Wakar Zanga-Zanga 2024 Ta Prof. Aliyu Muhammad Bunza

Waƙar Zanga-Zanga 2024

Ta

Prof. Aliyu Muhammad Bunza

Rerewar Sha'iri Bello Shehu Alkanci Talatar Mafara

Matsalolin da suka haɗa da na tsaro da talauci da ƙuncin rayuwa sun yi matuƙar tsarami a Nijeriya ya zuwa shekarar 2024. Wannan ya kai ga kiraye-kiraye da dama musamman a kan kafafen sadar da zumunta a kan a fito zanga-zangar lumana a faɗin ƙasa baki ɗaya. Malaman addinai da masana siyasa da kuma 'yan siyasa sun yi ta tofa albarkacin bakainsu game da wannan lamari. A cikin watan Yulin 2024, shi ma Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da ke Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato ya tsara waƙa game da lamarin. Sha'iri Bello Shehu Alkanci Talatar Mafara ne ya rera a madadinsa.

Haƙƙin Mallaka:
* Prof. Aliyu Muhammad Bunza
* Mal. Bello Shehu Alkanci

Post a Comment

0 Comments