Ɗanmalikin Gabake, Ɗanmalikin Gidan Goga da Ɗanmalikin Janbaƙo duka Dagatai ne a wancan lokaci, watau kafin samuwar Jihar Zamfara a watan Oktoban 1996.
Gabake a Gundumar Ƙaura Namoda, Gidan Goga da Janbaƙo a Gundumar Maradun a Tsohuwar Jihar Sakkwato.
Laƙabin Sarautar Ɗanmaliki nada alaƙa da Cibiyar Daular
Usmaniya, Sakkwato inda ake hasashen daga nan ne ta samo asali tun bayan
tabbatarwa Malam Doshiro Bn Abdullahi Mujakka(Fulani Bororo/Bororoji ne)
Sarautar Galadiman Sakkwato bayan kafa Daula.
Galadima ne a Daular Gobir, ya yi mubayi'a ga mujahidai.
Bayan an tabbatar masa da wannan sarauta a Cibiyar Daular Usmaniya sai ya naɗa ɗansa a matsayin mataimakinsa da laƙabin
"Ɗanmaliki".
Ya zuwa yanzu zuriyarsa ke riƙe da wannan sarauta ta Ɗanmaliki
a Masarautar Sakkwato. Marigayi Alhaji Zubairu Tela, wanda shahararren Ɗan
Kwangila kuma Ɗan Siyasa ne ya taɓa
riƙe
wannan sarauta ta Ɗanmalikin Sakkwato.
A gefe ɗaya
kuma Gabake(a Masarautar Ƙaura Namoda ta yanzu) wadda ta samu ne a cikin ƙarni
na 18 ta hanyar ƙirƙira daga wasu jinsin Fulani da ake kira "Alwanko"
dake da tushen su a wani wuri a cikin Jamhuriyar Nijar ta yanzu, laƙabin
sarautarsu Ɗanmaliki
duk da yake babu takamaiman dalili da lokacin da suka fara amfani da wannan laƙabi.
Samuwar Marigayi Alhaji Mu'azu a matsayin Ɗanmalikin
Gabake wanda ya yi sarauta daga cikin 1940s zuwa rasuwarsa a shekarar 1989 ya sanya
wannan laƙabi
na Ɗanmaliki
ya yi amo sosai a mafi yawan masarautun Arewa.
Saboda shahararsa masarautu da dama sun ɗauki wannan laƙabin
sun ayyana sa a matsayin sarauta. Shi dai ne wanda Makaɗa da Mawaƙa suka yiwa Waƙoƙi da dama duk da yake
wasu Waƙoƙin
basu yi fice ba kamar yadda ta Makaɗa
Musa Ɗanƙwairo
Maradun mai amshi "Jikan Musa Ɗanmaliki, gamda'aren Amadu(Baura jikan
Baura, Mu'azu Allah sa ka gama lahiya) ta yi amo ba.
Har ila yau akwai Ɗanmalikin Achida wanda Uban Ƙasa/Hakimi
ne a Gundumar Achida, Masarautar Sakkwato da ya fito daga tsatson Muɗagel ɗan Modibbo Ummaru
Mu'alkammu (suke sarautar Gundumar Mu'alkammu da kuma Magajin Rafin Sakkwato).
Modibbo Ummaru Mu'alkammu aminin Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ne da ya na cikin
mutanen da suka fara yi masa mubayi'a a matsayin Mujaddadi a Tafkin Kwatto
gabanin fara Jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya a shekarar
1804.
Akwai kuma Ɗanmalikin Katsaura a Masarautar Ƙaura
Namoda duk da yake babu takamaiman lokacin da suka fara amfani da wannan laƙabi a
matsayin Dagaci.
Gidan Goga da Janbaƙo a halin yanzu hedikwatocin Gunduma ne a
Masarautar Maradun dake Jihar Zamfara. Ana iya alaƙanta samuwar laƙabin
Sarautarsu ta Ɗanmaliki da samuwar ta a Cibiyar Daular Usmaniya idan aka yi
la'akari da zamowar Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi
ɗan Sarkin Musulmi
Muhammadu Bello ɗan
Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi a matsayin Sarki a
Maradun a cikin 1870. Allahu Wa'alam!!!
Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara
08149388452, 08027484815
birninbagaji4040@gmail.com
Alhamis, 04 /07 /2024
Ƙarfe 8:03 na Dare
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.