Shin Akwai Wani Alama Da Mace Za Ta Gane Maniyyi Ya Shiga Gabanta Yayin Saduwa

    TAMBAYA (138)

    Assalamu alaikum. Malam Ina wuni, ina gajiya, ya aiki, ya iyalai

    So, malam nidai tambaya nakeyi, Allah yasa an san amsa ta, yau sati na daya da yin aure kenan, nidai muna jima'i da miji na, malam, shi yana gamsuwa, nice dai bansan ya gamsuwar take ba malam, ko dan ina farin shiga. Sannan kuma malam, idan har sperm ya shiga cikin jikin mace, akwai wani sign da za ta ji ne alama na maniyyi ya shigeta ko ko ba wani sign. Allah ya karawa malam lafiya. Nagode sosai

    ✍️AMSA A TAQAICE

    Waalaiki Salam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

    (Dadin saduwa zai iya mantar dake ko maniyyin ya shiga ko bai shiga ba duk da dai yana wahala ace mace ta manta amman shi namijin yasani cewar ya shiga ko akasin haka. To kinga kenan ba abin damuwa bane idan kinji alamun sperm din nashi bai shige gabanki yanda kike tunani ba musamman ma la'akari da ke sabon shiga ce. Kawaidai kada ku manta da addu'ar saduwa kafin ku fara)

    Bismillaahir Rahmaanir Raheem

    Tabbas ana samun irin haka ga sabbin ma'aurata, musamman ga mace

    Amman yau da gobe za tasa ki ji kin saba, in sha Allahu

    Shi sperm ai yana shiga mahaifa ne kai tsaye, kuma ai zaki ji alamun shigarsa da zarar mijinnaki ya kawo (releasing)

    Idan kuma ba ki ji shigar sa din ba, kada ki damu da wai dole ne sai kin ji shigar sperm din ba, domin kuwa kowanne release daya tak da akwai halittu a cikin maniyyin masu rai at least ko kuma sama da miliyan ashirin (20,000,000) wanda a cikinsu guda daya ne tak yake karasawa mahaifa a raye duk sauran mutuwa sukeyi silar attack (feshin) chemicals da suke samu daga white blood cells

    Guda daya dinnan ne yake haduwa da egg cell (maniyyin mace) sai a samu zygote bayan fertilization ya faru, bayan kuma kwanaki 40 sai ya koma jini, 80 days ya zama tsoka sannan a 120 days ya zama qashi daganan sai a busa masa rai

    To kinga kenan ba abin damuwa bane idan kinji alamun sperm din nashi bai shige gabanki yanda kike tunani ba

    Sannan kuma matuqar ba ta baya (dubura) mijinki ya sadu dake ba to ba laifi yazo miki duk ta yanda yaso saboda fadin Allah (Subhanahu wata'ala)

    ( نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ لَّكُمْ فَأْتُوا حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ ۖ

    البقرة (223) Al-Baqara

    Mãtanku gõnaki ne a gare ku, sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so

    Kawaidai shawarar da zan baki anan itace kada ku manta da addu'ar da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya koyar kafin saduwa aure. Itace

    بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.

    "Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana"

    Ma'ana

    "Da sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi"

    Wallahu ta'ala a'alam

     Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.