𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam barka da war haka da fatan Allah ya sada mu da alkhairi. Tambayata anan itace budurwa ce akayi mata aure sai ya kasance a saduwan ta nafarko da mijin bai jita kamar yanda ake bada labarin 'ya budurwa take ba sai yace mata shifa yanda yake tunani bahaka yasamuba don Allah ta faɗa masa gaskiya in ta taɓa yin zina kafin Auren su don shikam bai taɓa yi ba sai ta cemasa yanzu meza ta masa don ya yarda cewa bata taɓa zina ba sai yace ta rantse masa da Alqurani kafin ya yarda shikennan sai tayi Alwala ta dau alqurani ta rike ta ce masa wallahi tallahi narantse da Alquani ban taɓa zina ba inkuma na taɓa nayi qarya Allah yatozarta ta tayi masa irin wannan rantsuwar ya kai sau shida alokaci daban daban haka shima yayi mata irin wannan rantsuwar Duk lokaci da tamasa. tambayar malam sune:-
1. inkarya take ya halasta ayi irin wannan
rantsuwar don kare mutunci?
2. In bai halastaba tozarta na iya afkawa Wanda
yayi karya daga cikin su?
Kuma agarin da suke an yarda cewar duk wanda yayi
irin wannan rantsuwar akan karya baya gamawa lafiya
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Da farko dai shi wannan mijin, tabbas ya zalunceta
bisa wannan tuhumar da yake yi mata. Domin kowacce mace tana da irin halittar
da Allah yayi mata. Ba dole ne idan anzo saduwar farko sai an tarar da murfin
budurci ba. Sannan akwai dalilan dake janyo fashewar murfin budurci Misali
kamar
1. Ɗaukar kaya mai nauyi.
2. Faɗuwa daga wani tsauni ko bishiya.
3. Wasu daga cikin wasannin motsa jiki.
4. Daɗewar shekaru kafin aure.
Za ta yiwu ita wannan matar ta haɗu da wani daga cikin dalilan nan.
Don haka ya zalunceta ta fuskar tuhumar da yayi mata, da kuma rantsuwar
da ya sanyata tayi masa.
Shi Alqur'ani zancen Allah ne. Zance kuma yana
daga cikin siffofin Allah. Kuma ya halasta mutum yayi rantsuwa da sunayen Allah
ko siffofinsa Maɗaukaka.
Ɗaukar Alqur'ani ko rikeshi yayin yin rantsuwa, wannan ba sharaɗi bane game da sahihancin rantsuwar. Ko da baki mutum ya furta yace
"NA RANTSE DA ALQUR'ANI" Shikenan rantsuwa ta afku. Kuma duk wanda
yayi rantsuwar fajirci (wato rantsuwar Qarya) to hakika ya aikata kaba'ira.
Wajibi ne ya tuba domin samun sauki awajen Allah. Manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallam ya lissafa rantsuwar Qarya cewa tana kwashe albarkar rayuwa,
kuma tana talauta mai yinta.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.