Sanarwa Ta Musamman

Assalamu alaikum, Warahmatullahi, Wabarakatuh

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (Subhanahu wata'ala), tsira da amincin Allah su qara tabbata ga Manzon tsira, Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) da ahlayen sa da sahabban sa da musulman da suka bi tafarkin gaskiya (tafarkin Salaf wato magabata na qwarai)

Muna amfani da wannan damar domin isar da gaisuwa ta musamman ga masu bibiyar zaurenmu na TAMBAYA DA AMSA (Mai dauke da Group na 1 har zuwa Group na 24. Wanda a kowanne Group guda 1 da akwai mutane kusan ko kuma sama da 1,000. Jimillar mutane wajen 24,000 wanda hakan ne yake sa bama iya amsawa kowa tambayar sa akan lokacin da mutum yake son amsar)

Ga kuma Public Channel dinmu mai dauke da mutane sama da 5,000. Banda kuma dubunnan mabiya daga Facebook da kuma daruruwa daga manhajar Telegram. Dalilin zayyano wadannan alqaluma yana da alaqa da rarrashin wadanda suke tunanin kamar muna sane ne bama basu amsa da wuri. Muna roqon za'a karbi uzurinmu. Sannan kuma zamu dage mu ga mun gamsar da mai tambaya kamar yanda aka saba da hujjoji daga Qur'ani, Hadisi, Ijma'i da Qiyasi

Bayan haka, komai yana buqatar ci gaba. Bayan tattaunawa da kuma shawarwari mun fitar da wani tsari (Program) na musamman da zai kara inganta tare da kwadaitar da yan uwa da abokan arziqi da suke cikin wannan Group mai albarka ta hanyar TAMBAYA kai tsaye da ta shafi AQIDA, IMANI da IBADAH. Wanda kuma muna albishir din sanar daku cewar duk wanda ya amsa tambaya a daidai to da akwai kyauta/kyaututtuka na musamman da suka hada da

1️) Kujerar MAKKAH domin gudanar da HAJJI/UMRAH

2️) Yan kudaden kashewa wanda za'ayi transfer ga BANK ACCOUNT din wanda yayi nasarar amsa TAMBAYA

3️) Abubuwan AMFANI na yau da gobe (Ya danganta da abinda aka turo)

Saidai yakamata ku sani cewar Group dinmu ba a karkashin wata kungiya yake ba duk da cewar da akwai Non Governmental Organizations a ciki haka kuma ba'a karkashin gwamnati yake ba duk da cewar akwai ma'aikatan gwamnatin a cikinsa. Group ne mai dauke da mutanen da baka taba tunanin kana tare dasu a ciki ba, wadanda suka hada da: Yan siyasa, ma'aikatan lafiya, engineers, jami'an tsaro, manoma, yan kasuwa da sauransu

Kenan zamu hada kanmu ne baki daya mu zamo tsintsiya mai madauri guda daya don ganin mun kawo sauyi ga rayuwar wasu daga cikinmu, misali: Likitocin Group din zasu iya bada gudunmawar abinda ya shafi magani don a bayar da shi kyauta ga wanda ya amsa wata Tambayar ko yayi amfani da maganin ko kuma shima ya bayar ga wani mabuqaci wanda ya sani. Dan Siyasa ko Dan Kasuwa zai iya bada gudunmawar Kujerar MAKKAH ga duk wanda ya amsa Tambaya ta hakan sai ya samu ladan wanda ya bawa kujerar. Engineers zasu iya bada gudunmawar kafa rijiyar burtsatse ko da a kungiyance ne, sun samu ladan shayar da al'ummar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam). Manoma zasu iya bada gudunmawar hatsi ga wanda ya amsa Tambaya a kalla Manomin zai samu ladan ciyarwa ga Dan uwansa da suka hadu a wannan Group din haka shima jami'in tsaro (Public Servant) zai iya bada gudunmawarsa gwargwadon ikonsa

To ammanfa wadannan tsare-tsaren duk zasu tashi a fanko ne indai har ba mu yi su da ikhlasi (Don Allah) ba saboda kishiyar ikhlasi shine Riya (Yi don wani ba don Allah ba). Allah ne kadai yasan mutane nawa ne zasu amfana da wannan sabon Program din kuma idan munyi don Allah to ranar Lahira zamu dara. Mu kuma da muka tsara indai muka ci amana to sai mun fi kowa shan wahala a ranar Lahira domin kuwa duk abinda aka samu sai munyi bayanin sa a gaban Allah Azzawajallah. Sai ku tayamu addu'ar Allah yabamu ikon sauke nauyin kamar yanda daga ni (Usmannoor_Assalafy) har shi (Malam Khamis Bin Yusuf) zamu bawa Allah zabi akan al'amarin ta hanyar yin addu'ar Istikhara

Bamu fitar da lokacin da zamu fara Program din ba saboda wasu shirye - shirye da bamu kammala ba amman zamu dinga gabatarwa duk ranar Juma'ah da daddare, ta hanyar kiranmu kai tsaye a waya, in sha Allaah. Tambayar da zamuyi za ta zamo a cikin tambayoyin da aka amsa ne a tsawon kowanne sati

Sannan kuma a kiyaye da wadanda zasu tambayeku ta Private domin kuwa akwai wadanda shaidan yayi nasara akansu da suke damfarar wasu dake wannan group din

DALILIN QIRQIRO WANNAN PROGRAM

1️) Sadaqatul Jariya {Ko ka rasu zaka ci gaba da samun ladan abinda ka bayar don amfanuwar wasu. Sannan kuma zaka iya janyo wasu don su ma su bada tasu gudunmawar}

2️) Don karfafa gwiwa ga masu bincike a cikin addininmu na Musulunci {Domin kuwa wasu suna samun kudin haram a sharholiyarsu ta duniya alhalin a tafarkin taimako ya kamata su gina lahirarsu}

3️) Don toshe budaddiyar kofar yan damfara {A maimakon wani ya damfare ka a group, gara ka tura don a gudanar da wannan program a qalla kasan me za'ayi da gudunmawarka}

Muma kuma kuma (Ni da Malam Khamis) zamu dinga bada tamu gudunmawar financially don hadaka a cikin ladan. Sannan kafin mu fara muna buqatar addu'arku da kuma shawarwarinku akan yanda za'a gudanar da wannan PROGRAM

Idan kuma za'a samu wanda zai iya daukar nauyin gudanar da gudunmawar fisabilillah shi kadai to kofa a bude take

MENE NE RAAYINKU GAME DA WANNAN PROGRAM

✒️Sanarwa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy (admin 2)

Da sahalewar

Malam Khamis Bin Yusuf (admin 1 & Group founder: TAMBAYA DA AMSA)

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments