Mun Kai Shekara Daya Da Rabi Mijina Bai Kusance Ni Ba

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum' wa rahamatullahi wa barakatuhu. Malam kimanin shekara goma kenan da yin auranmu da mijina, Babu abinda ba ya yi mun kamar ci da sha, sutura, magani, da Ihsani idan yana dashi. Amma babbar matsalar shine ayanzu haka mun kai shekara daya da rabi mijina be kusanceni ba. Kuma na tambayeshi dalili yace babu komai. na sanar da mahaifinshi yayi mishi magana amma be chanza ba. na cigaba da sanar dashi cewa kar yayi sanadiyar jefani cikin hallaka domin yana cutar dani amma yaki ya saurareni. Sai na sanar da iyayena amma har yanzu banga abinda ya chanza ba. Tunanina kawai ni a yanzu in fita in bar masa gidansa tunda har ya iya cewa bashi da buqatata, kuma Malam dan Allah shawara nake nema da fahimtar dani abinda ya shege min duhu. Allah ya saka maka da alkharan duniya da lahira na gode.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    Shi hakkin jima'i, hakki ne wanda yake rataye a wuyan dukkan ma'auratan. Kamar yadda ya zama wajibi mace ta amsa kiran mijinta duk lokacin da ya bukaceta, to shima wajibi ne akansa ya biya mata bukatarta bisa gwargwadon ikonsa da kuma yanayin bukatarta.

    Bisa wannan dalilin ne ma wasu daga cikin Malamai suke ganin cewa muhimmancin jima'i a aure, ya fi girma fiye da mihimmancin ciyar da ita matar.

    Allah (SWT) ya wajabta kyautatawa atsakanin Ma'aurata. A inda Yace

    ...وَعَاشِرُوهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ...

     "KU ZAUNA DASU TARE DA KTAUTATAWA". (Suratun Nisa'i Ayah ta 19).

    Acikin Suratul Baqarah ayah ta 228 Allah Yace

    ...وَلَهُنَّ مِثْلُ الَّذِي عَلَيْهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ...

     "SU MA (MATA) SUNA DA HAKKI (AKAN MAZAJENSU) KAMAR IRIN WANDA (MAZAJEN)  SUKE DASHI AKANSU".

    Wato yadda ya zama wajibi ne mace ta ba wa mijinta hakkinsa na kwanciyar aure, to shima wajibi ne akansa ya bata nata hakkin na kwanciyar aure domin kiyaye mata mutuncinta da kange mata sha'awarta da killaceta daga sharrin afkawa cikin alfasha.

    Tunda dai kin kai Qararsa wajen mahaifinsa ba'a samu chanji ba, kuma kin sanar da naki iyayen duk dai ba'a samu mafita ba, abinda ya kamata yanzu kuma kiyi shine

    1. Ki sameshi ku zauna kiyi masa magana tare da tausasawa ki tambayeshi ko yana ɗauke da wata larura wacce ta haddasa masa raunin mazakuta ko ɗaukewar sha'awa. Misali kamar ciwon sugar (Diabates) ko hawan jini (hyper tension). Ko wani ciwon na daban. Idan larura gareshi, to kiyi hakuri ki kwantar masa da hankali, kuma ki taimaka masa wajen neman magani a wuraren da suka kamata a nema. Amma idan haka kawai ya tsiri wannan halin, to sai ki ba wa iyayenki shawarar su sake dawowa su sameshi tare da waliyyansa,  a zauna domin neman mafita. Su shawarta atsakaninsu su samar muku da mafita.

    Allah ya faɗa acikin Alqur'ani : "IDAN KUKA TSORACI CHUTARWA ATSAKANINSU (SU MA'AURATAN) TO KU KIRA MASU YANKE HUKUNCI DAGA BANGARENSHI, DA KUMA MASU YANKE HUKUNCI DAGA BANGARENTA.  IDAN SUKA NUFI YIN SULHU, TO ALLAG ZAI DAIDAITA TSAKANINSU".

    2. Idan wasu halaye kike nuna masa marasa daɗi, to kiji tsoron Allah ki dena. Kiyi masa alkawarin kin dena domin ku daidaita tsakaninku.

    3. Idan kuma duk an bi waɗannan matakan amma ba'a samu dacewa ba, to mataki na gaba shine ki sanar da alqali, ya kirashi yayi masa magana. Idan kuma bai gyara ba, to shi alqalin yana da damar raba aurenku.

    Kiyi hakuri kibi abubuwan ahankali, kuma kiji tsoron Allah kada wannan kauracewar tashi ta sanyaki kiji sha'awar aikata alfasha.

    WALLAHU A'ALAM. 

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.