Zanga-Zanga: Nijeriya Ina Muka Dosa?

Daga:
Prof. Muhammad Babangida Muhammad 

1. Na yi wannan rubutu cikin tsoro da fargaba akan makomar kasata, Nijeriya. Kafafen Sada Zumunci (ko kuma bata zumunci) a cikin kwanankin nan, cike suke da soki burutsu da yarfe da kage da munanan maganganu na cin mutumci da tozartarwa ga malamai. Wannan ya biyo bayan kiraye-kiraye da shirin da wadansu mutane, wadanda ba a san hakikaninsu ba, suke yi na yin gagarumar zanga-zanga ta nuna fusatarsu ga Gwamnati akan yanayi da jama'ar kasa suke ciki.

2. Hakika, jama'ar kasa suna cikin kunci da talauci da rashin abin hannu da karancin abinci, ga hauhawar farashi da tsadar rayuwa. Ga kuma halin rashin tsaro da ‘yan ta'adda da masu garkuwa da mutane. Malamai sun yi kiraye- kiraye ga mahukunta da basu shawarwari a boye da bayyane a kan minbari game da wajibcin da ke kansu na daukar matakan da suka dace domin ganin bayan wadannan matsaloli. Anan, malamai sun sauke nauyin da ke kansu. Ba su da ikon tilasta shugabanni su karbi nasiharsu, ba kuma za su yi tawaye ba irin yadda masu zagin malaman suke so.

3. Sassan al'umma sun fusata ne akan mabambantan dalilai; ko na talauci, ko kabilanci, ko bangaranci, ko siyasa ko wassu dalilan dabam. Wadannan sassa suna son lallai malamai su bar manufar addini da maslahar al'umma, su fifita wadansu boyayyun manufofi. Malamai ba da kuri'a aka zabe su ba, saboda haka bai lizimce su da su bi abinda mutane suke so ba, alhali akan kuskure suke.

4. Al’amura sun kara gurbacewa ta fuskar cewa su kuma shugabanni na siyasa da jagororin gwamnatoci a matakai dabam dabam ba sa son su ji maganar gaskiya daga malamai. Sun fi so a fada musu abinda suke so su ji; cewa kun fi kowa adalci… kun fi kowa aiki. Kun fi kowa kishin kasa. .  ba a yi ba, kuma ba za a yi kamarku ba…. !!! A'a, wannan ba aikin malamai ba ne!

5. Su kuma matasa masu tada kayar baya da ruruta wutar zanga-zanga da kuma wadanda suka fake da su domin boyayyun manufofi, suna son malamai su ma su ajiye iliminsu a gefe, su bar amfani da hankalinsu, su ji tsoron fushin ‘yan tawaye, kada su malaman su tsawatar musu. Wai idan sunyi haka suna tare da azzalumai, sun karbi kudinsu ne. Idan za a yi ba daidai ba kada malamai su ce ba daidai ba ne. Idan masu zanga-zanga suka fito suna kone-kone, suna bin mutane a kan tituna da gidaje suna karkashe su, to kada malamai su tsawatar. To, al'ummar da matasanta suka rasa mai tsawatarwa, ina makomarta?

6. Abin la'akari game da kamfen da ake yi na cin mutumcin malamai shine cewa, idan aka tashi wannan zanga-zanga, kasa za ta kasance cikin rudu da tashin hankali da harigido da rashin alkibla. Zai kasance babu mafadi, babu mai tsawatarwa, kuma babu mai jagorar abinda matasan za su yi. Matasan da ake tunzura su, za su ci karensu babu babbaka. Za su yi artabu da jami'an tsaro, a kashe su, su ma su kashe, da wanda ya ji da wanda bai ji ba, kuma su kona kayan gwamnati (public property- kayan al'umma). Hasarar wa? A rasa ruwa, a rasa lantarki, a rasa abin hawa, a rufe asibitoci, a rufe makarantu, a rufe kasuwanni. Dama can yaya? Shikenan sai abubuwa su kara rincabewa. Anya za a samu gyara ta haka? An samu ci gaba a Libya ko Somalia ko Syria ko Sudan a dalilin zanga-zanga da tawaye? 

7. Idan ba kwa son malamai su ce muku, ‘kalallahu kala rasuluhu’ akan wannan batu, to ba sai kun zage su ba, ba sai kun yi musu yarfe ba, amma dai da za ku hankalta daga darussan wassu kasashe. Haba! Gani ga wane bai isa wane tsoron Allah ba? A fa la tatafakkarun? - Shin ba za ku yi tunani ba? (Al an'am:50) Idan an fusata da gazawar gwamnati shikenan sai hankali ya gushe, a aikata abinda za a yi nadama? Wani ma ya ce, da ma za a yi girgizar kasa kowa ya halaka, da mai cewa Nijeriyar ma duk ta fashe! Ina hankali? Wani ma tun daga China ya kyalla ido ya ga Tinubu yana mika wa malamai su sama da dari, ko wannensu Naira miliyan sha shida (16 million).  Sa tuktabu shahadatuhum wa yus'alun - Tabbas, za a rubuta shaidarsu, kuma lallai za a tambaye su - a lahira. (Zukhruf:19). Idan ma laifin malamai shine a nazarinsu na halin da aka shiga lokacin zabe, a kyakkyawan zatonsu sun ce maslaha ita ce a yi Muslim-Muslim ticket, to shikenan a jira lokaci, idan sun so su jarraba Christian- Christian ticket ko ma Pagan- Pagan ticket. Idan tunanin malamai da iliminsu basu zama abin dogaro ba, to, su jarraba na jahilan cikin al'umma su gani.

8. (Sabran, sabran ya warathatal anbiya'i ) : Ku lizimci hakuri akan cutarwar jahilai, ya ku magada Annabawa. Kada ku bari su tunzura ku har ku fadi ko ku aikata abinda ya sabawa iliminku. Ku girmama juna, ku hada kai. Ku riki addu'a. Ku kuma ‘yan tsaurin ido da nina rashin da'a a ‘social media', wallahi ku yi a hankali. Idan kuka zubar da kimar malamanku, tabbas za ku fada hannun jahilai, su yi ta walagigi da ku, su kai ku su baro, ba addini ba addila.

9. Hakika, matsaya ta ilimi da sanin ya kamata, ita ce, shugabanni su saurari kukan jama'arsu, su sassauta musu. Su kuma matasa da masu zuga su, su guji fitina wadda za ta haifar da matsaloli da kunci da wahala da suka fi wadanda ake ciki. Wannan fadakarwa ko a karba ko a yi dariya. Dariyar kuma, a fadar Sa'adu Zungur, ta zam kuka gaba, da nadamar mai kin gaskiya. Allah Ya tsare.

10. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya da arziki da wadata, Ya shiryar da shugabanninmu wajen yi mana adalci da matasanmu wajen tarbiyya da ilimi da biyayya.

 Nigeria

Post a Comment

0 Comments