Ya Daina Sallah Saboda Zina Da Yake Yi

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Meye hukuncin mazinaci wanda baya sallah sabida zina da yake yi wai Allah baya son sallarsa, tunda ya yi zina kuma yana Sallah juma'a?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    To farko dai ka sani sallah ita ce babban ƙinshin da ke riƙe da Addini domin ita ce abu mafi girma, kuma ita ce take riƙe da Addinin bayan kalmar shahada. Kuma rashin yin sallar na daga cikin manyan hanyoyin da ke sawa mutum ya afka a cikin manyan laifukan ire-iren su: shan giya, sata, da ita zinar. Dalilin faɗin Allah maɗaukakin sarki

    ۖ إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَىٰ عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنْكَرِ ۗ وَلَذِكْرُ اللَّهِ أَكْبَرُ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا تَصْنَعُونَ

    Lalle salla tanã hanãwa daga alfãsha da abin ƙyãma, kuma lalle ambaton Allah ya fi girma, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke aikatãwa. (Suratul Ankabut Aya ta 45)

    Abu ba biyu ita zina bata fitar da mutum daga musunci, ballantana har ta hana a ƙarɓi sallarsa. Sai dai aikata zina babban laifi ne, kuma Alfasha ce kamar yadda Allah ya ambata a cikin littafinSa mai tsarki

    وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا ٢٣۝

    Kuma kar ku kusanci zina. Haƙiƙa! Ita alfasha ce, kuma mummunar hanya ce. (Suratul Israa’i Aya ta 32)

    Abu na uku duk wanda ya faɗa acikin irin wannan ya sani barin yin sallar ka iya fitar da shi daga musunci, kuma yin sallar juma'a kaɗai ba tare da yana yin sauran salloli ba, ba zai iya hana shi haɗu da azabar Allah ba, matuƙar bai tuba ba ya har ya mutu. Saboda da Allah maɗaukakin sarki ya iyawa waɗanda suke yin wasa da sallah alƙawarin azaba a cikin suratul Ma'un

    فَوَيْلٌ لِلْمُصَلِّينَ ٤۝ الَّذِينَ هُمْ عَنْ صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ ٥۝

    To, azaba yã tabbata ga masallata. Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu. (Sūratul má'un Aya ta 4-5)

    Kuma Aranar ƙiyama idan an tambayi ƴan wuta me ya shigar da su a cikin wuta zasu ce ne rashin yin sallar. Kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa a cikin littafinSa mai tsarki

    مَا سَلَكَكُمْ فِي سَقَرَ ٢٤۝ قَالُوا لَمْ نَكُ مِنَ الْمُصَلِّينَ ٣٤۝

    (Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin wutar Saƙar?" Suka ce: "mun kasance Bama yin sallah" (Suratul mudasirb Aya ta 42-43)

    Haka kuma ya tabbata a cikin hadisi, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: Tsakanin mutum da shirka da kafirci shi ne barin sallah.

    Allah maɗaukakin sarki Yace

    قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ ٣٥۝

    Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." (Suratul zumar:l Aya ta 53)

    Ibnu kasir rahimahullah yace: Wannan aya tana kirane ga dukkan masu saɓo harda kafirai su tuba su koma zuwa ga Allah, tana kuma bada labarin Allah yana gafarta zunubai baki ɗaya ga duk wanda ya tuba yadawo daga aikata laifukan, komai irin yawansu da girmansu koda sunkai yawan kumfar kogi, matukar anyi tuba nagaskiya Allah yana gafarta su.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.