Tazara Da Mutum Zai Iya Wucewa Ta Gaban Mai Sallah

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. Malam akwai iyaka game da tazara ta yadda mutum zai iya wuce ta gaban mai sallah ? . Jazaakallahu khairaa.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Walaikumus salamam Warahmatalahi wabarkatahu

    Sanya Sutura ita ce wani abu da mai sallah zai sanya a gaban shi, tsakaninsa da wanda zai wuce ta gaban shi.

    Sanya Sitira wajibi ne, saboda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi umarni da sanya sitira ga liman da wanda yake shi kaɗai, ya Kwaɗaitar akan yin hakan, don haka ya kamata musulmi ya sanya sitira a gabansa yayin da zai yi sallah, ya hana wanda zai wuce tsakaninsa da tsakanin sitirarsa, saboda faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Kada ka yi sallah sai da sitira, kada ka bar wani ya wuce ta gabanka, idan ya qiya ka hana shi”[Ibnu Khuzaima ne ya rawaito shi]

    Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Idan ɗayanku ya tashi yana sallah, idan a gabansa akwai (sitira) kwatankwacin sandar dake qarshen sirdin raqumi to tana yi masa sitira (ta kare shi). Idan kuwa babu kwatankwacin sardar dake qarshen sirdin raqumi a gabansa, to (wucewar) jaki da mace da baqin kare suna yanke masa sallah “Yace, nace,” Ya Abu Zarrin! Me yasa kare baqi (kawai) daga cikin karnuka ruwan dorawa? Sai ya ce, “Ya ɗan ɗan'uwana, na tambayi Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) kamar yadda ka tambaye ni, sai ya ce min, “Baqin kare shaiɗan ne”[Muslim ne ya rawaito shi].

    Wucewa ta gaban mai sallah baya halatta, yana ma cikin manya-manyan zunubai, saboda faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Da wanda yake wuce wa ta gaban mai sallah ya san abin da yake kansa (na laifi) da ya tsaya arba’in shi ya fi masa alheri a kan ya wuce ta gaban (mai sallah). Abun Nadri “mai riwayar hadisin” ya ce, : “Ban Sani ba, kwana arba’in ya ce, ko wata ko shekara?” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

    (Babu laifi) idan wucewar ta bayan sitirarsa ce, ko kuma ya wuce nesa da shi, daga bayan wurin da yake sujjada idan shi mai sallar bai sanya sitira ba.

    Dole ne akan mai sallah ya hana wanda zai wuce ta gabansa.

    An karbo daga Abu Sa’id – Allah ya yarda da shi – ya ce, na ji Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana cewa, “Idan ɗayanku yana sallah da wani abu da ya kare shi daga mutane (Sitira), sai wani ya yi nufin ya wuce ta gabansa, to ya tunkuɗe shi, idan ya qiya to ya yaqe shi, domin shi Shaiɗan ne”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

    Tazarar da take tsakanin mai sallah da sitira ana qaddara ta da kwatankwacin wurin da akuya za ta iya ficewa, saboda hadisin Sahli – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Tsakanin wurin sallar Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) da sitirarsa, akwai kwatankwacin wurin da akuya za ta iya wuce wa”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.