Ticker

    Loading......

Shin Ruwan Nonon Mace Najasa Ce?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam inada tambaya Ance in nono ya taɓa Kaya, kayan bazaiyi sallah ba, to macenda take shayarwa Kuma ruwan nono yana zuba mata dayawa har Yana Ɓata mata kaya. Shin duk lokacinda zatayi sallah zata wanke jikinta ta canja Kaya? Koko yaya zatayi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To baiwar Allah shi ɗan Adam babu yadda za'ayi ace da najasa ake shayar dashi kuma nasan babu wanda zai yadda cewa da janasa ake shayar da yaro to yanzu don Allah ta yaya za'a ce muku shi ruwan nonon najasa ne?

Sabida haka shi nono Abinci ne halattacce Da Allah maɗaukakin sarki Ya samar dashi daga jikin mace domin shayar da ɗanta, kunga kuma tayaya za'ace idan abinci ya taɓa tufafi ba zai yi sallah ba?

Sabida haka waccan maganar kawai karyace domin bata da asali Babu wani nassi ingantacce da yace matar da take shayarwa idan nonon ya zuba a tufafinta, tufafin ba zai yi sallah ba Wannan kawai tatsuniyace. kai koda tunbuɗin da yara ke yi ba najasa bane zubar sa a tufafi baya hana sallah balle kuma shi ruwan nonon kansa. Sabida haka dukkansu tsarkakakku ne basa hana sallah kuma ko da ya zuba a tufafi babu laifi tayi sallarta da kayan idan kuma taso sai ta wanke Amma dai wankewar ba dole bane.

Amma su waɗanda suka ce najasane to kuce dasu su zo muku da hujja su ɗin idan sun kasance suna da gaskiya

WALLAHU A'ALAMU

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments