Yanda Ake Yin Wankan Janaba A Bisa Koyarwar Annabi (S.A.W)

    TAMBAYA

    Assalamu Alaikum

    Malam dan Allah ni budurwa ce ban dade da fara jinin haila ba

    Malam dan Allah ina so A koya min yadda ake yin Wankan janaba

    AMSA

    DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN QAI SALATI DA AMINCI SU QARA TABBATA SUGABAN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W).

    allah madaukakin sarki ya wajabta yin wankan janaba acikin alqur,ani mai girma da daukaka kuma ya gaya mana wani da ga cikin dalilan da suke sawa ayi wankan, a inda yake cewa

    يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَقْرَبُوا الصَّلَاةَ وَأَنْتُمْ سُكَارَىٰ حَتَّىٰ تَعْلَمُوا مَا تَقُولُونَ وَلَا جُنُبًا إِلَّا عَابِرِي سَبِيلٍ حَتَّىٰ تَغْتَسِلُوا ۚ وَإِنْ كُنْتُمْ مَرْضَىٰ أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوْ جَاءَ أَحَدٌ مِنْكُمْ مِنَ الْغَائِطِ أَوْ لَامَسْتُمُ النِّسَاءَ فَلَمْ تَجِدُوا مَاءً فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا طَيِّبًا فَامْسَحُوا بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَفُوًّا غَفُورًا

    (النّساء 43:4)

    Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku kusanci salla alhalin kuna maye har sai kunsan abin da kuke fada, haka mai janaba, sai dai in masu ketara hanya ne, har sai kun yi Wanka, idan kuma kun kasance marasa lafiya ko a halin tafiya, ko daya daga cikin ku ya dawo daga bahaya, ko kuma kuka sadu da mata kuma ba ku sami ruwa ba, to sai ku nufi doron kasa mai tsarki ku yi taimama, sai ku shafi fiskokin ku da hannayanku. Haqiqa allah ya kasance mai afuwa ne, mai gafara. [ suratun-nisa,i aya ta 43]

    Da kuma fadin sa allah madaukakin sarki

    يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا قُمْتُمْ إِلَى الصَّلَاةِ فَاغْسِلُوا وُجُوهَكُمْ وَأَيْدِيَكُمْ إِلَى الْمَرَافِقِ وَامْسَحُوا بِرُءُوسِكُمْ وَأَرْجُلَكُمْ إِلَى الْكَعْبَيْنِ ۚ وَإِنْ كُنْتُمْ جُنُبًا فَاطَّهَّرُوا ۚ وَإِنْ كُنْتُمْ مَرْضَىٰ أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوْ جَاءَ أَحَدٌ مِنْكُمْ مِنَ الْغَائِطِ أَوْ لَامَسْتُمُ النِّسَاءَ فَلَمْ تَجِدُوا مَاءً فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا طَيِّبًا فَامْسَحُوا بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُمْ مِنْهُ ۚ مَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيَجْعَلَ عَلَيْكُمْ مِنْ حَرَجٍ وَلَٰكِنْ يُرِيدُ لِيُطَهِّرَكُمْ وَلِيُتِمَّ نِعْمَتَهُ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

    (المائدة 6:5)

    Ya ku wadan da suka yi imani, idan ku ka tashi za ku yi salla, to ku wanke fiskokinku da hannayanku zuwa gwiwoyinsu, kuma ku wanke kafafunku zuwa idon sawu. Kuma idan kun kasance masu jana ba, to sai ku tsarkaka. Idan kun kasance marasa lafiya, ko a halin tafiya, ko daya daga cikin ku ya dawo daga bayan gari, ko kuka sadu da mata, kuma sai ba ku sami ruwa ba, to sai ku yi taimama a doron kasa mai tsarki, ku shafi fuskokinku da hannayanku daga shi. Allah baya na nupin ya sanya kunci a tare da ku ba ne, a'a, yana nufi ne ya tsarkakeku, kuma ya cika ni'imarsa a gare ku, don kuyi godiya. [sutul-ma'ida aya ta 6]

    ABUBUWAN DA SUKE WAJABTA YIN WANKAN JANABA GUDA BIYAR NE :

    1=futar mani daga mafutar sa da sha'awa da fita da qarfi, daga na miji ko maci( afarke ko a bacci amma in afarke ne da sharadin an samu jin dadi kapin fitar sa amma idan a bacci ne to da zaran an farka aka ganshi to wanka ya waja ba, amma da mutum ya yi mafarki yana tarawa da mace kuma da ya farka bai ga komai ya futa daga jikin sa ba to babu wanka akan sa. )

    2= haduwar kaciya biyu(ko da mani bai futa ba dazaran an samu haduwar su to wanka ya wajaba)

    3=almautu, ya wajaba a yiwa mamaci wanka.

    4=mai jinin haila: (wajibine ga mace bayan jinin haila ya yanke mata tayi wanka).

    5=jinin nifasi (wato jinin haiwuwa) shi ma idan ya yanke mata wajibine ta yi wanka.

    ABUBUWAN DA AKA SO AYI WANKA SABODA SU

    1=musuluntar kafiri (idan  kafiri ya musulunta to wanka ya wajaba agare shi a wajan mazahabar hanabila da malikiyya saboda hadisin qaisu dan asim: haqqi shi da ya musulunta annabi (s.a.w) ya umarce shi da yayi wanka da ruwa da bagaruwa. [malamai biyar ne suka rawaitu shi banda bn majah. kuma imam albani ya ingan ta shi a cikin sahihit-tirmizii 605]. Amma mafi yawan malamai sun tafi akan mustahabbin sa (wato an so wanda ya shiga musulunci ya yi wanka, Domin an samu wasu da yawa da suka musulunta a zaminin annabi (s.a.w) amm baice musu suyi wanka ba).

    2=wankan juma'a (an so mutum yayi wankan juma'a).

    3=wankan ranar idin karamar salla ko babbar salla (anso ayi wanka ranar idi).

    4=wanka idan mutum ya wanke mamaci (anso mutumin da ya wanke mamaci yayi wanka).

    5= wanka a yayin da mutum zaiyi ihramin aikin hajji. (anso mutum yayi wanka saboda ihramil).

    6=wanka saboda shiga makkah (anso ayi wanka saboda shiga makkah).

    7= wankan ranar arfah (anso mutum yayi wanka sbd ranar arfah).

    8= wanka yayin da mutum ya farka daga suma ko gigicewa (an so wanda ya farka daga suma ko gigicewa yayi wanka).

    TAMBIHI

    duka wadannan abubuwan da suka wajabta yin wanka, ko wadan da aka so ayi wanka saboda su, to wankan dai suffar sa daya ce sai dai niyarsuce ta bambanta.

    Kamar yanda annabi (s.a.w) ya fada acikin hadisin amirul-mu-uminin umar dan qaddab (r. d)

    إنما الأعمال بالنيات، وإنما لكل امرئ ما نوى.[متفق على صحته.]

    Dakkan aiyuka basa yihuwa sai da niyya kuma haqiqa kowa ne mutum akwai abin da ya nufata. [Bakhari da muslim ne suka rawaitu shi].

    YANDA AKEYIN WANKAN JANABA

    Wankan janaba ya na da siffa biyu:

    1= siffar da ta wadatar (ita ce suffar da idan aka yita ta wadatar kuma wanka yayi.)

    2= siffar kamala (itace irin yanda annabi. (s.a.w) ya ke yin wanka janaba. Kuma ita ce suffar da tafi palala)

    1= yan da ake wankan janaba siffar da ta wadatar : ita ce yayin da mutum yayi niyar wankan da zaiyi to zai game dukkan jikin sa da ruwa (wato ya zuba ruwa adukkan jikin sa ko ina da ina) tare da shaqa ruwa a hancin sa da kuskure bakin sa, idan mutum yayi haka to dakkan wani hadasi da yake jikin sa qarami ne ko babba ne ya kau, saboda fadin allah mai rahma: IDAN KUN KASANCE MASU JANABA TO SAI KU TSARKAKA..... [SURATUL-MA'IDA AYA TA 6].

    2=yan da ake yin wankan janaba siffar kamala.

    **Annabi (s.a.w) yana fara da wanke tafukan hannayan sa kafin ya sanya su a cikin abin wankan.

    ** sannan ya zuba ruwan da damar sa akan hagun sa sai ya wanke farjin sa da hagun sa (bayan ya gama wanke farjin nasa sai ya goga hannun hagun sa a qasa gogawa dan ya qara tsaftace shi)

    ** sannan yayi alwala ci kakkiya irin ta salla (ko kuma yayi alwalar banda kafafun sa sai ya gama wankan sai ya dan matsa daga in da yai wankan sai ya wanke kafafun sa).

    ** sannan ya shigar da yatsun hannayan sa cikin ma tsurar gashin kansa ya chucu-chuda shi har sai ya kosar da ko ina akan nasa sau uku( sannan ya zuba ruwa sau uku akansa)

    ** sannan ya zuba ruwa a bangaran jikin sa na dama sai kuma ya zuba ruwan a bangaran jikin sa na hagu.

    ** sannan an sami ruwayar da ta nuna ce wa yana sharce ruwan daga jikin sa da hannayan sa bayan ya gama wankan.

    Wannan shi ne suffar wankan annabi (s.a.w) na janaba.

    Dalili kuwa shi ne

    Hadisin da yake cikin sahihaini an karbo da ga dan abbas daga yar'uwar mahaifiyar sa maimuna (allah ya qara yarda da su)ta ce: na kusantarwa da annabi (s.a.w) ruwan Wankan sa na janaba, sai ya wanke tafukan hannunsa sau biyu ko sau uku, sannan ya shigar da hannun sa cikin kwaryar wankan, sannan sai ya zuba ruwan akan farjin sa sai ya wanke shi da hagun sa, sannan ya bigi qasa da hagun sa sai ya gogata gogawa mai sosai sannan yai alwala irin alwalar sa ta salla sannan ya zuba ruwa akan sa zubawa sau uku cikin tafin hannun sa, sannan ya wanke dukkan jikin sa, sannan ya dan matsa daga inda yiyi wankan sai ya wanke qafafuwan sa, sannan na zo masa da tawul sai ya maida shi. (ma'ana bai anshe shi ba) [bakhari da muslim suka rawaitu shi]

    Kuma babu wani bambanci tsakanin wankan janaba da wankan haila,

    Sai dai an so mace ta chuch-chuda kanta sosai a wankan haila sama da yanda take yi a wankan janaba, kuma an so a wankan haila mace ta samu auduga ta sanya turare a jikin audugar sai ta bibiyi wajan jinin da ita (wato ta goga tiraran a wajan jinin) , saboda ya gusar da qarnin jinin.

    Saboda hadisin nana a'isha (r.d) da yake cikin sahihi muslim hadisi na (332)

    AMSAWA

    {(ABU ABDULLAH)}

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.