Shan Maganin Hana Bacci Saboda Sallar Dare

    TAMBAYA (137)

    Assalamualaikum, ya malan dafatan kana ciki koshin lfy, tambayar,  yahalasta mutum yanaso yayi salar tsakar dare zai iya shan magani Dan Kar yayi bachi

    AMSA

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

    Yawan shan magani yana kawo side effects wato matsaloli na musamman don haka ni a shawarata gani nake kamata yayi k dinga kwanatawa da wuri ka rage amfani da wayanki har zuwa cikin dare da kake yi

    Idan ka kwanta kamar karfe 9 zuwa 10 na dare zaka samu wadataccen bacci na tsawon awanni 7

    Kaga zaka farka wajen karfe 4 kenan

    Sai ka tashi a tsanake kayi ibadarka gwargwadon iko

    Wallahu ta'ala a'alam

     Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.