayi muka fita, zanga-zanga muka yi matsalar ta gyaru? Meyasa muke ganin dole sai zanga-zanga ne zai gyara wannan? Muyi tunani mana, ya ƴan'uwana matasa ƴan Najeriya.

    Amsoshin duk waɗancan tambayoyin shine, ba zanga-zanga mukayi ba, haƙuri mukayi muka koma ga Allah, sai Allah Ya taimake mu Yaji kukanmu Ya share mana hawaye Ya fitar damu daga waɗancan matsaloli. Toh a wannan karon ma, Allah Yana nan, kar mu gajiya da yin haƙuri da fawwala maSa al'amuran mu, tabbas Yana ganin bayinSa, Yasan halinda suke ciki.

    RUFEWA

    A ƙarshe, ina kira ga gwamnati da ta gyara salonta wajen kula da ƴan ƙasa da magance damuwoyinsu. Tabar yaudara da alƙawuran ƙarya don ta samu abinda take so, ta sani yaudara da ƙarya basa tasiri na har abada. Misali, gwamnatin tarayya ta sanar da sayar da shinkafa a Naira dubu arba'in (N40,000) buhu, kamar yadda ta taɓayi a baya na wani shinkafa da akace Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa ce take sayarwa, wato Custom. Amma haka abun ya zama labarin ƙanzon kurege! Toh wannan ɗin ma, akwai yiwuwar haka. Batun ware biliyan ɗari da goma (N110 billion) don shirin bada rance wa matasa, wato shirin NYIF wanda ministan matasa da wasanni ta sanar da ƙaddamarwa, duk gwamnati ta tabbatar ba yaudara bane kamar na kyauta dubu hamsin da rancen miliyan guda. Domin a wajen ƴan ƙasa, an daɗe ana ruwa ƙasa tana shanyewa. Ina fatan wannan gargaɗi zai shiga kunnuwar da ya kamata.

    Sa'adu Zungur dai ya ce;

    Mu dai burinmu faɗa muku
    Ko ku karɓa ko ku yi dariya, 

    Dariyar ku tazam kuka gaba
    Da nadamar maiƙin gaskiya.

    Zanga-Zanga

    Yusuf Abdullahi Umar
    (yusufaumar97@gmail.com)
    Bauchi, Najeriya.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.