Albarkacin #RanarHausa
Zuwa ga Rabiu Isah Hassan
Hausawa sun rayu a doron ƙasa sama da shekara dubu 60!
Da alama dai naka binciken na daban ne, domin ba ka ma iya bambancewa tsakanin Hausawa da harshen Hausa ba. Idan ba Hausawa a doron ƙasa cikin shekara dubu 60, to ina suka maƙale sai shekara dubu 5 da suka wuce aka sako su? Shi kuma harshen Hausa da kake magana ya fito daga tsatson ahalin Afrika da Asiya ya wanzu ne a tsakanin shekara dubu 9 zuwa 10, ka ga ke nan maganar shekara dubu 5 da ka ce ya samu, kana zancen zamanin Annabi Musa ne da makusantan sa, wanda mun bayyana dangantakar wannan da rayuwar Hausawa ta dauri a maƙalun da muka buga na ilimi a lokutta mabambanta a baya, a leƙa ƙila a ƙara samun haske!
Idan ba ka sani ba ina ƙara sanar da kai cewa Hausawa mutane ne
ba aljannu ko mala'iku ba, sun wanzu tun farkon halittar Adamu da Hawwa'u, sun
kuma wanzu ko bayan ruwan ɗufana,
wato a cikin halittar ahalin Annabi Nuhu da suka rayu a cikin kwale-kwale na
kusan shekara biyu. Sun kuma fito daga tsatson mutanen da suka samar da
al'ummar duniya na zamani daga yankin Omo-Kibish a ƙasar Habasha ta yau, sama
da shekara dubu ɗari
da hamsin da suka wuce. Bulaguro ya kai wasu daga cikin su zuwa da kuma wanzuwa
a nahiyar Asiya da yankin Larabawan dauri tun daga shekara ta dubu 60 zuwa dubu
40 da suka zaunu a waɗannan
yankuna.
Haka daga shekara dubu 20 a daidai lokacin da yankin Amurka
ya fara ginuwa; (idan ba ka sani ba, yankin Amurka duka-duka ya wanzu ne
shekara dubu 15 da suka wuce) ko a wannan lokaci waɗannan
al'umma ta Hausawa suna a doron ƙasa, sun rayu a Kudancin Masar, inda
yawancin ahalin Hausawa ta ɓangaren
Uba suka wanzu, suka rayu da kuma musamman yankin Siwa, wanda ke a Yammacin ƙasar
Masar da iyakar ƙasar Libya kusan shekara dubu 20 da suka wuce.
Idan ka nazarci harsuna da al’ummar waɗannan yankuna, musamman
daga yankin Maleshiya a Asiya da yankin Larabawa, musamman ɓangarorin Yemen da Falasɗinu da Saudi Arabiya da
Masar da Isira’ila za ka tsinci wasu al’adun Hausawa da addinai da wasu kalmomi
na harsunan waɗannan
yankuna a cikin rayuwar Hausawa ta yau; dubi lamarin bautar rana, abinci da
sutura da soyayya da mulki da waƙe-waƙen gargajiya. Akwai misalai na kalmomin
Hausa na yau da suka samo asali daga waɗannan
yankuna da addinai da al'adu in kana son ƙarin ilimi.
Bayan wannan zama na tsawon tarihi a Arewacin Afirka, a
tsakanin ‘yan uwa da abokan hulɗa
kamar su Kibɗawa da
Yahudawa da Misirawa, wannan al'umma ta yi hijira zuwa yankin kogin Chadi da ke
a tsakiyar Afirka, a wannan lokaci yankin mai dausayi ne da lema da ke ɗauke da manyan dabbobin
ruwa da na daji. A zamansu ne na wannan yanki aka samar da harshen da aka yi wa
laƙabi
da Ahalin Afrika da Asiya a daidai shekaru dubu 9 zuwa 10, KHA, nan kuma aka
samar da tsatson Ahalin harsunan Chadic,
wanda ya haifar da harshen Hausa da 'yan uwansa, irin su Gwandara da Ron da
Tangale da Warji da Bade da Angas da
Barawa da Kare-Kare da sauran su. Sai daga baya da dausayi da lemar da ke a
wurin suka bushe, hamada ta bayyana, al'ummar Hausawa suka watsu zuwa sassa
daban-daban na tsakiyar Afrika da suka haɗa
da Habasha da Libya da Kamaru da sassan ƙasar Hausa da dama na yanzu.
Wannan shi ya haifar da damar da aka samu suka sake haɗuwa da sauran 'yan uwansu,
musamman na ɓangaren
jinin Uwa da ba su yi bulaguro zuwa ko'ina ba a sassan duniya, suna zaune a
nahiyar Afirka a tsawon shekaru. Wannan haɗakar
barbarar 'yan'yawa ita ta samar da kai da ni da duk wani Badauri ko Bagobiri ko
Bakatsine ko Bazamfare ko Bakabe ko Bazazzage ko Basantolo ko Bakano ko Bagunge
ko Bahaɗeje ko Barane
da wasu ƙasashe
da al'ummun Hausawa da dama da suka yi rayuwa suka ɓace a tsawon tarihi.
Wannan ba komi yake nuna mana ba sai cewa Hausawa ba na
yanzu ba ne, shi harshen Hausa ne na yanzu, shi ma ba yanzun-yanzu irin na yau
ba ne, shekara dubbai ne ake magana.
Na ɗauki
wannan tsawon lokaci ina maka wannan taƙaitaccen bayani ne domin na fahimci kana ƙishirwar
ilimin asalin Hausawa da harshen Hausa, sai dai da alama ba ka neman ruwan sha
mai sanyi domin kawar da ƙishin, shi ruwan zafi da kake sha, ba abin da zai ƙara
maka sai ƙone
maƙoshi,
ba dai ya biya buƙata ba!
Bincike ake yi Malam Rabi'u ba shaci-faɗi ba ne, bincike ne na
sanin asali ba kuma na kunne ya girmi kaka ba ne, bincike ne da ya haɗa da na tarihi, labarin ƙasa,
kimiyyar halitta da na ƙwayar halitta da na hijira da bulaguro da samuwar harsuna da
addinai da ginuwar zamantakewar al'umma tun daga samuwar ɗan Adam na zamani.
Allah ya sa ka tsinci wani abu daga wannan jawabi. Idan kuma
akwai wani ƙarin
haske da kake da shi kan wannan batu, muna jira da buƙata domin mu ɗaliban ilimi ne ba na
hasashe da jita-jita ba!
Daga Prof. Ibrahim Malumfashi
Allahu a’alam!
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.